Fitattun sarakunan da aka taɓa dakatarwa a arewacin Najeriya

Wasu manyan sarakunan arewacin Najeriya da aka taba dakatarwa
    • Marubuci, Aminu Kutama
    • Marubuci, Abdulrazzaq Kumo
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

A tarihin arewacin Najeriya, an sha ganin sarakuna da masu riƙe da sarautun gargajiya suna rasa kujerunsu ko fuskantar dakatarwa sakamakon saɓani da gwamnatoci, rikice-rikicen mulki ko kuma zarge-zargen da suka shafi yadda suke gudanar da mulki.

Duk da irin darajar da masarautu ke da ita a idon al'umma, ikon gwamnati na amincewa da sarakuna ko cire su ya sanya alaƙar da ke tsakanin ɓangarorin biyu ta kasance mai sarkakiya lokaci zuwa lokaci.

A cikin shekarun baya-bayan nan kuwa, an dakatar ko cire wasu sarakuna a sassa daban-daban na Arewacin Najeriya saboda zarge-zargen cin zarafi, karya dokoki, tsoma baki a siyasa da sauran batutuwan da suka tayar da kura.

BBC ta tuntuɓi masana tarihi Ibrahim Ado Kurawa da Dr. Tijjani Naniya domin sanin sarakuna a arewacin Najeriya da aka taɓa dakatarwa ko aka tsige.

Sarkin Daura - Muhammadu Bashar

Mohammad Bashar
Bayanan hoto, Mohammad Bashar

An naɗa Alhaji Muhammadu Bashar a matsayin Sarkin Daura na 59 a ranar 18 ga watan Yuni, 1966. Sai dai kuma wani abin jan hankali da mamaki shi ne yadda jim kaɗan bayan hawansa mulki a cikin wannan shekara ta 1966, gwamnatin soja ta dakatar da shi.

An ɗauki wannan mataki ne domin gudanar da bincike na musamman kan harkokin kuɗi da gudanarwa na hukumar tallafa wa manoma ta Arewa ta Northern Region Marketing Boards da kuma kamfanin raya tattalin arzikin Arewa na NNDC, waɗanda ke ƙarƙashin kulawarsa a lokacin da yake minista kafin naɗa shi sarkin Daura.

Sai dai bayan kammala bin ciken da kwamitin da gwamnatin ta kafa ya gudanar, an wanke Alhaji Muhammadu Bashar daga dukkan zarge-zargen da ake masa, sannan gwamnatin soja ta mayar da shi kan karagar sarautar Daura a shekarar 1968, inda ya ci gaba da mulki har zuwa rasuwarsa a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2007.

Sarkin Kano - Ado Bayero

ADO BAYERO
Bayanan hoto, Marigayi Sarkin Kano Ado Abdullahi Bayero

Sarkin Kano na 13 Ado Bayero na daga cikin sarakunan da aka taɓa dakatarwa a arewacin Najeriya. Dakatarwarsa ta biyo wata ziyara da ya kai ƙasar Isra'ila tare da Ooni of Ife a lokacin Oba Okunade Sijuwade, a shekarar 1984.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masanin tarihi Ibrahim Ado Kurawa ya ce tafiyar tasu a lokacin ba ta zo wa gwamnatin Najeriya da daɗi ba kasancewar babu kyakkyawar alaƙa tsakanin ƙasashen biyu saboda wasu dalilai na siyasar duniya.

Bayan dawowarsu Najeriya ne aka dakatar da su na tsawon wata shida tare da hana su yin tafiye-tafiye.

Daga baya dai aka mayar da su bayan wa'adin dakatarwarsu ta cika.

Haka kuma an taɓa samun saɓani tsakanin marigayi Sarkin Kano Ado Bayero da Gwamnan Jihar Kano na farar hula na wannan lokacin, Marigayi Abubakar Rimi.

Sun sami saɓanin ne kan gaisuwar sarauta da ikon gudanar da harkokin masarauta, inda marigayi Abubakar Rimin ya aika wa Sarkin takardar tuhuma wato (query) a matsayin ladabtarwa, sannan ya dakatar da shi daga sarautar sarkin Kano.

Wannan mataki da Marigayi Abubakar Rimin ya ɗauka ya jawo zanga-zanga da tarzoma mai tsanani a Kano a watan Yulin 1981, wanda bayan nan ne aka ƙirƙiro wasu masaautun a Kano, amma sai dai bayan hawan mulkin marigayi Sabo Bakin Zuwo aka soke su.

Sarkin Daura - Umar Faruk

SARKIN DAURA

Na baya-bayan nan shi ne dakatar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, da gwamnatin Katsina ta yi bayan zargin cin zarafin da wata baƙuwa mai yawon buɗe ido ta yi a kansa.

A 2026 gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, daga dukkan ayyukan masarauta da wasu tafiye-tafiye, bayan zargin cin zarafin da wata baƙuwa mai yawon buɗe ido ta yi a kansa.

A cikin bidiyon da ta wallafa an ga baturiyar a cikin fada irin ta masarautun ƙasar Hausa tare da wani da ake kyautata zaton Sarkin Daura ne Alhaji Faruk Umar Faruk.

A cikin bidiyon an ji yadda matar, wadda ta bayyana kanta da suna Beduina a shafin instagram ke cewa : "ɗaya daga cikin abin da ya burge ni shi ne jin tarihin Daura, kasancewar a baya mata ne suke mulkin Daura".

A ƙarƙashin bidiyon da ta wallafa, matar ta ce ta naɗi bidiyon ne ta amfani da tabarau ɗin da take sanye da shi mai kyamarar ɗaukan hoto, wanda ake kira Meta glasses a Ingilishi.

Ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a cikin watan Nuwamban 2026 sa'ilin da ta je yawon bude ido a Najeriya.

Sarkin Birnin Yandoton Zamfara

A cikin shekarar 2022 ne gwamnatin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta dakatar da Sarkin ƴandoton Daji bayan bai wa ƙasurgummin ɗan fashin dajin nan Adamu Aliero, sarautar Sarkin Fulani.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi 17 ga watan Yunin 2022, inda ta ce ba ta da masaniyar naɗin da aka yi wa Adamu Aliero, wanda hukumomin tsaron Najeriya ke nema ruwa-a-jallo.

An dai miƙa riƙon sarautar sarkin ga sarkin garin na 'Yandoton ga Alhaji Mahe Garba Marafa, wanda shi ne Hakimin 'Yandoto.

Sai dai daga bisani gwamnatin ta mayar da shi kan muƙaminsa bayan da kwamitin da aka kafa don bincike akansa ya wanke shi daga zargin.

Sarkin Lame - Aliyu Yakubu

Mai Martaba Sarkin Lame Alhaji Aliyu Yakubu Lame

Mai Martaba Sarkin Lame Alhaji Aliyu Yakubu Lame shi ma na cikin jerin sarakuna da aka ta ɓa dakatarwa.

Gwamnatin Jihar Bauchi ce ƙarƙashin gwamna jihar Bala Mohammed ta dakatar da Mai Martaba Sarkin na Lame, Alhaji Aliyu Yakubu Lame, daga kujerarsa nan take.

Dakatar da shi ɗin ta biyo bayan zarge-zargen da ake yi wa Sarkin na karɓar haraji ba bisa ƙa'ida ba, da tsoma baki a harkokin rabon filaye ba tare da izini ba, da yi wa kamfanonin haƙar ma'adinai katsalandan a yankin masarautarsa, in ji gwamnati.

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar a ranar 14 ga watan Nuwamba, 2026, ta ce dakatarwar ta wucin gadi ce, tare da bai wa hukuma damar gudanar da bincike na gaskiya ba tare da wata tangarɗa ba.

Gwamna Bala Mohammed ya kafa kwamitin bincike mai mambobi 12, wanda aka ba shi wa'adin mako uku don bincikar waɗannan zarge-zarge da kuma miƙa rahoto tare da shawarwari ga gwamnati.

Haka kuma an umurci Galadiman Lame, Alhaji Bala Abubakar ya ci gaba da kula da harkokin gudanarwar masarautar.

Sarkin Gwandu - Haruna Jokolo

A ranar 3 ga watan Yunin 2005 ne Gwamnan jihar Kebbi na lokacin, Adamu Aliero ya sauke Sarkin Gwandu, Alhaji Al-Mustapha Haruna Jokolo saboda zargin 'furta kalaman tunzura alʼumma.

Saukewar tasa ta zo bayan da gwamnatin jihar ta zarge shi da yin kalaman da za su iya zama "barazana ga tsaron ƙasa".

Sai dai a shekarar 2014 da kuma 2016 ne Babbar Kotun Jihar Kebbi da kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara suka soke sauke shin. Amma Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin gwamnatin ta Kebbi na sauke rawanin sarkin a watan Yunin 2025.

Sarkin Maru - Abubakar Chika

Sarkin Maru Abubakar Chika
Bayanan hoto, Sarkin Maru Abubakar Chika

Sarkin Maru Abubakar Chika ne basarake na farko da gwamnatin PDP a Zamfara ta fara dakatarwa tare da tuɓe shi kan zargin hannu a matsalar tsaron jihar.

A watan Agustan 2019 gwamnatin Bello Matawalle ta tsige Sarkin Maru Abubakar Chika bisa zargin cin amanar talakawansa kan alaƙarsa da ƴan bindiga masu kashewa da satar mutane.

Gwamnatin Zamfara ta ce ta tsige Sarkin na Maru ne bayan da kwamitin da ta kafa na binciken zarge-zargen hannun sarakunan gargajiya a sata da garkuwa da mutane, ya samu Sarkin 'da hannu dumu-dumu'.

Gwamnatin ta fara dakatar da basaraken ne kan zarginsa da wasu talakawansa suka yi yana da alaka da masu satar jama'a.

Sai dai ɓangaren sarkin na Maru ya musanta zarge-zargen da ake yi wa basaraken.

Baya ga sarakuna akwai kuma wasu hakimai ko dakatai da aka dakatar waɗanda ake zarginsu da alaƙa da ƴan bindiga.

Sarkin Zurmi - Atiku Abubakar

Atiku Abubakar
Bayanan hoto, Atiku Abubakar

Sarkin Zurmi, Atiku Abubakar shi ma na daga cikin Saakunan da gwamnatin tsohon gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle shi ma ta dakatar kan zarginsa shi ma da alaƙa da kashe-kashen da 'yan fashin daji ke yi a yankin masarautarsa.

An dai dakatar da shi ne bayan wani kwamati da gwamnatin lokacin ta kafa don yin bincike ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin gwamnan jihar Ibrahim Wakkala kan zarge-zargen da ake yi wa basaraken.

An umarci Bunun Kanwa, Bello Suleiman, ya karɓi jagorancin masarautar nan take.