Zaɓen 2027: Jihohi 7 da Atiku Abubakar zai fuskanci ƙalubale

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A daidai lokacin babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027 ke ƙara tunkarowa, tuni an fara lissafe-lissafe da lalubo hanyoyin da jam'iyyun ƙasar za su bi domin samun ƙuri'u.

Masu sharhi kan harkokin siyasa na ci gaba da tantance jihohin da za su iya zama mabuɗin nasara ko akasin haka ga manyan ƴan takara.

Duk da cewa akwai ƴan takara da dama da za su fafata a babban zaɓen, ana ganin akwai manyan ƴan takara irin su Bola Tinubu na jam'iyyar APC da Atiku Abubakar na ADC da Peter Obi na NDC.

Sadai dai ana ganin dukkan ƴan takarar akwai jihohi da sassan ƙasar da za su yi tasiri, sannan akwai jihohi da sassan da ake ganin za su fuskanci ƙalubale wajen tara ƙuri'u.

Duk da cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, na da tasiri a sassa daban-daban na ƙasar, wasu jihohi masu yawan masu kaɗa ƙuri'a na iya zama ƙalubale gare shi.

Masanin harkokin siyasa, Kabiru Sufi, ya ce akwai jihohi da dama da ake sa ran Atiku zai fuskanci gagarumar hamayya saboda tasirin gwamnoni, jam'iyyun da ke mulki, ko kuma kasancewar manyan 'yan takara da suka fito daga jihohin.

Kano

Jihar Kano na daga cikin manyan jihohin Najeriya wajen yawan masu rajistar zaɓe da masu kaɗa ƙuri'a. Sai dai Kabiru Sufi ya ce Atiku ba zai fuskanci ƙalubale sosai a jihar ta Kano wajen samun ƙuri'a.

"Kano na da ƙuri'u masu yawa, amma akwai ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC daga jihar. Haka kuma APC ce ke da gwamnati a jihar. Wannan zai sanya Atiku ya yi fafutuka sosai idan yana son samun rinjaye," in ji Kabiru Sufi.

A cewarsa, kasancewar manyan jam'iyyu suna da ƙarfi a Kano na nufin za a yi gwagwarmaya mai zafi kan kowace ƙuri'a.

Kano ce dai jiha ta biyu mafi yawan ƙuri'a a alƙaluman da hukumar INEC ta fitar na waɗanda za su kaɗa ƙuri'a a babban zaɓen mai zuwa.

Kano na da masu rajistar zaɓe guda 6,570,276

Legas

Kabiru Sufi ya bayyana Legas a matsayin wata jiha da za ta iya zama babban ƙalubale ga Atiku.

"Legas ita ce jihar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu. A zaɓen da ya gabata kuma Peter Obi ne ya samu rinjaye a jihar. Yanzu idan Obi ya sake tsayawa takara, sannan APC ta ci gaba da amfani da tasirin Tinubu, Atiku zai fuskanci ƙalubale sosai."

Ya ce siyasar Legas ta zama mai matuƙar jan hankali, inda ake ganin jam'iyyu uku ko fiye za su iya rabon ƙuri'u a tsakaninsu.

Jihar Borno

A yankin Arewa maso Gabas, Kabiru Sufi ya yi nuni da cewa jihar Borno na daga cikin wuraren da APC ke da dogon tarihi na samun rinjaye.

"Borno na da mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, wanda har yanzu yake da tasiri sosai a jihar. Wannan zai sa APC ta ci gaba da kasancewa mai ƙarfi."

Ya ƙara da cewa ko da Atiku ya fito daga yankin Arewa maso Gabas, hakan ba yana nufin zai samu cikakken goyon baya daga Borno ba.

Yobe

Kabiru Sufi ya ce Yobe na daga cikin jihohin da ke da da kusanci da jihar Atiku ta asali, amma tarihin zaɓenta na nuna karkata ga APC.

"Yobe da Adamawa maƙwabta ne, amma idan aka dubi yadda jama'a ke zaɓe a lokuta da dama, APC ce ke da rinjaye. Wannan na iya rage wa Atiku damar samun kuri'un da yake fata."

A cewarsa, tasirin shugabannin APC a jihar na ci gaba da zama muhimmin abin la'akari.

Tasirin APM a Bauchi da Oyo

Duk da cewa ana ganin gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde zai iya rage wa Bola Tinubu ƙuri'a a yankin kudu maso yammacin ƙasar, Kabiru Sufi ya ce shi ma Atiku zai fuskanci ƙalubale.

Jihar Oyo na daga cikin jihohin Kudu maso Yamma da ake sa ran siyasar gwamnoni za ta yi tasiri sosai.

"Akwai Oyo inda Seyi Makinde ke da tasiri sosai. Duk inda gwamna yake da ƙarfi, yawanci yana iya karkatar da akalar ƙuri'u."

Kabiru Sufi ya ce duk wata dabara da Atiku zai yi a jihar dole ne ta yi la'akari da matsayin gwamnan da kuma tasirinsa a siyasar yankin.

Masanin siyasar ya kuma ambaci Bauchi a matsayin wata jiha da za ta iya rage wa Atiku yawan kuri'u da yake tsammani.

"Bauchi ma na daga cikin jihohin da tasirin gwamna zai taka rawa sosai. Duk inda gwamnati mai ci take da ƙarfi, ɗan takara daga wata jam'iyya zai fuskanci ƙalubale."

Ya ce tsarin siyasar jihar da yadda aka gina cibiyoyin siyasa a cikin ta na iya tasiri kan sakamakon zaɓe.

Rivers

Jihar Rivers, wadda ta daɗe tana matsayin jihar PDP ke samun tagomashi, amma duk da haka, ita ma na cikin jihohin da Kabiru Sufi ke ganin Atiku zai iya fuskantar matsala.

"Rivers asali jihar PDP ce, amma tun bayan rikice-rikicen siyasa da suka biyo baya da kuma matsayin Nyesom Wike, ba za a iya cewa Atiku zai samu kuri'u cikin sauƙi ba."

Ya ce sauyin kawancen siyasa da ke gudana a jihar na iya raba kuri'un magoya bayan PDP.

Kabiru Sufi ya ce baya ga jihohin da ya lissafo, akwai wasu wurare a Najeriya inda tasirin gwamnoni zai taka muhimmiyar rawa.