Saurin da lalacewar dajin Amazon ke yi ya ragu a shekarar 2025 - Bincike

Asalin hoton, Getty Images
Wani bincike da masana kimiyya na Amurka suka gudanar ya gano cewa saurin da lalacewar dajin Amazon ke yi ya ragu a shekarar 2025, bayan asarar da ba a taba samun irinta ba a tarihi a 2024.
Masu binciken sun ce hakan ya fi nasaba da kokarin da ƙasar Brazil ta yi na dakile sare dazuzzuka a yankin Amazon.
Sai dai binciken, wanda cibiyar World Resources Institute da kuma jami'ar Maryland suka gudanar ya kiyasta cewa har yanzu ana asarar kusan murabba'in kilomita dubu arba’in da uku na tsofaffin dazuzzukan.
Wannan yanki ya yi daidai da girman ƙasar Denmark, ko kuma daidai da bacewar filayen ƙwallon ƙafa goma sha ɗaya a kowane minti.
Binciken ya nuna cewa duk da cewa tsauraran dokokin kare muhalli na iya yin tasiri, har yanzu asarar filayen dazukan ta zarce wadda ake samu shekaru goma da suka gabata yawa.
Masana kimiyyar sun kuma yi gargadin cewa ƙaruwar yanayin zafi na iya ƙara haddasa gobarar daji a ƙarshen wannan shekara.


