Ko kankana na iya maye gurbin maganin karfin maza?

Asalin hoton, Getty Images
Kankana tana da matuƙar amfani kuma tana da fa'idodi da yawa ga lafiyar jiki.
Masu bincike a Amurka sun kwatanta aikin kankana a jikin mutum da irin wanda maganin karfin maza ke yi.
Kankana tana ɗauke da sinadarin citrulline, wani sinadari mai kama da wanda ke cikin maganin karfin maza da ake kira Viagra.
A cewar Ma'aikatar Lafiya ta Burtaniya, Viagra magani ne da ake amfani da shi don magance matsalar rashin karfin mazakuta.
Ƙwayar Viagra, wadda a wasu lokutan ake kira sildenafil, ƙwaya ce da aka samar don inganta yadda jini ke zagaye a jikin mutum, kuma asalin aikin maganin shi ne buɗe jijiyoyi domin jini ya samu wucewa cikin sauƙi.
Aikin da Viagra ke yi a jijiyoyin jini ya yi kama da wanda citrulline ke yi, kuma ana samun wani sinadari citrulline a cikin kankana.
Sinadarin citrulline da ke jikin kankana yana sa janyoyin jini su warware, lamarin da ke infants zagayen jini a jikin mutum.
Haka nan kuma idan jini na wucewa cikin sauƙi a jijiyoyi mutum zai samu ƙarfin sha'awa sosai.
Cibiyar bincike kan tsirra ta Texas a Amurka ce ta gudanar da binciken.
"Mun sani cewa kankana tana da amfani ga lafiya. Bincike na ci gaba da zaklo alfanun ta. Ana ƙara sanin fa'idar da ke tattare da shan kankana,'' in ji Dr. Bhimu Patel, wanda ya jagoranci bincike kan kankana.
Sauran amfanin kankana

Asalin hoton, STEVE EVANS/ WIKIMEDIA COMMONS
- Kankana tana ƙara wa jiki ruwa: Ruwa na da matuƙar muhimmanci a jiki. Ƙarancin ruwa a jiki yana janyo gajiya da ciwon kai da hawan jini da kuma ciwon jiki. Kashi casa'in da biyu cikin ɗari na kankana ruwa ne, kuma tunda jiki yana buƙatar ruwa, shan kankana na da amfani sosai.
- Tana da amfani wajen kula da ƙibar jiki: Kankana tana da ƙarancin sinadarin calories, don haka ko mutum ya sha da yawa babu wani haɗarin ko za ta ƙara mashi ƙiba. Saboda yawan ruwa da take da shi, tana sa ƙoshi nan da nan, kuma tana hana jin yunwa da kuma ƙoshin da ya wuce ƙima.
- Tana ƙara lafiyar fata da ido: Sashin da ke da launin ja a jikin kankana yana ɗauke da sinadarin carotenoid mai yawa. Wannan sinadari yana da muhimmanci sosai wajen gyaran fata. Yana kuma sinadarin beta-carotene vitamins, mai ƙara lafiyar ido da ƙarfin fata.
- Tana rage haɗarin kamuwa da ciwon suga da kansa: Kankana tana da sinadarin lycopene, wanda jiki ke saurin naɗewa. Binciken da aka yi ya nuna cewa lycopene na rage haɗarin kamuwa da kansa da kuma ciwon suga.











