Maniyyatan Najeriya 50,000 ne za su sauke farali a 2026 - NAHCON
Ba za mu yi sulhu da ƴanbindiga a Arewa Maso Yamma ba - Gwamnan Sokoto
Iran ta ce a shirye take ga tattaunawa ko komawa yaƙi
Rahoto kai-tsaye
Daga Abdullahi Bello Diginza da Muslim Muhammad Yusuf
Kwankwaso da Obi sun koma jam'iyyar NDC
Asalin hoton, Hon. Saifulllahi Hassan/FB
Tsohon ɗantakarar shugaban Najeriya a zaɓen 2023 Peter Obi, da tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun koma jam'iyar NDC.
Jiga-jigan adawar sun karɓi katin jam'iyar ne bayan ficewa daga jam'iyar ADC saboda rikice-rikicen shugabanci da suka ce sun dabaibaye ta.
Dukkansu sun karɓi katin NDC ne a hedikwatar jam'iyar tare da jagoranta Hon. Seriake Dickson.
Ana ta hasashen cewa jiga-jigan adawar na son yin takarar shugaban ƙasa da mataimaki, inda magoya bayansu suka ƙaddamar da wata tafiya da suka kira da OK Movement.
Asalin hoton, Hon. Seriake Dickson
APC ta fitar da ɗan takarar gwamna a jihar Gombe
Asalin hoton, Ismaila Uba Misilli
Bayanan hoto, Dr. Jamilu Ishiyaku Gwamna [daga tsakiya] shi ne wanda Inuwa ya goyi baya a matsayin wanda zai wa APC takarar gwamna Gombe a zaɓen 2027.
Jam'iyar APC mai mulki a jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya, ta zaɓi Dr. Jamilu Ishiyaku a matsayin wanda zai mata takarar kujerar gwamnan jihar a zaɓen 2027.
Kakakin gwamnan ismaila Uba Misilli ya shaida wa BBC cewa an cimma wannan matsaya ce a wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyar da aka yi ƙarƙashin jagorancin gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya.
Ya ce an bi tsarin masalaha ne wajen fidda ƴan takarar a zaman da aka yi, inda aka amince da fitar da waɗanda za su yi takarar Sanata a mazaɓu uku da Ƴan Majalisar Wakilai ta Tarayya da Ƴan Majalisar Dokokin Jihar.
Ana jimamin rasuwar ɗan jarida Saleh Ashaka
Asalin hoton, Uwaisu Abubakar Idris/FB
Allah ya yi wa tsohon wakilin sashen Hausa na gidan rediyon Muryar Amuka (VOA) Saleh Shehu Ashaka rasuwa.
Makusantan marigayin sun tabbatar da cewa ya rasu ne a yau Lahadi, bayan fama da doguwar rashin lafiya da ya riƙa yi a tsaitsaye.
Marigayin ya je birnin Cairo na ƙasar Masar ne da iyyar dubiya, amma daga bisani, shi ma ta shi rashin lafiyar ta tashi, inda har aka kwantar da shi a sashen kulawar gaggawa.
Ɗan jaridar wanda ya shafe gomman shekaru yana aikin, ya kasance ɗaya daga cikin wakilan VOA Hausa a birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Ya rasu ya bar mata biyu da yaro ɗaya.
ƴan uwa da abokan aikin marigain da dama sun yi ta aika saƙon ta'aziyyarsu a shafukan sada zumunt, ciki har da tsohon ministan sadarwa Sheikh Isa Ali Pantami da Abdulaziz Abdulaziz, mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin yaɗa labarai.
Tinubu ya tafi balaguro Faransa, Kenya da Ruwanda
Asalin hoton, @NGRPresident/X
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bar Najeriya zuwa ƙasar Faransa, inda ya fara ziyarar aiki zuwa ƙasashe uku da suka haɗa da Kenya da Ruwanda.
Da ranar yau Lahadi ne jirgin shugaban ƙasar ya tashi daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, babban birnin ƙasar, yayin da ya fara wani rangadin na diflomasiyya da nufin ƙarfafa dangantakar tattalin arziki da kuma jawo masu zuba jari daga ƙasashen waje.
Fadar shugaban ƙasar ta ce, Tinubu zai fara yada zango ne a Faransa, daga nan kuma zai tafi Nairobi babban birnin Kenya. domin halartar taron ƙasashen Afrika da Faransa da aka shirya gudanarwa daga ranar 11 zuwa 12 ga watan Mayu.
Daga Kenya kuma, Tinubu zai zarce zuwa Kigali, babban birnin Rwanda, domin halartar taron shugabannin Afirka da za a gudanar daga ranar 14 zuwa 15 ga Mayu.
Sojojin Amurka biyu sun ɓace lokacin atisaye a Moroko
Asalin hoton, Universal Images Group via Getty Images
Rundunar Africom, ta sojin Amurka da ke aiki a Afirka ta sanar da ɓacewar wasu sojojin Amurka biyu a lokacin atisaye a Moroko.
Jami'ai sun ce sojojin na cikin atisayen 'African Lion 2026,' da rundunar ke gudanar shekara-shekara, domin ƙarfafa ƙawancen sojin Amurka da ƙawayenta na Nato da na Afirka
Rundunar Africom ta ce an bayar da rahoton ɓacewar sojojin ranar Asabar da maraice a kusa da sansanin horon soji na Cap Draa, da ke kusa da birnin Tan Tan a Moroko.
Tuni dai sojojin Amurka da na Moroko da sauran ƙasashe suka fara aikin nema ta sama da ƙasa da ruwa domin ceto sojojin biyu.
Hukumomi sun ce da alama ba ƴanta'adda ba ne suka kama sojojin, ɓacewa suka yi, kamar yadda wani jami'in sojin Amurka da ke da masani game da lamarin ya shaida wa BBC.
Rundunar Africom na gudanar da atisayen na shekara-shekara ne a ƙasashen Moroko da Ghana da Senegal da kuma Tunisiya.
An fara atisayen wannan shekara ne da ya ƙunshi dakaru 5,000 daga ƙasashe fiye da 40 daga ranar 27 ga watan Afrilu zuwa 8 ga watan Mayu.
OPEC ta amince ta ƙara yawan man da take haƙowa
Ƙungiyar Opec ta ƙasashe masu arzikin man fetur ta amince da ƙara yawan man da take fitarwa da ganga 188,000 ga kowace ƙasa a kowace rana.
To amma ana ganin matakin da zai fara aiki a watan Yuni zai fuskanci cikas daga ƙara yawan man da UAE ke fitarwa, wadda ta fice daga ƙungiyar a baya-bayan nan.
Babban kamfanin haƙar mai na Abu Dhabi National Oil Company, ya alƙawarta kashe dala biliyan 55 kan sabon aikin haƙar man fetur da zai gudanar nan da shekara biyu masu zuwa.
Ƙasar UAE ta jima tana yin fushi da OPEC kan man da ake ƙayyade wa ƙasar.
Ƙasar ta Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na da burin faɗaɗa yawan man da take fitarwa zuwa ganga miliyan biyar a akowace nan da shekarar 2027.
Matar da ta samu ciki ɗaya daga mazaje biyu
Asalin hoton, BBC Mundo
A shekarar 2018, wata mata ta je ɗakin gwaje-gwajen ƙwayoyin halitta a Jami'ar National University ta Colombia domin tabbatar da ainihin mahafin tagwayenta maza masu shekara biyu a duniya.
Sai masu bincike suka gudanar da gwaje-gwaje, sannan suka sake maimaitawa.
Sun maimaita ne domin tabbatar da abin da suka gani na mamaki. Ita ce mahaifiyar tagwayen, amma kowanne mahaifinsa daban.
Wannan wani yanayi ne da ba a cika samu ba da ake kira heteropaternal superfecundation.
Kusan sau 20 ne kacal aka samu labarin irin haka a mujallun kimiyya a duniya.
Masana a jami'ar su ce za su iya samun haka, amma ba su taɓa ganin haka ba.
Wannan ya sa suka ƙara ƙaimi wajen zurfafafa bincike.
Mutum tara sun mutu a harin jirgi maras matuƙi a Sudan
Aƙalla mutum tara sun mutu a wani harin jirgi maras matuƙi a tsakiyar ƙasar Sudan.
Harin ya faɗa kan gidan kwamandan rundunar Sudan Shield Force, mai aiki da sojojin ƙasar, Abu Aqla Keikal a unguwar Wad Madani da ke jihar Aljazira.
Ƙungiyarsa ta ɗora alhakin harin kan mayaƙan RSF masu faɗa a gamnati.
Keikal, ya kasance tsohon kwamandan RSF a yankin, wanda ya koma ɓangaren sojojin ƙasar.
Ya dai sha zarge-zargen aikata laifuka a lokacin yaƙin.
Hare-haren jirage marasa matuƙa sun riƙa ƙaruwa tsakanin ɓangarorin biyu a ƴan watannin baya-bayan nan.
Peter Obi ya tabbatar da ficewa daga jam'iyyar ADC
Asalin hoton, Peter Obi/X
Tsohon ɗan takarar shugaban Najeriya a zaɓen 2023, kuma jigo a jam'iyyar ADC ta masu haɗaka, Peter Obi ya tabbatar ficewa daga jam'iyyar.
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, Peter Obi ya ce ya ɗauki matakin ne sakamakon rigingimun cikin gida da suka dabaibaye jam'iyyar.
Mista Obi ya ce rigimar da ya yi ƙoƙarin guje wa a tsohuwar jam'iyyarsa ta LP, ta sake kunno kai a cikin sabuwar jam'iyyar da ya shiga ta ADC.
Ya kuma bayyana cewa ya ɗauki matakin ne ba don wani shugaba ko jigo a cikin ADC ya ɓata masa rai ba.
''Ban ɗauki matakin saboda shugaban jam'iyyar, David Mark ko Atiku ko wani jigo a jam'iyyar ya yi min wani abu ba'', in ji shi.
Jam'iyyar ADC na fuskantar rikicin shugabanci, wanda yanzu haka ke gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda Nafi'u Bala ya shigar da ƙarar tsagin David Mark da cewa ba halastattun shugabanni ba ne.
A makon mai ƙarewa ne Koton Kolin ƙasar ta ce ɓangarorin biyu su koma babbar kotun tarayyar domin ci gaba da shari'ar.
Tun a cikin makon ne kuma ake ta raɗe-raɗin cewa Peter Obi da Kwankwaso za su fice daga jam'iyyar ADC zuwa NDC, kodayake kawo yanzu ba su tabbatar da hakan ba.
Shi ma kwankwason a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce yana tuntuɓar abokan siyasarsa domin ɗaukar mataki kan makomarsa a siyasance.
Dole Amurka ta zaɓa tsakanin ci gaba da yaƙin 'da ba zai yiwuwa ba' ko yarjejeniya maras kyau - IGRC
Sashen tattara bayanan sirri na rundunar juyin juya halin Iran ya ce Amurka na cikin tsaka mai wuya na zaɓin ci gaba da yaƙi, wanda ta bayyana da ''abin da ba zai yiwuwa ba'' ko kuma ta amince da yarjejeniya maras kyau'' da Iran.
Cikin wata sanarwa da sashen ya fitar ya ce ''lokacin Amurka na ɗaukar mataƙi na ci gaba da ƙurewa''.
Sanarwar ta ci gaba da cewa wa'adin da Iran ta bayar kan dakatar da rufe tasoshin ruwanta da kuma matsayin Rasha da China da Turai kan Amurka, da ma wasiƙar Trump ga majalisa da kuma amincewa da sharuɗaɗan Iran duka ba abin da za su haifar.
''Don haka dole ne Trump ya zaɓa tsakanin ''ci gaba da kai hare-hare, wanda kuma hakan ba abu ne da zai yiwuwa ba, ko kuma ta amince da yarjejeniyar maras kyau da Iran'', in ji sanarwar.
ADC ta fara sayar da fom ɗin takarar shugaban ƙasa kan naira miliyan 100
Asalin hoton, ADC
Jam'iyyar hamayya ta ADC ta fara sayar da fom ɗin takara muƙamai daban-daban gabain babban zaɓen ƙasar na 2027.
Cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar na ƙasar, Bolaji Abdullahi ya fitar, ta ce jam'iyyar ta saka kuɗin fom ɗin takarar shugaban ƙasa kan naira miliyan 100.
Sanarwar ta kuma ce jam'iyyar ta fitar da jadawalin zaɓukan fitar da gwani na jam'iyyar, inda za a yi na shugaban ƙasa ranar 25 ga watan Mayu.
Jam'iyyar ta kuma saka kuɗin fom ɗin takarar gwamna kan naira miliyan 50, yayin da na sanata ke naira miliyan 20, sai na ɗan majalisar tarayya a kan naira miliyan 10 da ɗan majalisar jiha naira miliyan uku.
Sanarwar ta kuma bayyana rangwamen kashi 50 cikin ɗari ga matasa, da ragin kashi 75 ga mata da masu buƙata ta musamman.
Iran ta ce a shirye take ga tattaunawa ko komawa yaƙi
Asalin hoton, Getty Images
Wani babban jami'in sojin Iran, Mohammad Jafar Asadi, ya ce akwai ''yiwuwar'' sabon yaƙi ya ɓarke tsakanin Amurka da Iran, sakamakon yadda Trump ya soki buƙatun da Iran ta gabatar don tattaunawar zaman lafiya a baya-bayan nan.
Kamfanin dillancin labarai na Fars ya ambato Asadi, wanda mamba ne rundunar sojin Iran ta 'Khatam al-Anbiya command center' na cewa ''Akwai yiwuwar ɓarkewar sabon yaƙi tsakanin Iran da Amurka, kuma alamomi da dama sun tabbatar da cewa Amurka ba ta shirya wa amincewa da kowane irin alƙawari ko yarjejeniya ba''.
A wani abu mai kama da wannan, mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi ya ce Iran a shirye take ga tattaunawar zaman lafiya ko kuma komawa yaƙin.
Ba za mu yi sulhu da ƴanbindiga a Arewa Maso Yamma ba - Gwamnan Sokoto
Asalin hoton, Ahmad Aliyu
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ce gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya ba za su yi sulhu da ƴanbindigar da ke addabar yankin ba.
Yayin da yake jawabi a wurin bikin ƙaddamar da wani titi da gwamnan Katsina ya gina, Ahmad Aliyu ya ce gwamnonin yankin na yin aiki tare domin kawo ƙarshen matsalar.
Yankin arewa maso yammacin Najeriya dai ya shafe shekaru yana fuskantar hare-haren ƴanfashin daji, masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, lamarin da ya sa ake tsananta kiraye-kirayen kawo ƙarshen matsalar, ciki har da masu kiran amfani da hanyar sulhu.
Sai dai gwamnan na Sokoto ya ce ba za su yi tattaunawar sulhu da ƴanbindigar ba.
“Ba za mu yi sulhu da kowane mai laifi ba, ba za mu amince da duk wata buƙatarsu ba, har sai sun amince za su ajiye makamansu ba tare da kowane irin sharaɗi ba,'' kamar yadda ya jaddada.
Gwamnan ya ci gaba da cewa gwamnatocin jihohin yankin na aiki da jami'an tsaro don kawo ƙarshen matsalar.
Ya kuma yi kira ga mutane su riƙa bai wa gwamnati da jami'an tsaro haɗin kai wajen fallasa masu kwarmata wa ƴanbingar bayanan sirri, yana mai cewa babu wani harin, yanbindiga da zai gudana ba tare da hadin bakin ƴan garin ba.
Wani ƙaton jirgin dakon mai da zai je Indiya ya wuce ta mashigar Hormuz
Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar kula da fiton kaya da Indiya ta ce wani katafaren jirgin dakon mai ɗauke da fetur da nauyinsa ya kai metric ton 46,313, ya ƙetare mashigar Hormuz a ranar Asabar.
A cikin wata sanarwa, da ma'aikatar ta fitar ta ce jirgin ɗauke da ma'aikata 20, ana sa ran zai isa tashar jiragen ruwa ta Visakhapatnam a gabashin ƙasar ranar 13 ga watan Mayun da muke ciki.
Har yanzu dai mashigar ta Hormuz ta kasance a rufe yayin tattaunawar ƙawo ƙarshen yaƙin Amurka da Iran ke cikin halin rashin tabbas.
Maniyyatan Najeriya 50,000 ne za su sauke farali a 2026 - NAHCON
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Alhazan Najeriya, NAHCON ta ce maniyyatan ƙasar kimanin 50,000 ne za su sake farali a wannan shekara ta 2026.
Mataimakiyar darakta a sashen yaɗa labaran hukumar, Fatima Sanda Usara ce ta bayyana haka a hirarta da BBC.
A yau ne dai ake fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa ƙasa mai tsarki.
Fatima Sanda Usara ta ce tuni hukumarsu ta kammala dukkan shirye-shirye da suka kamata don gudanar da jigilar maniyyatan cikin nasara.
A baya dai ana yawan samun jinkiri a aikin jigilar alhazan Najeriyar a duk shekara, wanda hakan kan sa wasu alhazan su gaza samun damar sauke faralin, sai dai Fatima, ta ce tuni suka ɗauki mataki kan lamarin.
Hare-haren Isra'ila sun kashe aƙalla mutum bakwai a Lebanon
Aƙalla mutum bakwai ne suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa kan mayaƙan Hezbollah a kudancin Lebanon duk da yarjejeniyar dakatar da wuta.
Sojojin Isra'ila na ci gaba da rusa gine-gine a kudancin Lebanon, ciki har da wani Cocin Katolika da ke wani ƙauyen kan iyaka.
Dakarun na Isra'ila sun ce Hezbollah na amfani da ginin domin harba makaman roka zuwa Isra'ila, zargin da Cocin Katolika a Lebanon ya yi watsi da shi.
Amurka ta karɓi daftarin buƙatun Iran 14
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da karɓar daftarin buƙatun Iran domin tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin ɓangarorin biyu.
Buƙatu 14 ne ke ƙunshe a daftarin na Iran, ciki har da buɗe tasoshin jiragen ruwanta da Amurka ta datse, da biyanta diyyar abubuwan da aka lalata mata a tsawon yaƙin da kuma sakin kadarorinta da aka riƙe
Mista Trump ya ce yana nazarin sharuɗɗan da Iran ɗin ta gindaya cikin buƙatun nata, amma ya ce ba lallai ya amince da su ba.
Kafin yanzu shugaban na Amurka ya ce gwamnatin Iran ta matsu a cimma yarjejeniya, kuma a cewarsa gwamnatin ƙasar ta ragu.
Yanzu dai Iran ɗin ta ce tana jiran martanin Amurka.
Barkanmu da hutun ƙarshen mako
Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da hutun ƙarshen mako.
Abdullahi Bello Diginza Ke fatan sake kasancewa da ku a wannan lokaci