Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 19/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 19/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Isra'ila ta ce ta kawo ƙarshen farmakin da ta ƙaddamar a Gaza

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kawo ƙarshen farmakin da suka ƙaddamar a Gaza tun ranar Laraba.

    A cikin wata sanarwa, hukumar ma'aikatar tsaron Isra'ila da ke kula da harkokin fararen hula a yankunan Falasɗinu ta ce an sake bai wa Falasɗinawa damar zirga-zirga a yankunan da abin ya shafa da ke kusa da sansanonin ƴan gudun hijira na Bureji da Nuseirat, bayan layin rawaya.

    Layin rawayar dai shi ne iyakar da sojojin Isra'ila suka ayyana domin raba yankunan da suke iko da su da sauran sassan Gaza.

    Tun da farko dai sojojin Isra'ila sun umarci mazauna yankin su fice daga wuraren kafin fara aikin soja.

  2. 'Putin ya ji daɗin ganawa da Trump'

    Mai bai wa shugaban Rasha shawara kan harkokin Waje, Yuri Ushakov, ya ce Shugaba Vladimir Putin na cikin farin ciki sosai bayan ganawarsa da Shugaba Trump na Amurka.

    Da yake zantawa da gidan talabijin na gwamnatin Rasha, Vesti, Ushakov ya ce tattaunawar da shugabannin biyu suka yi ta gudana cikin nasara.

    Kafofin yaɗa labaran Rasha sun yaɗa wani bidiyo da ke nuna Trump na shiga ɗakin taro yana tunkarar Putin tare da cewa: Wannan abokina ne!"

    A cewar Ushakov, yaƙin Ukraine ne ya kasance babban abin da aka fi mayar da hankali a kai a ganawar, wadda ta ɗauki tsakanin minti 35 zuwa 40.

    Ya ce shugabannin sun kuma tattauna kan alaƙar ƙasashen Amurka da Rasha.

    Fadar Kremlin ta ce babu wani daga cikin shugabannin da ya yi wata muhimiyar sanarwa bayan ganawar, yayin da ɓangarorin biyu ke shirin wata ganawa da Shugaban China Xi Jinping daga baya a yau.

  3. Kwale-kwale ya kife a Senegal ɗauke da sama da mutum 100

    Ana ci gaba da gudanar da aikin ceto da neman waɗanda suka ɓace bayan wani kwale-kwale ɗauke da baƙin haure ya kife a gaɓar tekun Senegal.

    Wani da ya tsira daga haɗarin ya shaida wa ƴan sanda cewa akwai kusan mutum 100 a cikin kwale-kwalen.

    Jami'an yankin sun ce ƙaramin jirgin ya bugi wasu duwatsu kafin ya nutse a ranar Laraba.

    Lamarin ya faru ne ƙasa da mako guda bayan da baƙin haure 43 suka mutu sakamakon hatsarin wani jirgin ruwa a gaɓar garin Thieppe da ke arewa maso yammacin ƙasar.

    A shekarun baya-bayan nan dai dubban ƴan yammacin Afirka sun rasa rayukansu yayin da suke ƙoƙarin tsallaka Tekun Atlantika zuwa Tsibiran Canary na ƙasar Spain, cikin neman ingantacciyar rayuwa.

  4. Musulunci zai fi kowane addini yawan mabiya nan da 2035 - Bincike

    Wata cibiyar bincike ta Amurka ta yi hasashen cewa addinin Musulunci zai zama addini mafi yawan mabiya a duniya nan da shekarar 2035, inda zai zarce Kiristanci.

    Binciken da cibiyar Pew Research Center ta gudanar ya nuna cewa yawan mabiya addinin Kirista na ci gaba da ƙaruwa, amma yawan Musulmai na ƙaruwa cikin sauri saboda yawan haihuwa da ya fi yawa a tsakanin Musulmai.

    Rahoton ya ce ana ƙiyasin cewa mace Musulma na haihuwar yara fiye da uku a matsakaici, idan aka kwatanta da kusan yara biyu da rabi ga mace Kirista.

    Tun shekaru shida da suka gabata, Musulmai suka kasance masu rinjaye a ƙasashe 53 na duniya.

    Ana sa ran mafi yawan ƙaruwar yawan Musulman za ta faru ne a waɗannan ƙasashe.

    Binciken ya kuma hasashen cewar adadin Musulmai zai ƙaru da ƙarin mutum biliyan 1.2 nan da shekarar 2070.

  5. An ci gaba da musayar wuta tsakanin Saudiyya da Houthi

    An sake samun musayar wuta a tsakanin Saudiyya da kuma 'yan tawayen Houthi a Yemen.

    Mahukuntan Saudiyya sun ce sun daƙile wani harin makami mai linzami da aka kai kan birnin Riyadh, sai dai rahotanni sun nuna tarkacen makamin da ya faɗo ya haddasa ɓarna a wasu wurare.

    A nasu ɓangaren, ƙungiyar Houthi ta ce jiragen yaƙin Saudiyya sun kai hare-haren sama kan babban birnin Yemen, Sanaa.

    Tun da farko Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya gana da babban kwamandan rundunar sojin Amurka a yankin, Admiral Brad Cooper, inda suka tattauna kan halin da ake ciki.

    Faɗan da ake tsakanin ƙawancen ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta da kuma mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran ya ƙara tsananta a watan jiya.

  6. Trump ya fara ganawa da Putin a China

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya fara tattaunawa da Shugaban Rasha Vladimir Putin a ƙasar China, gabanin wata ganawa ta musamman da za su yi tare da Shugaban China Xi Jinping.

    Ana sa ran shugabannin ƙasashen uku za su haɗu a wani taron ƙoli na tarihi da ba a taɓa yin irinsa ba.

    A farkon ganawarsa da Mista Putin, Shugaba Trump ya ce suna da kyakkyawar alaƙa, yana mai cewa taron na iya haifar da "abubuwa masu kyau da dama" ga ɓangarorin da abin ya shafa.

    Shugabannin uku suna da bambancin ra'ayi a kan abin da suke son a cimma a yayin wannan taro, inda shugaba Trump ke son a samu ci gaba amma ta fannin abin da zai daɗaɗawa Amurkawa.

    Ƙasar China ta ce shugabannin za su yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan da suka shafi zaman lafiya a duniya.

  7. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta da zaurenmu na Whatsapp domin samun arin labarai da bidiyoyi.