KAI TSAYE, Yaƙin Iran da labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 06/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan abubuwan da ke faruwa tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma sauran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 06/06/2026.

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. 'ICPC ta hana El-Rufia damar samun kulawar aisibiti'

    .....

    Asalin hoton, Muyiwa Adekeye/X

    Mai ba tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya zargi hukumar ICPC da hana shi damar samun kulawar asibiti yayin da yake tsare.

    A cikin wata sanarwa da ya fitar, Adekeye ya ce El-Rufai ya koka kan matsalar idanusa suna ƙaiƙayi da kumburi, inda ya nemi a kai shi asibiti domin duba lafiyarsa, amma jami’an ICPC suka ƙi amincewa da bukatar.

    Ya bayyana cewa an riga an kai shi asibitin ido a ranar 4 ga watan Yuni, amma daga baya yanayin idon ya ƙara taɓarɓarewa, abin da ya jawo damuwa ga iyalansa.

    A cewarsa, jami’an ICPC sun ga halin da idanuwansa ke ciki, amma ba a shirya masa ƙarin kulawar likita ba, abin da ya ce ya ƙara dagula lamarin.

    Ya kuma zargi hukumar da bayar da bayanan da ba su dace ba ga iyalan El-Rufai, inda aka ce bai nemi ganin likita ba, zargin da ya ce ba gaskiya ba ne.

    Adekeye ya kuma ce akwai umarnin kotu da ke ba El-Rufai damar samun kulawar lafiya, amma har yanzu ba a bi umarnin yadda ya kamata ba.

    ICPC dai ba ta mayar da martani kai tsaye kan waɗannan zarge-zarge ba, yayin da batun ke ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce.

  2. Matatar Dangote ta ƙara yawan fetur da take samarwa zuwa ganga 700,000 a rana

    Matatar man fetur ta Dangote ta ƙara yawan man fetur da take samarwa da kuma rabawa gidajen mai a Najeriya, bayan da ƙarfin tace danyen man da take yi ya kai ganga 700,000 a rana.

    Matatar, wadda babban attajirin ɗan kasuwan Najeriya, Aliko Dangote ya mallaka, ta fara samar da man fetur ne a shekarar 2024, kuma tun daga lokacin take ci gaba da ƙara yawan samar da fetur, dizal, man jiragen sama da sauran kayayyakin man da aka tace.

    Rahotanni sun nuna cewa an samu ƙarin isar da fetur zuwa gidajen man da ke haɗin gwiwa da matatar, musamman na MRS, tsakanin ranar Juma'a da safiyar Asabar.

    A makon da ya gabata, matatar ta sanar da rage farashin fetur daga naira 1,275 zuwa naira 1,250 kan kowace lita a farashin da take sayarwa ga dillalai, yayin da ta rage farashin dizal daga naira 1,800 zuwa naira 1,700 kan kowace lita.

  3. Iran ƙasa ce mai ƙarfi da girman kai shiyasa ba ta amince da yarjejeniya ba - Trump

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa har yanzu Iran ba ta amince da yarjejeniyar da Washington ta gabatar ba saboda ita ƙasa ce mai ƙarfi kuma mai girman kai.

    Da yake amsa tambaya daga mai gabatar da shirin Meet the Press na NBC, Kristen Welker, Trump ya ce ba abu ne mai sauƙi ga Iran ta amince da wasu daga cikin buƙatun Amurka ba.

    Trump ya kuma yi ikirarin cewa Iran na da kusan kashi 21 zuwa 22 cikin 100 ne kawai na makamanta masu linzami da suka rage.

    Ya ce Amurka ta san kusan adadin sauran makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa da Iran ke da su, da kuma wuraren da ake ajiye su.

    Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa mafi yawan cibiyoyin kera makamai masu linzami, masana'antun jiragen yaƙi marasa matuƙa, da wuraren harba makamai na Iran sun lalace.

    Sai dai ya ce har yanzu Iran na da wasu makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa.

    Duk da haka, Trump ya bayyana fatan cewa tattaunawar da ake yi tsakanin Amurka da Iran za ta kai ga cimma matsaya, ko da yake ya amince cewa samun yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu har yanzu abu ne mai wahala.

  4. Mun kai harin martani kan sansanonin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya - Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta ce dakarun juyin juya halin ƙasar (IRGC) sun kai hare-hare kan sansanonin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya da makamai masu linzami na rundunar sararin samaniyarta.

    Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito cewa sashen hulɗa da jama'a na IRGC ya bayyana cewa harin ya zo ne a matsayin martani ga abin da ya kira "ta'addancin soji" da Amurka ta aiwatar a Sirik da tsibirin Qeshm na Iran.

    A cewar sanarwar, an kai hare-haren ne kan sansanonin da Iran ta bayyana a matsayin na "abokan gaba" da ke yankin da makamai masu linzami.

    Rahotanni sun ce Iran ta zargi Amurka da kai hari kan wani hasumiyar sadarwa a kudancin tsibirin Qeshm, lamarin da ya haddasa wannan martani daga Tehran.

    Sai dai rundunar CENTCOM ta Amurka ta bayyana hare-haren da ta kai a yankin a matsayin matakan kariyar kai, yayin da rikicin da ke tsakanin kasashen biyu ke ci gaba da ƙara tsananta duk da ƙoƙarin sasanta rikicin.

  5. Assalamu alaikum!

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye wanda ke kawo muku labaran duk abubuwan da ke faruwa game da yaƙin Iran da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da saurarn sassan duniya a wannan rana ta Asabar,

    Aisha Bababngida ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za kuma ku iya yin tsokaci a shafukanmun na sada zumunta: facebook, X, instagram, YouTube sai kuma zaurenmu na WhatssApp.