Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu 5 da ya kamata ku sani kan fara yaƙin neman zaɓen Tinubu a Kaduna
- Marubuci, Imam Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Yayin da Najeriya ke shirin gudanar da babban zaben shekarar 2027, jam'iyyar APC ta shirya fara yakin neman zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar 24 ga watan Oktoba, 2026, a Jihar Kaduna.
Taron, wanda ake sa ran zai samu halartar manyan jiga-jigan jam'iyyar, da gwamnoni, da shugabannin siyasa da magoya bayan APC daga sassa daban-daban na kasar, na daga cikin matakan da jam'iyyar ke dauka domin fara shirye-shiryen neman wa'adin mulki na biyu ga Tinubu.
Ana kuma sa ran taron zai bai wa APC damar bayyana alkiblar yakin neman zabenta, da kuma yadda take shirin gabatar da ayyukan gwamnatin Tinubu a matsayin wani bangare na neman goyon bayan masu kada kuri'a.
To, me ya sa aka zaɓi jihar Kaduna domin ƙaddamar da wannan kamfen? Waɗanne muhimman batutuwa ne za su iya mamaye taron, kuma me hakan ke nufi ga shirin APC na babban zaɓen 2027?
Ga muhimman abubuwan da ya kamata ku sani.
1. Yaushe za a fara kamfen din?
An tsara fara kamfen din ne a ranar Asabar ɗin nan, 24 ga Oktoba, 2026.
Yakin neman zaben zai kasance farkon jerin tarukan da APC ke shirin gudanarwa a sassa daban-daban na Najeriya domin neman goyon bayan masu kada kuri'a gabanin zaben 2027.
A cewar shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaba Tinubu, tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari, kwamitin yakin neman zaben ya kuma tsara ziyarar da shugaban kasar zai kai wasu jihohi, inda aka sanya Fatakwal ta Jihar Ribas da Maiduguri ta Jihar Borno cikin wuraren da za a ziyarta bayan taron Kaduna.
An kuma bayyana cewa za a fitar da cikakken jadawalin ayyukan kwamitin bayan kaddamar da shi.
2. A ina za a gudanar da taron?
Za a gudanar da babban taron ne a filin wasa na Kaduna Township Stadium, da ke cikin birnin Kaduna.
Mataimakiyar gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Balarabe, wadda ke jagorantar kwamitin shirya taron, ta bayyana cewa an kammala muhimman shirye-shiryen karbar shugaban kasa da sauran manyan baki.
Ta bayyana hakan ne bayan ta jagoranci tawagar kwamitin wajen duba filin wasan, inda ta ce an tanadi wuraren da za a tarbi jama'a da sauran abubuwan da ake bukata domin gudanar da taron.
3. Me ya sa zai fara da Kaduna?
Kaduna na daga cikin muhimman cibiyoyin siyasa a Arewacin Najeriya. Birnin ya taba zama hedikwatar siyasar tsohuwar Arewacin Najeriya, abin da ya sa yake da matsayi na musamman a tarihin siyasar yankin.
Kwamitin yaƙin zaɓen Tinubu ya bayyana cewa zaɓar Kaduna ya nuna muhimmancin da Shugaba Tinubu ke bai wa Arewa da burin hada kan al'ummomin yankin.
A cewarsa, Kaduna ta dace da taron saboda muhimmancinta ga al'ummar Arewa da kuma kasancewarta jiha mai al'ummomi daban-daban da ƙabilu daban-daban.
Ƙarin wani abu da ake ganin zai iya zama dalili shine ƙokarin APC na kara karfin siyasarta a Arewa maso Yamma, yankin da ke da matukar muhimmanci wajen neman kuri'un shugaban kasa.
APC ta bayyana cewa tana son ganin Tinubu ya samu kuri'u masu yawa a Kaduna da sauran jihohin Arewa. Jam'iyyar reshen jihar ta bayyana burin samun kuri'u miliyan biyu ga Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027.
4. Wane shiri aka yi domin taron?
Gwamnatin Jihar Kaduna da kwamitin shirya taron sun bayyana cewa an dauki matakan tsaro da kuma shirye-shiryen gudanar da taron.
Kwamishinan watsa labaran jihar Maiyaƙi, ya shaida wa BBC cewa jami'an tsaro na matakin jiha da na tarayya sun shiga cikin shirin tabbatar da tsaron shugaban kasa, da shugabannin jam'iyya da sauran mahalarta.
An kuma bayyana cewa za a rika tantance mutanen da za su shiga filin wasan domin tabbatar da tsaro.
Wasu al'ummar jihar da BBC ta yi magana da su, sun bayyana cewa sun ga ana ta ƙara tsaurara tsaro a wasu muhimman hanyoyi da wuraren taruwar jama'a a birnin Kaduna, yayin da ake kammala shirye-shiryen taron da ake sa ran zai samu halartar dimbin magoya bayan APC.
5. Menene muhimmancin Kaduna ga Tinubu?
Ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Kaduna na da muhimmanci ba kawai a matsayin wurin gudanar da taron siyasa ba, har ma a matsayin wata dama ta nuna ƙarfin jam'iyyarsa, haɗin kan shugabanninta da kuma goyon bayan da take da shi a yankin.
Kaduna jiha ce mai bambancin ƙabilu, addinai da ra'ayoyin siyasa. Wannan ya sa samun goyon bayan al'umma a jihar ya zama babban abun fata ga shugaba Tinubu, domin hakan zai sa ya gamsar da ƴan Najeriya cewa ya haɗa kan al'ummar da ke da banbancin ra'ayi.
Wani ƙarin dalili da ya sa Kaduna ke da muhimmanci ga shugaba Tinubu shi ne tasirinta a siyasar Arewa da kuma yawan masu zaɓe a yankin. Bisa bayanan hukumar zaɓe ta Najeriya (INEC), yankin Arewa maso Yamma ne ke da mafi yawan masu rajistar zaɓe a ƙasar, kuma Kaduna ce ta Uku a yawan masu zaɓe a Najeriya.
Sai dai, sakamakon zaɓen 2023 ya nuna cewa APC na da jan aiki a Kaduna, domin Atiku Abubakar na PDP a wancan lokaci ne ya lashe jihar da ƙuri'u 554,360, yayin da Tinubu ya samu 399,293. Wannan ya nuna cewa, duk da kasancewar APC a kan mulkin tarayya a wancan lokaci, ba ta samu rinjaye a jihar ba a wancan zaɓen.
Saboda haka, gudanar da babban taron kamfen a Kaduna na iya zama wata dama ga APC ta nuna cewa tana son ƙarfafa tasirinta a yankin.