Ko ya kamata mata su riƙa haihuwa a rigingine?

    • Marubuci, Lucy Sherriff
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shekaru aru-aru da suka shuɗe, mata a faɗin duniya sukan haihu ne a tsaye - ko su durƙusa a gwiwoyinsu, ta hanyar amfani da kujera, ko su tsuguna.

Ana ganin ma durƙusawa yayin naƙuda na iya ƙara faɗin ƙashin ƙugu da aƙalla santimita 2.5cm, kuma hakan yana sa a samu sauƙin haihuwa.

To me ya a yanzu mata suke kwantawa a rigingine idan za su haihu?

"Akwai wannan tunanin da ya shiga kan ma'aikatan lafiya da masu juna biyu ke da shi a lokacin haihuwa," in ji Janet Balaskas, shugabar cibiyar Active Birth Centre a Birtaniya UK, kuma ta wallafa littafai da dama kan yadda mata za su haihu.

A 1982, Balaskas ta wallafa wani littafi kan "dabarun haihuwa cikin sauki", wanda ya sa ƙungiyarta ta yi suna.

"A duk faɗin duniya, a dubban shekaru da suka wuce, mata sun yi naƙuda kuma sun haihu ne ta hanyar yin tsuguno," kamar yadda aka bayyana a cikin littafin. "A kowace ƙabila... ana amfani da salo iri ɗaya ne."

Yawancin mata a kasashen da suka ci gaba ana sa su bin wannan tsarin a asibiti, in ji Balaskas.

"Wannan salon bai da ma'ana, kuma yana haifar da ruɗani a lokacin a lokacin haihuwa, da maida mace mai naƙuda da haihuwa wata mara lafiya sosai," in ji ta.

"Babu wasu nau'ukan halittu da su ke amfani da wannan salon a wannan zamanin"

Wasu masanan kuma sun yarda da tsarin. A ganinsu, haihuwa a ta rigingine "shi ne wayewa," in ji Hannah Dahlen, Farfesa a fannin ungonzoma a jami'ar Australia.

Ana yi wa juna biyu kallon rashin lafiya

Bai wuce shekaru 300 zuwa 400 ba da mata suka fara haihuwa ta kwance a kan bayansu. Ya kamata su gode wa wani Bafaranshe mai suna François Mauriceau. Ya yi iƙirarin cewa sauya salon zai fi daɗin haihuwa ga mata kuma ya fi sauƙi ga likita namiji a lokacin karɓar haihuwar.

Mauriceau yana ganin juna biyu a matsayin abu na rashin lafiya ne. A littafinsa da wallafa a 1668 kan haihuwa, ya ba da shawarar cewa: "Hanya mafi dacewa wajen haihuwa ita ce a kan gado, domin a rage wahalar ɗaukar mutum bayan an haihu."

Sai dai wasu masanan sun ce sauya salon yadda ake haihuwa ya samo asali ne a lokacin wani Bafaranshen da suka yi zamani tare da Mauriceau mai suna Sarki Louis XIV.

"An ruwaito cewa saboda yadda Sarki Louis XIV ya ke jin daɗin kallon lokacin da mata ke haihuwa, shi ya damu a kan yadda ake kare masa abin da ya kamata ya gani idan aka yi amfani da kujera, har ta kai ga ya ba da shawarar a sauya yadda mata ke haihuwa," kamar yadda Farfea a kwalejin McDaniel da ke Amurka, Lauren Dundes, ta wallafa a wata maƙala kan nazarin yadda mata ke haihuwa a 1987

"Sai dai ba kowa ya san tasirin da yunƙurin sarkin ya yi ba, ko da yake ana ganin al'adar gidan sarauta za ta iya taka rawa wajen ɗaukar matakin," in ji ta.

Ko ma dai ta yaya ne aka canza yadda mata ke haihuwa, abin la'akari shi ne kowa akwai yadda haihuwarta ta zo mata.

"Haihuwa abu ne da ba makawa, inda wasu matan suka son su haihu a gida kuma abu ne da yanzu ba kowa ke yi ba," in ji Balaskas

Abin da kimiyya ta tabbatar

Babban dalilin da yasa mata suke haihuwa a tsugune a dubban shekaru da suka shuɗe shi ne ya fi sauƙi saboda nauyin ciki. Dole ne sai jariri ya gangaro zuwa ƙasa daga mahaifa, kuma yanayin nauyin yana taimakawa.

Bayanai sun cewa, mata za su fi son su haihu a rigingine ta ciki a madadin kwanciya a kan bayansu, inda wasu suka fi tsugunawa ko kuma durƙusawa kan gwiwoyinsu tare da ɗora hannunsu a ƙasa.

Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2013 tsakanin mata 5,200, ya bayyana cewa da dama sun fi son su haihu a tsugune a madadin kwanciya kan bayansu, kuma hakan yana rage yiwuwar yin tiyata domin cire jariri da barazanar sanya shi cikin kulawar gaggawa.

An kuma gano cewa mata sun rage amfani da salon haihuwa a tsugune, idan suna naƙuda.

"Haihuwa a tsugune yana taimakawa uwa da jaririnta," kamar yadda Dahlen ta wallafa a shekarar 2013. Ta lissafo wasu alfanu da hakan ke da shi, irinsu rage zafin naƙuda da buɗewar hanyar da yaro zai fito da sauransu.

A shekarar 2011, Dahlen da abokan aikinta sun gudanar da wani bincike kan matan da ke naƙuda domin gano ko yanayin yadda ake haihuwa yana da alaƙa da salon da mata ke bi.

Sun gano cewa mata da dama sun fi son haihuwa a tsugune musamman a matakin farko da na biyu saɓanin yadda aka saba a al'adance - kuma kaso 82% na mata sun haihu ne a asibitoci sai kuma 25% da suka haihu a gida.

A yanzu ana wayar da kan mutane a ƙasashen yamma game da salon haihuwar, in ji Balaskas - abin da zai ba mata damar haihuwa cikin sauƙi, ta hanyar amfani da salon tsugunawaa a madadin kwanciya kan baya. Sai dai ana samun ƙaruwar matan da ake yi wa mata tiyata wajen haihuwa.

"A Birtaniya, yadda ake haihuwa ya sa an canza wasu tsare-tsare a cibiyoyin karɓar haihuwa," in ji ta.

Ta ce wannan salon ya fi faruwa a asibitoci domin ba mata damar yin walwala yadda suke so. "Abin da bai faru a shekaru 50 da suka gabata ba."

Wasu ƙa'idoji da wata cibiyar bincike han samar da ingantaccen kiwon lafiya a Birtaniya ta fitar, ya shawarci mata da ke naƙuda "su daina kwanciya kan bayansu a lokacin da su ke matakin farko da na biyu na naƙuda, inda aka ba su shawarar su yi amfani da wasuu dabaru da salo na daban da suka fi fa'ida."

Sai dai an ce ilimi kogi ne, in dai aka ci gaba da wayar da kan mata game da cewa suna da zaɓi wajen haihuwa, zai fi ba su damar zaɓar hanyoyin da suke so.

"Wayar da kan mutane kan dabarun haihuwa zai taimaka," in ji Eileen Hutton, wata ungonzoma a jami'ar McMaster da ke Canada.

"Idan aka yi nazarin tunanin mutane kan yadda ake haihuwa a rubuce-rubuce da kuma fina-finai ko a talabijin, suna nuna cewa ba a fahimci yadda ya kamata a haihu ba. Idan har aka wayar da kai, hakan zai taimaka,"