Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Musulmi na farko da zai iya zama sanata a Amurka
- Marubuci, Fernando Duarte
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News World Service
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Zaben tsakiyar wa’adi da aka gudanar ranar Talata, 3 ga watan Nuwamba ne zai tantance jam’iyyar da za ta zamo mai rinjaye a majalisar dokokin Amurka daga yanzu har zuwa karshen mulkin shugaba Donald Trump.
To amma akwai yiwuwar zaben ya shiga cikin tarihi sanadiyyar wani abu daya - a jihar Michigan, kuri’ar jin ra’ayi na nuna cewa dan takarar Jam’iyyar Democrat Abdul El-Sayed zai iya zama Musulmi na farko da zai zama sanata a kasar.
El-Sayed, wanda likita ne wanda bai taɓa rike mukamin siyasa ba na a tsakiyar wani yakin neman zabe wanda ya haifar da rarrabuwar kawuna saboda bambancin launin fata.
Al’amura sun kara dagulewa ne a ranar karshe ta yakin neman zabe, bayan da abokiyar karawarsa a zaben fitar da gwani a jam’iyyar Democrat, Haley Stevens, wadda ya kayar da bambancin kuri’u kalilan, ta ayyana goyon bayanta ga dan takarar jam’iyyar Republican, Mike Rogers.
A ranar Lahadi El-Sayed ya mayar da martani game da hakan a lokacin fira da ‘yan jarida da cewa: “Wannan jiha ce mai kunshe da mutane miliyan 10 wadanda suka cancanci mulki mai inganci daga gwamnati. Na fi mayar da hankali kan sauran mutane miliyan 9,999,998 wadanda ba a kansu kuke magana ba.”
Wanda aka haifa a shekarar 1984 a unguwar Rochester Hills da ke gefen birnin Detroit ya taso ne a hannun mahaifinsa da matar mahaifin nasa Jacqueline Johnson, bayan da auren iyayensa ya mutu lokacin yana dan shekara uku.
Ya yi karatun likitanci a jami’ar Michigan da kuma jami’ar Columbia University, inda ya kware a harkar cutuka masu saurin yaduwa.
Nadin da aka yi masa a matsayin shugaban sashen lafiya na jihar Detroit a shekarar 2015 ya sa sunansa ya bazu a sassan Amurka.
Sai ga shi shekara uku bayan haka El-Sayed ya tsaya takarar gwamnan Detroit. Ya zo na biyu a zaben fitar da gwani da aka yi na jam’iyyar Democrat, inda ya yi rashin nasara da kimanin kashi 20 cikin dari na kuri’un a hannun Gretchen Whitmer, wadda ta lashe zaben gwamnan.
Whitmer ta goyi bayan Stevens a zaben fitar da gwanin sanata na wannan shekarar sai dai ta bayyana goyon bayanta ga El-Sayed bayan nasarar da ya samu.
Yana samun goyon bayan wasu jiga-jigan jam’iyyar Democrat kamar sanata Bernie Sanders da ‘yar majalisa Alexandria Ocasio-Cortez.
Haka nan kuma ‘yan Democrats masu sassaucin ra’ayubkamar tsohon shugaban Amurka Barack Obama sun nuna goyon bayansu ga yakin neman zabensa, musamman ganin cewa lashe zaben na Michigan zai taimaka wa shirin Democrat na samun rinjaye a majalisar dattijain Amurka.
El-Sayed ya yi yakin neman zabe ne bisa doro na masu sassaucin ra’ayi, inda yake sukar tallafin da Amurka ke bai wa Isra’ila da kuma goyon bayan tatsar haraji daga attajirai domin zubawa a harkar kiwon lafiya na kasar.
”Bai kamata ya zama abu mai wahala ba idan kuka biya harajinku tare da sanin cewa za a kashe kudin ne domin amfanin ku da yaranku a maimakon kefa bama-bamai a kan yaran waau mitanen,” in ki El-Sayed, kamar yadda ya shaida wa masoyansa a lokacin yakin neman zabe a a ranar 29 ga watan Oktoba.
Ya kuma bayyana hare-haren da Isra'ila ta kai a Gaza bayan harin Hamas na 7 ga watan Oktoban 2023 a matsayin kisan kiyashi, wani zargi da Isra'ila ta sha musantawa, sannan ya zargi Isra'ila da aikata ayyukan ƙyamar ɗan'adam a Gaɓar Yamma.
Adawar da El-Sayed ke yi ga tura tallafin sojin Amurka ga ƙasashen waje bai tsaya kan Isra'ila kawai ba, mutumin mai shekara 42 ya sha nanata cewa yana a riƙa amfani da kuɗaɗen harajin Amurka "wajen gina makarantu da samar da damarmaki a maimakon tura kuɗin zuwa waje domin jefa bama-bamai a kan mutane".
"Ba na tunanin ya dace mu riƙa bai wa sojojin ƙasashen waje kuɗi gaba ɗaya," kamar yadda El-Sayed ya faɗi a ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba. "Daga Isra'ila, zuwa Masar da Saudiyya da Qatar da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa."
Sai dai duk da haka shugaban Amurka Donald Trump ya zargi El-Sayed, wanda ɗa ne ga wani mutum ɗan asalin ƙasar Masar, da zama "mai goyon bayan ƴan ta'adda".
Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya faɗa wa dandazon mutanen da yake wa jawabi a ranar 15 ga watan Oktoba cewa: "kun cancanci samun mutumin da ya fi wannan ƙaramin ƙudan wanda ya kamata a ce ya ja bakinsa ya yi shiru sannan ya gode wa ƙasar da ta samar masa komai."
"Sunana da addinina ba shi ne dalilin da ya sa mutane ba sa iya sayen makamashin girki da kayan abinci da gaza samun kuɗin zuwa asibiti ko shiga cikin damuwa kan rayuwa ba," in ji El-Sayed.
"Duk da cewa yadda nake ibadata za ta iya shan bamban da wasu Amurkawa, amma abubuwan da muke roƙo ɗaya ne."