Matakan kariyar kai 7 da ya kamata malaman addini su ɗauka a Arewacin Najeriya

..
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Kisan gillar da aka yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, a jihar Katsina ya girgiza al'ummar Musulmi da masu ruwa da tsaki a harkokin addini a Najeriya, tare da sake jawo hankalin jama'a kan matsalar tsaro da kariyar malaman addini a ƙasar.

Rahotanni sun nuna cewa wasu mahara dauke da makamai sun harbe malamin tare da wani abokinsa a wajen gidansa da ke karamar hukumar Dutsin-Ma a daren ranar 26 ga Oktoba, 2026, kafin su tsere daga wurin. Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa an fara bincike domin gano wadanda suka aikata laifin.

Masana harkokin addini na ganin cewa wannan kisan na iya haifar da fargaba tsakanin malamai, musamman waɗanda ke gudanar da wa'azi kan batutuwan da suka shafi gyaran al'umma, zaman lafiya da kuma yaƙi da aƙidar tsattsauran ra'ayi.

Dalilin hakan ne BBC ta tuntuɓi Barista Bulama Bukarti, masani kuma mai binciken tsaro a Afirka domin sanin matakan da ya kamata malaman addinu su ɗauka domin kare kansu daga barazanar tsaro.

Idan Malami ya dage a kan wata karantarwa, hakan na janyo hankalin mutane, musamman waɗanda ba su yarda koyarwarsa ba ga ayyukansa. Bukarti ya ce duk da akwai bambancin aƙida tsakanin Sheikh Jaʼafar Adam da Albani da kuma Sheikh Masussuka, gaba ɗayansu sun haɗu wajen ƙoƙarin kore zubar da jinin mutane da sunan addini.

"Hakan na iya zama dalilin da ya sa masu adawa da wannan koyarwar tasu su kai musu hari, kuma rayuwarsu na cikin hatsari."

Ɗaukar barazana da muhimmanci

Masanin tsaron ya ce duk da cewa malamai na koyar da tawakkali da kuma mayar da lamari ga Allah, ana yawan yi wa malamai barazana saboda saɓanin raʼayi.

"Abin da yakamata shi ne su riƙa ɗaukar irin wannan barazana da muhimmanci, su kuma tabbatar da sun kai rahoto ga musamman ƴansanda da jamiʼan tsaro na farin kaya (DSS) don su bincika."

Saboda haka Bulama Bukarti ke ganin ya dace malaman su riƙa bibiyar irin waɗannan barazana daga masu adawa da su.

'Malamai su riƙa kula da tsaron muhallan da suke zama'

A cewar Barista Bulama Bukarti, an fi kai wa malaman hari cikin duhun dare ko asubahi, lamarin da ke nuna cewa akwai hatsari a waɗannan lokutan.

"Yawancin malaman da aka kai wa hari an kai musu ne yayin da suke fitowa daga gidajensu ko wuraren karatu da daddare ko asubahi."

Saboda haka akwai buƙatar malamai su sanya fitilu masu haske da kuma kyamarar CCTV a ƙofar gidansu da kuma masallatai domin kiyaye kai musu hari a cikin duhu.

Ɓadda-bami

A cewar masanin tsaron, yana da kyau a matsayinsu na mutane masu muhimmanci su riƙa sauya hanyoyi da kuma lokutan da suka fita zuwa uzurinsu.

"Ya kamata malamai su riƙa canza hanyar da suke bi da kuma abin hawa a lokuta mabambanta domin kawar da tunanin mutane."

Kafa matakan tsaro a gidajensu

Masanin tsaron ya ce yana da kyau malaman addini su sanya matakan tsaro a gidaje da masallaci da kuma wuraren da suke koyarwa.

Ya ce yana da kyau su tabbatar da cewa ba kowa ne zai iya ganin su a lokacin da suka ga dama.

"Ya kamata su samu jamiʼan da za su riƙa tambayar mutane game da dalilinsu na zuwa ganin malamin, sannan masu ƙarfi a cikinsu na iya sayen naʼurar duba mutane domin tabbatar da babu ƙarfe ko bindiga."

Taka-tsantsan kafin manyan taruka

Barista Bukarti ya ce ana yawan kai wa malamai hari gabanin wani taro da suka shirya ko kuma wani babban alʼamari a ƙasa.

"Idan ka duba an kai wa Sheikh Masussuka hari ne ana daf da gudanar da wani taron haɗin kai tsakanin alʼumma da ya shirya. Haka ma an kashe Sheikh Jaʼafar gabanin babban zaɓen (2007)."

Saboda waɗannan lokuta na da hatsari kuma ya kamata malamai su ƙarfafa tsaronsu yayin da ake irin wannan yanayi.

Ɓoye bayanan kansu

Barista Bukarti ya bayar da shawarar malamai su samu gogaggun maʼaikatan tsaro da na yaɗa labarai a tare da su.

A cewarsa, hakan zai rage hatsarin kai musu hari ta hanyar riƙe bayanai masu muhimmanci dangane da wurin da suke zaune ko suka kai ziyara.

Kazalika, masanin shariʼar ya bai wa gwannati shawarar ta riƙa taimaka wa malaman da jamiʼan tsaron domin ba su kariya.

Samun ƙwarewa game da agajin gaggawa

A cewar Barista Bukarti, ya kamata malaman addini da ƙungiyoyi su bai wa mabiyansu horo na musamman a kan agajin gaggawa (First Aid).

"Abu na farko ya kamata malamai da ƙungiyoyin addini su samu cikin mabiyansu wasu da za samu horo game da ba da agajin gaggawa, ta hanyar tsayar da jini da sauransu."

Hakan ya ce akwai matuƙar muhimmanci a masallatai a samu wasu mutane da suka san inda asibitoci suke da kuma hanyoyin da za a bi domin zuwa cikin gagggawa."