Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United ta samu gurbin Champions Lig 2026/27
Manchester United ta samu gurbin buga gasar Zakarun Nahiyar Turai bayan doke Liverpool da ta yi a wasan mako na 35 na Premier.
United ta samu tikitin Champions ɗin ne, bayan nasarar da ta samu da ci 3-2 a Old Trafford kan Liverpool.
Da wannan nasarar Manchester United ta haɗa maki 64 yayin da wasanni uku ne kacal suka yi ragowa a kammala gasar ta bana.
Tun a minti na shida da fara wasan ne Cunha ya jefa musu kwallo ta farko, wadda da ita ce United ta shiga gaba a wasan, bayan kwanar da aka kwaso wadda ya sa dama ya buga ta dawo ya kuma ƙarawa da hagu.
Daga baya a mintina na 14 Sesko ya ci ta biyu wadda ta haifar da ruɗani har sai da aka duba na'urar da take taimakawa alƙalin wasa kafin daga bisani alƙalin wasan ya tabbatar da kwallon.
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci sai Liverpool ta zare kwallo ta farko ta hannun ɗan wasanta na tsakiya Szoboszlai a minti na 47, bayan kuskuren da Amad Diallo ya yi daga tsakiyar filin wasan.
Ka zalika mai tsaron ragar Manchester Lammens, ya sake kuskure na biyu a wasan wanda yakan ya kai ga farke kwallo ta biyu da United ɗin ta ci, kuma Gakpo ne ya ci kwallon a minti na 56.
Daga nan wasa ya koma dai-dai tsakanin ɓangarorin biyu, amma daga bisani United ta sake shiga gaba.
Kobbie Mainoo ne ya ci kwallo ta uku da ta baiwa United nasara a wasan a minti na 77 da fara wasan.
Wasa uku ne ya ragewa United ta kammala gasar ta bana, za ta je Sunderland, sannan ta karɓi baƙuncin Nottengham ta ƙarƙare da Brighton a filin wasa na American Express.
Tun bayan karbar ragamar United Michael Carrick ya yi nasara a wasanni 10 cikin 14 da ya jagoranci ƙungiyar, sannan ya yi rashin nasara biyu, canjaras biyu.
Da wannan Carrick ya samu nasara a kan manyan ƙungoyin biyar ɗin farko na teburin gasar, da suka haɗa da Manchester City da Arsenal da Aston Villa.
Ya kuma yi nasara kan Chelsea da Liverpool da kuma Tottenham, wadanda dukansu suna cikin manyan ƙungiyoyin Premier waɗanda wasanni da su ke zama mai wuya a lokuta da dama.