Dalilai uku da ke bai wa Argentina damar farke ƙwallaye har ta ƙara

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Mohammed Abdu
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 8
A gasar Kofin Duniya ta 2026 da ta rage saura wasa biyu a kammala wasannin bana da ake gudanarwa a Amurka da Kanada da kuma Mexico, akwai abubuwa da dama da suke ja hankalin masu bibiyar fafatawar.
Wasu ƙasashe sun yi fice wajen kai hare-hare tun daga farkon take leda har a tashi daga wasan, yayin da wasu suke da ƙwarewa wajen tsaron baya.
To sai dai Argentina mai rike da kofin duniya na uku jimilla, tana da salon zura ƙwallo da karfin hali da sa matsi da sauran dabarun da ba kasafai tawaga kan haɗa ba.
Duk da cewa Argentina ce riƙe da kofin hakan bai hana ta fuskanci matsin lamba a wasanni da dama ba. Sai dai abin da ya bambanta ta da sauran ƙasashen da ke buga gasar kofin duniya a bana, shi ne yadda take iya sauya yanayin wasa idan ta shiga matsala.
Maimakon ta tashi hankalinta don an zura mata ƙwallo a raga, sai ta ƙara sa nutsuwa, ta tsara kai hare-hare, sannan ta dawo ta karɓe ragamar wasan.
Wannan salon da Argentina take bugawa ya bambanta da wanda ta yi a Qatar a 2022, duk da cewar ta fuskanci ƙalubale a kowacce, amma a bana tawagar tana da abubuwan ban mamaki da tun farko take cikin waɗanda aka yi hasashen lashe kofin, wadda ke fatan kaiwa zagayen ƙarshe karo uku a jere.
Argentina na nuna halin ita ce mai rike da kofin mai kuma hazaka

Asalin hoton, Getty Images
A tarihin manyan gasar tamaula ta duniya, ana cewa zakara ba wai wanda yake cin wasa cikin sauƙi ba ne kawai. Shi ne wanda yake da salo da dabarun da zai kai zagayen gaba a duk lokacin da ya fuskanci kalubale, abin da Argentina ke yi a gasar cin kofin duniya ta 2026.
Idan za ka lura da yadda take taka leda, duk lokacin da aka fara zura mata ƙwallo a raga ba ta canza tsarin wasanta cikin gaggawa. Ƴan wasan suna yin kokarin mamaye fafatawar, sannan suna lura da lokacin da za su yi wa abokan hamayya illa, suna kuma kula da inda abokiyar hamayya take da rauni.
Hakan kuma yana tasiri daga mai horar da tawagar da yadda yake canje-canjen ƴan wasa da suke yin abin da aka umarce su a fili da hakan ke sawa suke samun nasarori a fafatawar bana.
Wasannin da Argentina ta fuskanci ɗan karen ƙalubale, amma ta lashe karawar
- Wasan Cape Verde – Farkon bajintar da Argentina ta nuna, bayan fuskantar kalubale
A zagaye na biyu na tawaga 32, Argentina ta kara da Cape Verde, karamar kasar da ta ba mutane mamaki tun a matakin rukuni, wadda karon farko kenan da ta buga babbar gasar tamaula ta duniya a tarihi
Cape Verde ta nuna cewa ba ta je yawon buɗe ido bane. Ta yi amfani da kuskuren da aka samu daga masu tsaron bayan Argentina ta ci ƙwallaye.
Tun farko Lionel Messi ne ya fara cin ƙwallo a minti na 29 da fara wasan, sai a zagaye na biyu ne Cape Verde ta farke ta hannun Deroy Duarte.
Daga nan Argentina ta kara na biyu ta hannun Lisandro Martinez a minti na 92, amma kuma Cape Verde ta farke minti 11 tsakani daga karshe Cape Verde ta ci gida ta hannun Diney Borges a minti na 111, dalilin da ya kai Argentina zagaye na uku na ƴan 16.
Idan har ka kalli wasan ka kuma yi nazari mai zurfi, bayan da aka koma zagaye na biyu ne fafatawar ta canja gabaki ɗayanta.
Argentina ta ƙara sauri da guje-guje, ta fara kai hare-hare daga gefe hagu zuwa gefen dama, yayin da Lionel Messi da sauran manyan ƴan wasa suka riƙa jan ragamar wasan da nuna gogewa ba tare da tayar da hankali ba cikin natsuwa.
A ƙarshe Argentina ta yi nasara da ci 3-2, abin da ya tabbatar da cewa tawagar ba ta yanke ƙauna ba idan aka ci ta.
Wannan wasa ya zama darasi ga sauran ƙasashe cewa koda ka ci Argentina, ba yana nufin an gama aikin ba, shi ya sa Bahaushe ya ce ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare..
- Egypt ta kusan karya burin Argentina
Idan wasan Cape Verde ya kasance mai wahala ga Argentina, to fafatawar da ta yi da Masar a zagayen ƴan 16 ta fuskanci babban kalubale.
Masar ta taka leda cikin tsari da natsuwa da gogewa, inda take kai farmaki da yawa da kuma tsare bayanta kuma cikin gaggawa.
A wasu lokuta wasan ya nuna kamar za a yi waje da Argentina daga gasar, saboda yadda Masar ta dage wajen hana ta samun damar zura ƙwallo.
Sai dai abin da ya bambanta wasan shi ne hakurin da Argentina ta saka a karawar.
Ta ci gaba da buga ƙwallo a ƙasa, tana jan hankalin ƴan bayan Masar har sai da ta sami gurbin da ta ratsa ta kuma ci ƙwallaye.
Daga ƙarshe Argentina ta sake yin nasara da ci 3-2, inda ta tabbatar da cewa dawowa daga baya ba haɗari ba ne, illa wata alama ce ta ƙarfin tunani da kuma ƙwarewar dabaru.
Wasan Ingila – Gwajin da ya tabbatar da ƙarfin Argentina
Wasan kusa da na ƙarshe tsakanin Ingila da Argentina shi ne mafi girman gwajin da kasar ta fuskanta a Kofin Duniya a 2026.
Ingila ta fara wasan cikin kuzari da saka kaimi, ta matsa wa Argentina lamba tun daga farkon mintunan da aka take leda. Wannan salon ya ba ta damar samun zura ƙwallon farko, abin da ya sa magoya bayan Ingila suka fara ganin hanyar zuwa wasan ƙarshe ta buɗe.
Sai dai kamar yadda aka gani a wasannin baya, Argentina ba ta nuna alamar tashin hankali ba. Maimakon haka, ta ci gaba da bin tsarin wasanta na mallakar ƙwallo da kai hare-hare cikin natsuwa da amfani da gefen hagu da dama da kuma kai ƙwallo zuwa cikin gidan Ingila.
A zagayen wasa na biyu, bayan sun sha ruwa sun koma fili, sai kociyan Argentina, Lionel Scaloni ya yi wasu sauye-sauye masu muhimmanci. Sabbin ƴan wasan da suka shiga sun ƙara sa hazaka a tawagar da saurin kai hare-hare. Hakan ya sa Ingila ta fara komawa baya, domin kare ƙwallon da tta fara ciki, amma duk da haka bai zame mata mafita ba.
Argentina ta yi amfani da wannan damar wajen farke ƙwallon da aka zura mata. Daga nan kuma ta ci gaba da matsa wa Ingila lamba har zuwa mintunan ƙarshe. A ƙarin lokaci ne, Lautaro Martínez ya zura ƙwallon da ya kai Argentina karawa karshe, inda kasar ta yi nasara da ci 2-1.
Kenan Argentina za ta fuskanci Sifaniya a wasan karshe ranar Lahadi, kafin nan za a buga neman mataki na uku tsakanin Faransa da Ingila a ranar Asabar.
Mene ne sirrin wannan nasarorin Argentina?

Asalin hoton, Getty Images
Idan ka kalli yadda Argentina ke taka leda a gasar nan ta kofin duniya ta bana, akwai manyan abubuwa uku da suka taimaka mata.
- Na farko shi ne kwarin gwiwar ƴan wasa. Ba sa firgita idan aka ci su ƙwallo.
- Na biyu shi ne dabarun mai horarwa wato, Lionel Scaloni, wanda yake iya yin sauye-sauyen ƴan wasa a lokacin da ya dace.
- Na uku kuma shi ne gogewar manyan ƴan wasan tawagar irin su Lionel Messi, waɗanda suka saba buga manyan wasanni kuma suka san yadda ake magance matsin lamba.
Dalilai uku da suka Argentina ta kasance cikin manyan tawagogi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wadannan abubuwa uku ne suka sa Argentina ta kasance cikin tawagogin da suka fi wahalar doke wa a gasar.
- Rawar Messi da gogaggun 'yan wasa
Ko da yake Lionel Messi ba ya zura ƙwallo a kowane wasa, amma tasirinsa yana bayyana ta hanyoyi daban-daban. Yana jan hankalin masu tsaron baya, yana bayar da ƙwallaye a zura a raga, yana rarraba ƙwallaye masu inganci da haɗari, kuma yana ƙarfafa gwiwar abokan wasansa su ci gaba da sa ƙwazo har zuwa sai an tashi
Haka kuma, ƴan wasa irin su Lautaro Martínez sun tabbatar da muhimmancin kasancewa cikin shiri a kowane lokaci. Sau da dama yana fitowa daga benci ya sauya alkiblar wasan gabaki ɗayansa, abin da ya nuna cewa ƙarfin Argentina ba ya ta'allaka ne ga ɗan wasa guda ɗaya kawai, kowa zai iya yi maka illa a lokacin fafatawar
- Dabarun Scaloni sun bambanta
Ɗaya daga cikin manyan dalilan nasarar Argentina shi ne yadda koci, Lionel Scaloni ke karantar wasa. Yana lura da inda abokan hamayya suka fara gajiya suke da rauni da gazawa, sannan ya yi sauye-sauyen da suka dace suke kuma yin tasiri.
Maimakon ya yi gaggawar sauya tsarin wasan, bayan an ci Argentina, yakan ci gaba da amfani da dabararsa ta farko, har sai lokacin da ya ga ya dace ya canza. Wannan haƙurin ya taimaka wa Argentina wajen sauya sakamakon wasanni da dama.
- Darasin da sauran ƙasashe za su koya
Abin da Argentina ke nunawa a wannan gasar ta bana, ta tabbatar da cewa wasan ƙwallon ƙafa bai ƙare ba , har sai alkalin wasa ya busa usur ɗin tashi daga wasa, domin komai na iya faruwa, komai zai iya canjawa a kowanne lokaci.
Ƙasashe da dama sun rasa damar tsallakewa zagayen gaba a gasar nan, saboda komawa tsaron baya, wai don sun ci ƙwallo kuma tun da saura lokaci tashi daga wasan da yawa, yayin da Argentina ke ci gaba da neman nasara har zuwa minti na ƙarshe.
Wannan ya nuna muhimmancin:
- Rashin yanke ƙauna idan aka ci ƙwallo.
- Ci gaba da bin tsarin wasa ba tare da ruɗewa ba.
- Yin amfani da ƙwararrun masu maye wajen sauya yanayin wasa.
- Samun shugabanci daga gogaggun 'yan wasa a lokacin matsin lamba.
Idan aka duba wasannin da ta buga da Cape Verde da Masar da kuma Ingila, Argentina ta samu kanta cikin matsin lamba kafin daga bisani ta dawo ta yi nasara.
Wannan ba abin mamaki ba ne, domin manyan zakaru a tarihin ƙwallon ƙafa sun fuskanci ƙalubale mai ɗan karen wahala daga baya su lashe wasan. Argentina ta 2026 ta ƙara tabbatar da wannan lamarin.

Asalin hoton, BBC Sport
Yayin da duniya ke jiran wasan ƙarshe tsakanin Sifaniya da Argentina a Kofin Duniya a 2026, tuni Argentina ta riga ta aika saƙo ga sauran ƙasashe cewa ita ba ta dogara da fitattun ƴan wasan da take da su da hazakar da take sawa, tana da juriya da dabaru da kuma imani cewa za ta iya sauya sakamakon wasa a kowane lokaci.
Nasarorin da ta samu kan Cape Verde da Masar da kuma Ingila sun nuna cewa hakuri da juriya da kara ƙwazo kan kai ga yin nasara. Haɗin kan ƴan wasa da dabarun mai horarwa, Lionel Scaloni da gogewar Lionel Messi da tasirin ƴan wasan da suke shiga fili daga baya a matakin canji, sun gina kasar da ba ta yanke ƙauna har sai an busa usur na tashi daga wasan.
Ko Argentina za ta kare kambunta ko a'a, abin da ta nuna a Kofin Duniya a 2026 zai kasance ɗaya daga cikin manyan darussan da za a riƙa tunawa a tarihin gasar:
Zakara na gaskiya shi ne wanda ya san yadda zai fuskanci kalubale da sa juriya da hakuri da nuna gogewa ta karya lagwan abokin hamayya, domin lashe wasa da zuwa matakin gaba.










