Ana kaɗa ƙuri'ar ƙayyade yawan al'ummar Switzerland

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
Masu kaɗa ƙuri'a a ƙasar Switzerland na yanke hukunci a yau kan wata shawara da ke neman kayyade yawan al'ummar ƙasar zuwa miliyan goma.
Fiye da kashi ɗaya cikin huɗu na mutanen ƙasar miliyan 9.1 ba 'yan ƙasa ba ne, kuma wannan shiri ya fito ne daga jam'iyyar masu ra'ayin riƙau ta Swiss People's Party.
Jam'iyyar ta ce idan masu kaɗa ƙuri'a suka amince da shawarar, hakan zai rage matsin lamba kan gidaje, da ayyukan gwamnati da kuma muhalli.
Sai dai gwamnati da shugabannin harkokin kasuwanci da kuma sauran manyan jam'iyyun siyasar ƙasar na adawa da wannan mataki, suna masu cewa hakan zai hana Switzerland samun ma'aikatan da take matuƙar buƙata, tare da kawo cikas ga yarjejeniyoyin da aka daɗe ana kullawa da tarayyar Turai.
Babu wata ƙasa da ta taɓa yunƙurin sanya iyaka kai tsaye ga yawan al'ummarta a baya, kuma ana sa ran duniya za ta zura ido sosai kan sakamakon ƙuri'ar da za a yi a Switzerland.



