Me ya sa muke son a riƙa tunawa da mu bayan mutuwarmu?

    • Marubuci, Molly Gorman
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A lokacin da likitoci suka gano cewa mahaifin Beth Hunter na ɗauke da cutar Alzheimer da ba a warkewa, sai ta tambaye shi izinin naɗar hirarsu, saboda ta riƙa kunnawa tana saurara bayan shekaru.

Amma sai ya ƙi amincewa. Shi ba irin mutanen nan ne da suke shaƙuwa da wasu, a cewar Hunter - ya ƙi fuskantar cutar tasa, kuma ba ma ya son yin maganar mutuw.

A maimakon haka, ya fifita rubuta labaransa na yaƙi, kuma ya riƙa rubuta su ne da hannunsa, kafin ya bai wa wani ya buga masa a kwamfuta.

Yayin da tsofaffin da suka kusa mutuwa suka fi burin barin wani abu da za a riƙa tunawa da su, wasu masana sun ce ya kamata a ce an fara hakan tun lokacin ƙuruciya.

Binciken masana masu yawa ya nuna cewa fahimtar abin da ɗan'adam ya fi so zai taimaka wajen yin wani abu da zai taimaka wa masu tasowa bayan mun mutu.

"Amma mafi yawan mutane ba sa tunanin hakan," a cewar Hunter, Farfesa a Jami'ar Bowling Green da ke jihar Ohio a Amurka, kuma ƙwararriya a fannin tunawa da mutane bayan mutuwarsu.

Abin tunawa kan samu ta hanyoyi da dama koda mutum bai sani ba, ''kowane mutum na barin abin da za a riƙa tunawa da shi, ko da sun sani ko ba su sani ba,'' in ji Huntur.

Yakan iya zama dukiya ko kadara ko wata fikira kamar waƙa ko rubutu ko zane da sauransu.

Masana sun karkasa abin tunawa da mutane bayan mutuwarsu zuwa manyan kaso uku.

Na farko zuri'ar da ya bari, na biyu kuma addini da ala'adunmu, da ɗabi'unmu, sai na uku dukiya da kadarorin da muka bari.

Barin zuri'a

Ga mutane da dama babban abin tunawa da mutum bayan rasuwarsa shi ne zuri'arsa, ƴaƴa da jikoki da ya haifa da iyayensa idan suna raye da ƴan'uwansa da kuma matarsa.

Barin zuri'a ya ƙunshi barin wasiyyar amfani da wasu sassan jikin gawarka domin binciken kimiyya.

Kusan Amurkawa miliyan 170 ne suka yi rajistar wasiyyar amfani da wasu sassan jikinsu bayan sun mutu, sai dai uku cikin kowane 1,000 ne kawai ke mutuwa a yanyin da ke bayar da damar aiki da wasiyyar.

Wasu mutanen ma kan yi fatan bayar da duka gawar tasu domin binciken kimiyyar.

Abin da hakan ke nufi shi ne amfani da gawar tasu wajen ilimantar da ɗaliban da ke koyon aikin likitanci ko kuma yin binciken kimiyya, kamar samar da sabbin hanyoyin warkar da cutuka.

A shekarar 2021 fiye da gawarwaki 26,000 aka samu domin wannan aiki a Amurka.

A wani bincike na baya-bayan nan fiye da mutum 100 ne suka yi rajistar wasiyyar amfani da gawarwakinsu, kuma ilimin kimiyya babban dalilin da ya sa suke yin hakan.

Wasu dalilan sun haɗa da tallafa wa rayuwar wasu da bayar da kulawar lafiya, amma wani abin jan hankali shi ne kusan kashi 16 na masu wasiyyar amfani da gwarwakin nasu na yi ne domin a riƙa tunawa da su bayan mutuwarsu.

Kuma haka batun yake ga masu ɗauke da cutukan gado.

Kamar fitacciyar ƴargwagwarmayar nan marigayiya, Susan Potter, wadda ta yi fama da cutaka masu yawa, da suka haɗa da kansa da ciwon siga ta yi wasiyyar bayar da gawarta domin koyawa sabbin likitoci aiki a jihar Colorado ta Amurka.

Matsalarta ta daban ce, yayain da ta amince a daskarar da gawarta kafin a daddatsa ta zuwa yanka 27,000.

Inda aka riƙa ɗaukar hoton kowane yanka, domin bai wa ɗaliban damar ganin kowane sassa na jiki da tsoka.

Abubuwan tunawa masu daraja

Tallafa wa mutane da wasiyyar bai wa wasu dukiyarka ko amfani da kadarorinka domin taimaka wa wasu na daga cikin abubuwan tunawa masu ƙima.

Litattafai da muƙalu na daga cikin abubuwa masu daraja na tunawa da tarihin mutanen da suka shuɗe.

Bayar da wani gini da sunan wani mutum a jiki na daga cikin hanyoyin tunawa da mutanen da suka mutu.

Amma bincike ya nuna cewa abubuwan da mutane da dama ke son bari don a riƙa tunawa da su su ne abubuwan kyautawa rayuwar wasu.

Wani bincike da aka yi a kan labaran wasu mata 38 masu bambantan shekaru da matsalolin lafiya daban-daban ya gano cewa mutane sun fi son a riƙa tunawa da wani kyakkyawan hali nasu.

Musamman sukan yi haka ta hanyar yin wani abu ta amfani da ɗabi'arsu da addininsu wajen rubuta ko naɗar bayanansu da tarihin danginsu, ko wani muhmmin abu da suka cimma a rayuwarsu, kamar dai suna bayar da tarihin rayuwarsu da kansu.

Abin abin tunawa mai daraja na da amfani mai yawa ga mutane.

Fargabar mutuwa

Yayin da ɗan'adam ya shafe dubban shekaru yana tunani kan abubuwan tunawa da zai bari, masana sun fara bincike kan batun shekara 75 da suka gabata.

A shekarar 1950, Erik Erikson, ƙwararren masanin ɗabi'un mutane ya ƙirƙiro kalmar 'generativity' wadda ya bayyana da tsananin yadda mutane kan mayar da hankali wajen samar wa masu tasowa abin amfaninsu, domin a riƙa tunawa da su.

Ya saka ''generativity'' a matsayin mataki na bakwai na ginuwar tunani, inda ya ce muhimmin mataki ne ga mutane masu matsaicin shekaru.

Erikson ya ce idan mutum ya gaza samun ''generativity'' hakan zai shafi makomarsa a rayuwa, kuma hakan ka iya illa ga lafiyarsu.

Haƙiƙa akwai abin da ke jan hankalin mutane wajen yin abin da za a riƙa tunawa da su bayan mutuwarsu - wanda kuma shi ne tsaron mutuwa.

"Fargabar mutuwa na sa mutane su riƙa tunanin cewa me zai faru idan suka suka mutu?'' a cewar Farfesa Kimberly Wade-Benzoni na Jami'ar Duke da ke Carolina ta Arewa.

"A duk lokacin da ɗan'adam ya tuna mutuwa, yakan ji fargabar zuwanta, zai yi fatan ya ci gaba da rayuwa.''

Tunanin abin da mutum zai bari domin tunawa da shi bayan mutuwarsu kan sa mutane su rage fargabar mutuwa, zuwa tunanin abin da za su bari domin a riƙa tunawa da su.

Rubuta abin da ka ke son a riƙa tunawa da kai

Duk da ƙaruwar cibiyoyin bincike, abin da ya sa muke son a riƙa tunawa da su d abubuwa masu kyau bayan sun mutu na da dalilai masu yawa.

Mayar da hankali a tsawon rayuwarmu kan yadda za a kalle mu bayan mutuwarmu kan ɗauke hankalinmu daga jin daɗin rayuwa, a cewar Bering.

Tunani kan samar da abin da za a riƙa tuna mutum kan sa mutane ɗaukar matakai kan abubuwan da suke son bari.

Hakan zai sa mutane su inganta ayyukansu na alkairi, kamar gwagwarmayar kula da muhalli ko sadaukar da dukiya ga ƙungiyoyin agaji ko binciken lafiya.

Ƴankasuwa, a wasu lokuta kan duba yiwuwar kafa kasuwancin da zai taimaka wa al'umma, ba sai lallai don samun riba ba, a cewar Wade-Benzoni.