Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Milner ya yi ritaya bayan shekara 24 yana taka leda

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga Litinin 01 zuwa Lahadi 07 ga watan Yunin 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Watakila Palace ta ɗauki Sage a matakin sabon koci, Premier League

    Ana sa ran kocin Lens, Pierre Sage, zai tattaunawa da Crystal Palace a farkon wannan mako yayin da ƙungiyar Premier League ke neman wanda zai maye gurbin Oliver Glasner.

    Palace (wanda ake yi wa lakabi da Eagles) na fuskantar kalubale a kokarin ɗaukar Andoni Iraola, wanda ake sa ran zai fara tattaunawa a hukuma da Liverpool a kwanaki masu zuwa domin maye gurbin Arne Slot da aka kore a ranar Asabar.

    Palace wadda ta lashe Conference League ta gabatar da tayin aiki mai tsoka ga Iraola, amma da alama yana kan hanyar zuwa wani wuri, yanzu Crystal Palace na duba wasu zaɓuɓɓuka daban.

    Ƙungiyar ta kudancin London, ƙarƙashin jagorancin shugaba, Steve Parish, ba zai yi gaggawa wajen yanke hukunci ba kan sabon koci, domin suna nazarin wasu sunaye daban.

    Daga cikin waɗanda ake dubawa akwai Sage, wanda ya yi suna a matsayin ɗaya daga cikin masu horarwa masu hazaka a Turai.

    BBC Sport ce ta fara bayyana sha’awar Crystal Palace ga mai shekara 47 a ranar 8 ga Mayu, amma a lokacin shugabancin Palace ya fi mayar da hankali kan ƙoƙarin ɗauko Iraola daga Bournemouth.

    Rahotanni sun ce kocin Lens ɗin da yiwuwar komawa Palace, kuma ana sa ran zai gana da jami’an ƙungiyar a cikin kwanaki masu zuwa.

  2. , Daga Jaridu

    Dan wasan Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31, yana sha'awar komawa Barcelona ya yin da kwantiraginsa a Manchester City na gab da karewa.(Mundo Deportivo - in Spanish), external

    Brighton za ta fuskanci hamayya daga Hoffenheim da Eintracht Frankfurt wajan sayen dan wasan Wolfsburg Patrick Wimmer mai shekaru 25 .(Florian Plettenberg), external

    Crystal Palace ta sake tattaunawa da kocin Lens Pierre Sage da ake ganin yana da kwarewa sosai .(Mail), external

    Kocin Como Cesc Fabregas na jin dadin aikinsa a kungiyar Italiya duk da cewa an alakanta da shi da wasu ayuikam horas dayan wasa a wasu wurare ciki harda Real Madrid (Sport - in Spanish)

  3. Slot ya ce ya bar Liverpool a gurbin da ta dace, Liverpool

    Arne Slot ya ce ya bar Liverpool “daidai inda ya kamata ta kasance: cikin manyan ƙungiyoyin Turai” bayan da aka kore shi daga aikin koci ranar Asabar.

    Ɗan kasar Netherlands mai shekara 47 ya lashe kofin Premier League a kakar sa ta farko, amma shugabancin ƙungiyar ya yanke shawarar korarsa, bayan da Liverpool ta kare a matsayi na biyar a gasar bana, inda ta kasance da tazarar maki 25 tsakaninta da Arsenal wadda ta lashe kofin a karon farko bayan shekara 22.

    Liverpool za ta fara tattaunawa a hukumance a wannan mako da tsohon kocin Bournemouth, Andoni Iraola, kan yiwuwar ya maye gurbin Slot a matsayin sabon koci.

    A cikin wata buɗaɗɗiyar wasika mai cike da tausayi da aka buga a Liverpool Echo, Slot ya ce magoya baya sun tarbe shi cikin murna tun farko kuma sun taimaka masa wajen gudanar da aikinsa. Ya ce “Wannan abu ne da ba zan manta da shi ba,” in ji shi.

    Ya kara da cewa: “Na bar ƙungiyar da cikakken tabbaci game da abin da ke gaba.”

    “’Ƴan wasan da yawa sun yi hidima sosai, sun kiyaye darajojinsa kuma suka samar da lokuta masu ban mamaki, sun gina tushe mai ƙarfi da zai dawwama.”

    Duk da cewa Liverpool ta sha kashi sau 20 a dukkan fafatawa a bana, Slot ya tabbatar da cewa Liverpool ta samu gurbin shiga Champions League na kakar gaba.

    “Samun gurbin Champions League wani muhimmin nauyi ne kuma ya tabbatar Liverpool za ta ci gaba da fafatawa a matakin koli a kakar gaba da ma bayan haka,” in ji shi.

    “Lokacin da na fara tsayawa a matakin kociyan Liverpool, na san abin da wannan ƙungiyar ke bukata. Na kuma san cewa ba mu daina kokari ba.”

    Slot ya maye gurbin Jürgen Klopp a Liverpool a shekarar 2024 bayan kocin Jamus ɗin ya sauka daga mukaminsa bayan shekaru tara.

    Ya fara aikinsa cikin nasara sosai, inda ya jagoranci Liverpool zuwa kofin Premier League na 20, har ma da tazarar maki huɗu kafin ƙarshen kakar wasa a gaban magoya baya a Anfield.

  4. Milner ya yi ritaya bayan shekara 24 yana taka leda, Premier League

    Tsohon ɗan wasan tawagar Ingila, James Milner, ya sanar da yin ritaya daga buga ƙwallon ƙafa bayan ya shafe shekara 24 yana taka leda a gasar Premier League.

    Milner mai shekara 40, wanda ke iya taka leda a wurare daban-daban a fili, ya zauna ba tare da kwantiragi ba bayan shekara uku da suka gabata a Brighton & Hove Albion.

    A tsawon rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa, Milner ya buga ƙungiyoyi shida wasa a gasar Premier League, kuma a watan Fabrairu ya kafa tarihin ɗan wasan da ya fi kowa yawan buga wasanni a gasar.

    Ya fara sana’arsa ne ta taka leda a Leeds United, sannan ya lashe kofin Premier League sau uku – guda biyu tare da Manchester City da kuma sau ɗaya tare da Liverpool. Haka kuma ya taimaka wa Liverpool ta ɗauki gasar UEFA Champions League a shekarar 2019.

    Milner ya fara buga wa Ingila wasa a shekarar 2009 lokacin yana tare da Aston Villa, ya yi wa tawagar kasar wasa 61.

    Milner ya fara bugawa Leeds United wasa yana ɗan shekara 16 a watan Nuwamban 2002. A lokacin, shi ne ɗan wasa na biyu mafi ƙarancin shekaru da ya taba buga Premier League.

    A wata mai zuwa kuma, ya zama mafi ƙarancin shekaru da ya ci ƙwallo a tarihin Premier League. A yanzu yana matsayi na uku bayan Max Dowman da James Vaughan.

    Rauni ya sa Milner ya rasa mafi yawan wasannin a kakar 2024-25, amma ya dawo ya buga karawa 22 a dukkan fafatawa a kakar 2025-26. Wasansa na ƙarshe a Premier League ya kasance na 658, wanda ya buga a ranar ƙarshe a kakar wasa da Brighton.

    Bayan shekara biyu a babbar ƙungiyar Leeds, an sayar da shi zuwa Newcastle United bayan Leeds ta faɗa gasar Championship a shekarar 2004.

    Daga nan ya koma Aston Villa a 2008, sannan Manchester City a 2010, inda ya taimaka musu wajen lashe kofunan Premier League na farko a shekarun 2012 da 2014.

    A shekarar 2015 ya koma Liverpool, inda ya shafe shekaru takwas a filin Anfield, ya zura ƙwallaye 26 a wasa 332.

    A shekarar 2020, ya taimaka wa Liverpool lashe kofin Premier League na farko tun 1990. Haka kuma ya lashe kofin FA Cup da League Cup tare da Liverpool da Manchester City.

  5. Barkanmu da shiga fagen labarin wasanni

    Jama'a barkanmu da kasancewa a cikin shirin labarin wasanni da za mu ke sanar da ku wainar da ake toyawa daga wannan ranar zuwa Asabar 18 ga watan Afirilu.

    Sunana Mohammed Abdu za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko kuma ku bibiyi labaran da muke wallafawa a BBC Hausa WhatsApp.