Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya rage wa Arsenal bayan gaza ɗaukar Champions League?
Yayin da Arsenal ta kammala bikin murnar lashe kofin Premier League a bana da rawar da ta taka a kakar nan a gasar Champions League, yanzu hankalinta ya koma kan yadda za ta ɗora a kan nasarar da ta samu da kuma gyara kura-kuren da ta yi.
Kenan dama tana ga koci Mikel Arteta kan yin duba na tsanaki kan irin rawar da Gunners ta taka a kakar nan da nasarar da ta samu da hanyoyin da ta bi ta kai ga wannan bajintar.
Tuni dai darajar Arteta ta karu a Arsenal, saboda jan ragamar ƙungiyar zuwa ɗaukar Premier League a karon farko bayan sheakara 22 da zuwa wasan karshe a Champions League — kuma yanzu ya rage ga Arsenal ta aiwatar da shirinta na tunkarar kaka mai zuwa da za a fara a cikin watan Agusta.
Bayan rashin nasara a wasan karshe a Champions League da Paris St-Germain a ranar Asabar, kocin Arsenal ya ce akwai "muhimman shawarwari" da dole a yanke domin kai ƙungiyar zuwa mataki na gaba.
BBC Sport ta duba wasu daga cikin muhimman batutuwan da za a fuskanta a cikin makonni masu zuwa, ciki har da jerin ƴan wasan da ake nema kamar Morgan Rogers na Aston Villa da kuma Eli Junior Kroupi na Bournemouth.
Sabuwar yarjejeniya ga koci Arteta
Babban batun da ke gaban Arsenal a wannan bazarar shi ne kammala sabuwar yarjejeniyar tsawaita zaman koci, Mikel Arteta, wanda kwantiraginsa zai kare a ƙarshen kakar wasa mai zuwa.
BBC Sport ta bayyana a watan da ya gabata cewa an dan dakatar da tattaunawar sabunta kwantiragi tsakanin Gunners da kociyan, domin Arsenal ta mayar da hankali kan ƙarshen kakar wasa.
Yanzu da yake Gunners ta kammala kakar bana da lashe kofin Premier League bayan shekara 22, za ta ci gaba da tattaunawa da Arteta, domin tsawaita zamansa a Emirates.
Ba a sa ran za a kammala cimma yarjejeniya, domin Arteta yana hutu a yanzu haka.
Sai dai an fahimci cewa an samu ci gaba mai kyau a tattaunawar farko, kuma a Emirates akwai cikakken fata cewa lamarin "lokaci ne kawai", za a samu yadda ake bukata tsakanin Arsenal da kuma kociyan mai shekara 44.
Duk da haka, har yanzu akwai ɗan taka-tsantsan a Arsenal, amma jami'anta na mayar da hankali wajen tabbatar da an cimma yarjejeniya kafin a fara kakar wasa mai zuwa.
Majiyoyi sun shaida wa BBC Sport cewa sabon kwantiragin, wanda zai kasance aƙalla na shekara uku, zai kasance da ƙarin albashi mai yawa fiye da na yanzu.
Arteta yana samun kusan fam miliyan 10 a shekara, tare da ƙarin fam miliyan 5 idan Arsenal ɗin ta samu tikitin Champions League.
Sabon kwantiraginsa zai sa ya zama koci mafi yawan albashi a Ingila, bayan da Pep Guardiola ya yanke shawarar barin Manchester City.
Kwantiragin Guardiola ya kai kusan fam miliyan 20 a shekara, kuma Arteta zai kusanci irin wannan matakin na samun kuɗi.
Waɗanne ƴanwasa za su tsaya waɗanne za su tafi?
Arteta ya fara shirye-shirye a Arsenal don tunkarar kakar wasa mai zuwa, inda Arsenal ke neman ɗan wasan tsakiya, ɗan gaba, da kuma ɗan baya mai bugawa daga gefe a kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo.
Sai dai ba zai zama abu mai sauƙi ba.
Ganin cewa Arsenal ta kashe kusan fam miliyan £250 a kakar da ta gabata kan sayen sababbin ƴan wasa, tare da sabunta kwantiragi da kuma biyan manyan alawus ga ƴan wasa saboda nasarar Premier League, Arsenal na ƙoƙarin tabbatar da cewa kashe kuɗin zai zama kan ka'ida da hukumar gasar Premier League ta gindaya.
A ɓangaren ƴan wasan gaba, akwai ƴan wasa uku da ake sa ran za su kasance a jerin zaɓin Gunners: Rogers na Aston Villa da Kroupi na Bournemouth da kuma Julian Álvarez na Atlético Madrid.
Ana sa ran Rogers da Kroupi za su kai darajar sama da fam miliyan 80 kowanne, yayin da Álvarez—wanda Barcelona ke sha'awa ɗauka—ana ƙiyasta farashinsa sama da fam miliyan 120.
Duk wani sayen Rogers ko Kroupi ko kuma Álvarez zai iya dogara ne da sayar da wasu ƴan wasanta na gaba, kenan tana jiran ƙungiyar da za ta sayi Gabriel Jesus da Gabriel Martinelli, yayin da kwantiragin Leandro Trossard zai kare cikin wata 12.
Har ila yau, makomar matashin ɗan wasan, Ethan Nwaneri, wanda ya dawo daga buga wasannin aro a Marseille, babu tabbas, domin Arsenal na tunanin sayar da shi, wanda zai kara kawo riba ga asusun ƙungiyar.
Arsenal kuma na shirin sauraron tayin sayen Christian Nørgaard da Ben White, yayin da Fabio Vieira da Reiss Nelson suma za su iya barin ƙungiyar. Jakub Kiwior ya riga ya koma Porto kan fam miliyan 14.7m.
An tattauna yiwuwar ɗaukar Rogers, amma kasancewar Martin Ødegaard da Eberechi Eze suna iya taka rawar gani daga kai hari tun daga tsakiya, ana tunanin mahimmacin ɗaukar Rogers ɗin.
Sai dai saboda Rogers na iya taka rawa daga gefen hagu daga gaba, an lura cewa iya jujjuyawarsa na da amfani sosai a Arsenal.
Sha'awar sayen ɗan wasan mai shekara 23 ɗin gaskiya ce, amma ba Arsenal kaɗai ke son zawarcin ɗan ƙwallon ba, domin Manchester United ma na sa ido kan halin da yake ciki.
Rogers, a cewar rahotanni daban-daban, yana son komawa Arsenal a kaka mai zuwa.
Kroupi kuma wani zaɓi ne ga Arsenal da ta duba, bayan ya ci ƙwallaye 13 a Premier League, wanda ya kafa tarihi a matsayin matashin ɗan wasa mafi yawan zura ƙwallaye a kakarsa ta farko.
Babban burin Arsenal a gaba shi ne ɗaukar Álvarez, duk da cewa Barcelona na matuƙar sha'awa sayen ɗan wasan tawagar Argentina ɗin.
Arsenal ɗin kuma ta yi ƙoƙari kan tuntuɓar ɗan wasan Leicester mai shekara 16, Jeremy Monga, a ƴan makonnin nan.
Ana kallon Monga a matsayin ɗaya daga cikin fitattun matasan ƴan wasa a Ingila, kuma manyan ƙungiyoyi da dama suna zawarcinsa.
Rahotanni sun ce matashin ya buɗe hanyar yiwuwar komawa Arsenal, amma har yanzu ba a tabbatar ba ko barinsa Leicester zai buƙaci ƙungiyar ta ji bahasin kotu.
Rawar da Lewis-Skelly ya taka a bana ka iya hana sayen ɗan wasan tsakiya a Arsenal
Akwai rikitarwa a fannin ƴan wasan da ke taka leda a tsakiya
Ganin matsayin na ɗan wasan da ya fara daga gida, Arsenal ta taɓa tunanin sauraron tayin sayar da Myles Lewis-Skelly, amma rawar da ya taka a ƙarshen kakar wasan bana a matsayin da yake so na taka leda daga tsakiyar fili ya ja hankali sosai. Wannan ka iya sa Gunners ta sake tunani kan makomar ɗan wasan mai shekaru 19 a wannan bazarar.
Arsenal kuma ta tattauna kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na West Ham, Mateus Fernandes, wanda ake sa ran zai bar ƙungiyar, bayan da ta faɗa zuwa Championship da za ta fara a baɗi.
Sai dai, duk da cewa Fernandes da Lewis-Skelly ƴan wasa ne daban a salon wasan da suke yi, ƙwazon Lewis-Skelly da ya yi ka iya sa Arsenal ɗin taa canza tsarinta.
Dangane da masu tsare baya daga tsakiya kuwa, Gunners na duba ɗaukar ɗan wasa mai iya taka rawa a wurare daban-daban, domin ƙara ƙarfin ƙungiyar, inda suka bibiyar Tino Livramento na Newcastle, duk da cewa ɗan wasan mai shekara 23 ya sha fama da rauni a kakar da ta gabata. Wannan matsayi na cikin abubuwan da za a kula da su sosai.
Haka kuma, Arsenal na shirin kammala cimma yarjejeniya kan sabunta kwantiragi ga ɗan wasa, Jurrien Timber.
BBC Sport ta bayyana cewa ƙungiyar ta fara tattaunawa kan sabuwar yarjejeniya tun kakar da ta gabata, kuma tattaunawar na gab da kammaluwa.
Haka kuma Arsenal ta nuna niyyar fara tattaunawa da babban ɗan wasa mai taka leda daga tsakiya, Declan Rice, kan tsawaita masa kwantiraginsa.
Sai dai watakila a ci karo da cikas kan batun sabunta yarjejeniyar, Mikel Arteta da Timber da Rice, ba kamar yadda wasu ke ganin za a kammala komai cikin sauki ba.
Saboda haka, sayar da wasu ƴan wasa zai fi zama muhimmanci a wannan bazarar.
Har ila yau, har yanzu ba a san ko Arsenal za ta yarda ta sadaukar da wani daga cikin ƴan wasanta na 11 farko ba, domin daidaita kashe kuɗin ƙungiyar daidai samu ba.