Liverpool ta nace wa Olise, Manchester United na harin Truffert

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu Liverpool na sha'awar dan wasan gefe na Faransa, Michael Olise, mai shekara 24, amma Bayern Munich ba ta da niyyar sayar da shi a kasuwar musayar 'yan wasa ta Janairu. (Christian Falk)
Kungiyoyi na ci gaba da nuna sa'awarsu ta sayen dan wasan gaba na Brazil, Richarlison, mai shekara 29, bayan rushewar shirin tafiyarsa daga Tottenham zuwa Vasco da Gama ta Brazil. (UOL - in Portuguese)
Tsohon dan wasan gaba na Brazil, Philippe Coutinho, ya amince da kwantiragin wata uku da kungiyar Santos.
Dan wasan mai shekara 34, wanda ya taba buga wa Liverpool da Aston Villa wasa, na son tantance ko zai ci gaba da taka leda bayan ya zama ba tare da kungiya ba tun bayan barinsa Vasco da Gama a watan Fabarairu. (Globo - in Portuguese)
Manchester United na sa ido sosai kan dan bayan hagu na Bournemouth kuma dan kasar Faransa, Adrien Truffert, mai shekara 24, wanda ake kimanta darajarsa kan fam miliyan 60. (Teamtalk)
Liverpool na ci gaba da sha'awar dan wasan tsakiya na Serbia, Aleksandar Stankovic, mai shekara 21, wanda ke buga wa Inter Milan wasa, bayan da ta nemi bayani a kansa a wannan bazarar. (Teamtalk)
Crystal Palace ba ta hakura da yunkurinta na daukar dan bayan tsakiya na Faransa, Raphael le Guen, mai shekara 20, daga Brest ba, bayan ta kasa kammala cinikinsa a bazarar nan. (Ouest-France via SportWitness)
Dan wasan tsakiya na Senegal, Lamine Camara, mai shekara 22, ya ce hankalinsa na kan kungiyar Monaco bayan rushewar cinikinsa zuwa Chelsea a ranar karshe ta kasuwar musayar 'yan wasa. Ya kuma ce mai yiwuwa wasu damammaki su sake tasowa nan gaba. (ESPN)
Ba a sa ran tsohon dan wasan gefe na Ingila, Jadon Sancho, mai shekara 26, zai koma wata sabuwar kungiya nan kusa ba, yayin da yake ci gaba da nazarin zabin da ke gabansa bayan barinsa Manchester United a watan Yuni. (Football Insider)
Kungiyoyin Lazio da Parma sun bi sahun Everton wajen nuna sha'awar daukar tsohon dan wasan gaba na Argentina, Mauro Icardi, mai shekara 33, wanda a yanzu ba shi da kungiyar da yake wasa bayan barinsa Galatasaray a bazarar nan. (Corriere dello Sport - in Italian)
Malaga na nazarin yiwuwar daukar tsohon dan wasan gaba na Manchester United da Faransa, Anthony Martial, mai shekara 30, wanda ya zama ba tare da kungiya ba bayan barinsa Monterrey ta Mexico a watan Yuni. (Mundo Deportivo - in Spanish)













