Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona na zawarcin Martinez, Manchester United na neman Robinson
Mai tsaron baya na Manchester United kuma ɗan ƙasar Argentina, Lisandro Martinez, mai shekara 28, na iya zama ɗan wasan da Barcelona za ta yi ƙoƙarin ɗauka a watan Janairu, yayin da ƙungiyar ke neman ƙarfafa bangarenta na masu tsaron baya. (Mundo Deportivo)
A ɗaya ɓangaren kuma, Manchester United na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Fulham, Antonee Robinson, mai shekara 29, da kuma ɗan wasan baya ɗan Najeriya, Calvin Bassey, mai shekara 26, a watan Janairu. (the i)
Manchester United ta kuma nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan gaba na Monaco kuma ɗan ƙasar Amurka, Folarin Balogun, mai shekara 25, da kuma ɗan wasan gaba na Freiburg ɗan ƙasar Croatia, Igor Matanovic, mai shekara 23. (the i)
Liverpool ta tura wakilanta domin su sanya ido kan ɗan wasan gaba na Monza, Gustavo Varela. Ɗan wasan na ƙasar Portugal mai shekara 21 shi ne kan gaba wajen zura ƙwallaye a gasar Serie A, kuma ƙungiyar Juventus ma tana sha'awar ɗaukar sa. (Corriere dello Sport)
A yanzu haka Bournemouth na sa ran samun tayin da ya kai kusa da adadin £100m da ta sanya a matsayin farashin ɗan wasan tsakiya na Ingila, Alex Scott, mai shekara 23; inda Chelsea ke kan gaba wajen fafutukar ɗaukar sa. (Teamtalk)
Roma na sha'awar ɗaukar ɗan wasan gefe na Chelsea, ɗan ƙasar Ingila mai shekara 22, Jamie Bynoe-Gittens, a watan Janairu. (Corriere dello Sport)
AC Milan ta sanya ɗan wasan tsakiya na Napoli da Scotland, Scott McTominay mai shekara 29, a matsayin babban ɗan wasan da take son ɗauka, yayin da Real Madrid da Manchester United ma ke nuna sha'awa kan ɗan wasan. (Quotidiano Nazionale)
AC Milan da Roma na fatan samun damar shawo kan Real Madrid ta sayar da ɗan wasan gaba na Brazil, Endrick mai shekara 20, a watan Janairu, bayan da aka sanya masa farashin da ya kai kusan Yuro miliyan 70 (fam miliyan 58). (Corriere dello Sport)
Arsenal na ci gaba da sa ido kan ɗan wasan gaba na Brentford da Jamus, Kevin Schade mai shekara 24, yayin da suke nazarin yiwuwar ɗaukar sa a watan Janairu. (Teamtalk)
Mauricio Pochettino na son Manchester United ta cire daraktan ƙwallon ƙafa Jason Wilcox, tare da maye gurbinsa da Paul Mitchell—mutumin da Pochettino, wanda ɗan asalin Argentina ne, ya taɓa yin aiki tare da shi a ƙungiyoyin Southampton da Tottenham. (Football Insider)