Kuwait ta kunna na'urar da ke kare sararin samaniyarta
Sojojin ƙasar Kuwait sun fitar da wata sanarwa a safiyar yau Alhamis, inda suka bayyana cewa tsarin kariyar sararin samaniyar ƙasar na dakile “harin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa na abokan gaba” bayan abin da jami’an ƙasar suka kira “hari daga Iran.”
A safiyar Laraba, Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran da kuma sojojin Iran sun sanar da kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa kan sansanonin sojin Amurka da ke Bahrain, Jordan da Kuwait, a matsayin ramuwar gayya ga hare-haren saman da Amurka ta kai.
Sai dai, zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, babu wata sanarwa daga hukumomin sojin Iran da ta tabbatar da sabbin hare-haren makamai masu linzami ko jiragen sama marasa matuƙa da ƙasar ta kai.
Sanarwar Kuwait ta nuna ci gaba da zaman ɗarɗarwa na ci gaba kan rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da hukumomi ke sa ido kan halin da ake ciki da kuma yiwuwar ƙarin tashe-tashen hankula.