Shirinmu na murƙushe Iran ba zai ɗuki lokaci ba - Trump

Asalin hoton, Getty Images
Kwana guda bayan harin da aka kai wa Iran a daren jiya, Donald Trump ya bayyana a wani taron manema labarai a ofishinsa da ke Fadar White House cewa sabon shirin sojin Amurka na murƙushe ba zai ɗauki lokaci mai tsawo ba.
Ya bayyana hare-haren na daren jiya a matsayin “masu tsananin ƙarfi sosai,” yana mai cewa Amurka a shirye take ta sake kai wa Iran hari a kowane lokaci idan buƙatar hakan ta taso.
Mista Trump ya ce Iran na ƙoƙarin ƙera makami mai linzami da zai iya jefa nakiyoyi, kuma Amurka ta lalata wannan shiri.
A cewarsa, Iran ta kuma kasance tana sake gina tsarin radar da na makamai masu linzami, waɗanda hare-haren Amurka suka kai wa hari.
Trump ya jaddada cewa sojojin Amurka za su ci gaba da sa ido kan duk wani yunkuri da Iran za ta yi na sake ƙarfafa ƙarfin sojinta, kuma za su ɗauki mataki idan suka ga ya zama dole.

















