Me ya sa zaɓen tsakiyar wa'adin mulki a Amurka yake da muhimmanci ga Trump?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Yayin da kwanaki kaɗan suka rage kafin zaɓen tsakiyar wa'adi a Amurka, masu kaɗa ƙuri'a na shirye-shiryen jefa ƙuri'unsu a wani zaɓe da zai iya yin babban tasiri ga ragowar wa'adin shugabancin Donald Trump.

Menene zaɓen tsakiyar wa'adi?

A ranar 3 ga Nuwamba, 'yan ƙasar Amurka za su zaɓi mambobin Majalisar Dokoki ta Congress, wadda ta ƙunshi Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa.

Ana gudanar da wannan zaɓe duk bayan shekara biyu. Idan an yi shi a tsakiyar wa'adin shekara huɗu na shugaban ƙasa, ana kiransa zaɓen tsakiyar wa'adi .

Daya daga cikin muhimman ayyukan Congress shi ne kafa dokokin tarayya da ake amfani da su a faɗin Amurka.

Sakamakon zaɓen zai tantance wace jam'iyyar siyasa za ta mallaki ikon Congress, tsakanin Jam'iyyar Republican ta Trump da Jam'iyyar Democratic ta adawa, lamarin da zai shafi yadda shugaban ƙasa zai samu sauƙin aiwatar da tsare-tsarensa.

Haka kuma za a ɗauki sakamakon a matsayin ma'aunin yadda Amurkawa ke gamsuwa da yadda shugaban ƙasa ke gudanar da aikinsa zuwa yanzu.

Su wa ake zaɓa?

Za a zaɓi dukkan mambobi 435 na Majalisar Wakilai, wadda ita ce majalisar ƙasa ta ƙasa ta Congress. Waɗannan mambobi suna yin wa'adin shekara biyu kacal.

Majalisar Wakilai ce ta fi kula da gabatarwa da tattauna kudurin dokoki.

Haka kuma, za a gudanar da zaɓe domin cike kujeru 35 daga cikin kujeru 100 na Majalisar Dattawa, wadda ita ce majalisar koli ta Congress. Sanatoci suna yin wa'adin shekara shida.

Daga cikin sauran ayyukanta, Majalisar Dattawa tana da ikon amincewa ko hana kudurorin dokoki da Majalisar Wakilai ta amince da su.

A ranar guda, masu kaɗa ƙuri'a a sassa da dama na Amurka kuma za su zaɓi gwamnonin jihohinsu.

Zaɓen gwamna a jihohin California, Florida, Georgia da Michigan na daga cikin zaɓukan da ake sa ran za a fi sanya ido a kansu.

Wadanne manyan batutuwa ne?

Tattalin arzikin Amurka na daga cikin manyan batutuwan da ke damun masu kaɗa ƙuri'a da ke fama da hauhawar farashin man fetur, abinci, gidaje da kuma harkokin kiwon lafiya.

Har yanzu hauhawar farashin kayayyaki yana sama da matakin da Babban Bankin Tarayyar Amurka ke nema, lamarin da a wani ɓangare yake da alaƙa da yaƙin da Amurka da Isra'ila suka fara da Iran a watan Fabrairu.

Jam'iyyar Democratic na cewa shirin Shugaba Trump na sanya haraji kan kayayyakin da ake shigo da su daga ƙasashen waje ya kuma taimaka wajen ƙara tsadar rayuwa ga Amurkawa.

Shige da fice wani muhimmin batu ne. Jam'iyyar Republican na cewa Trump na cika ɗaya daga cikin manyan alƙawurransa na yaƙin neman zaɓen 2024 ta hanyar ƙarfafa tsaron kan iyaka da kuma ƙaddamar da babban shiri na yaƙi da shige da fice ba bisa ƙa'ida ba, matakin da ya sha janyo ce-ce-ku-ce.

A cikin makonnin baya-bayan nan, damuwa game da fasahar basirar wucin gadi (AI) ta ƙaru. Manyan 'yan siyasa daga jam'iyyun biyu suna ganin cewa ya kamata a sanya dokoki da za su daidaita amfani da wannan fasaha, ra'ayin da ya bambanta da na Trump, wanda ya yi adawa da ƙirƙirar dokokin da za su takaita ci gaban wannan fasaha.

Wane haɗari ake fuskanta?

Congress, tare da shugabancin ƙasa da kuma bangaren shari'a, na ɗaya daga cikin rassan gwamnati uku na Amurka. Ikon Congress wajen tsara da amincewa da dokoki yana da matuƙar muhimmanci.

A halin yanzu, Jam'iyyar Republican ce ke iko da Majalisar Wakilai da kuma Majalisar Dattawa. Sai dai rinjayen kujerunta ba shi da yawa.

Jam'iyyar Republican na da kujeru 218 a Majalisar Wakilai, wanda shi ne mafi ƙarancin adadin da ake buƙata domin mallakar ikon majalisar. Haka kuma suna da ɗan majalisa guda ɗaya mai zaman kansa wanda ke kaɗa ƙuri'a tare da su.

A Majalisar Dattawa kuwa, Republican na da kujeru 53.

Ikon Majalisar Dattawa na iya sauyawa idan Jam'iyyar Democratic ta lashe kujeru 51. Idan kuma jam'iyyun biyu suka samu kujeru 50-50, mataimakin shugaban ƙasa, wanda a yanzu ɗan Republican ne, zai iya kaɗa ƙuri'ar warware kunnen doki.

Idan Jam'iyyar Democratic ta adawa ta samu nasarar ƙwace ikon aƙalla ɗaya daga cikin majalisun biyu, za ta samu damar saka nata kudurorin dokoki cikin jadawalin tattaunawa da kuma neman amincewa da su su zama doka.

Ko Trump zai iya kara samun rinjaye?

A al'ada, masu kaɗa ƙuri'a a Amurka sun saba hukunta jam'iyyar shugaban ƙasa ta hanyar kaɗa ƙuri'a ga jam'iyyar adawa a zaɓen tsakiyar wa'adi.

Binciken ra'ayoyin jama'a na baya-bayan nan ya nuna cewa shugaban ƙasa na fuskantar ƙarancin goyon baya daga jama'a. A cewar shafin binciken ra'ayoyin jama'a na Silver Bulletin, Trump, wanda ya fara wa'adinsa na biyu da goyon bayan da ya ɗan wuce kashi 50%, ya ga wannan adadi ya ragu zuwa kusan kashi 37% a farkon watan Oktoba.

Kashi 61% na jama'a ba su gamsu da yadda yake gudanar da mulkinsa ba.

Sai dai ba duk kujerun majalisun biyu ne ake sa ran za a yi gasa mai zafi a kansu ba, domin wasu jihohi sun fi karkata ga Jam'iyyar Republican ko kuma Jam'iyyar Democratic.

Kamfanin labarai na CBS News, abokin hulɗar BBC a Amurka, ya bayyana zaɓen kujeru 10 na Majalisar Dattawa a jihohi irin su Iowa da New Hampshire, da kuma zaɓen kujeru 42 na Majalisar Wakilai a jihohi irin su Arizona da Ohio, a matsayin zaɓukan da ya kamata a sanya ido sosai a kansu.

Ana kuma sa ran zaɓen na wannan shekara ya kasance mai wahalar hasashe sakamakon saɓanin da ke tsakanin jam'iyyun biyu kan yadda ya kamata a zana iyakokin mazabun Majalisar Wakilai.

Jam'iyyar Republican ta yi ƙoƙarin amfana ta hanyar tsara iyakokin wasu mazabu ta yadda za su ƙara mata damar samun nasara a wasu jihohi, yayin da Jam'iyyar Democratic ita ma ta ɗauki irin waɗannan matakai domin samun ribar siyasa.

Me hakan ke nufi ga Trump?

Idan Jam'iyyar Democratic ta samu ikon Majalisar Wakilai ko Majalisar Dattawa, zai fi wahala ga Trump ya samu amincewar duk wata doka ta wuce ta hanyar Congress. Wannan na iya kawo cikas ga shirye-shiryensa na siyasa a cikin gida.

Sai dai, Trump ya kasance yana neman hanyoyin amfani da ikonsa ba tare da dogaro da goyon bayan babban ɓangare na jam'iyyarsa ba.

Idan Jam'iyyar Democratic ta samu nasarar mallakar ikon majalisun Congress guda biyu, za ta sami damar amfani da kwamitocinta wajen gudanar da bincike kan batutuwa daban-daban da suka shafi gwamnatin Trump.

Zarge-zargen cin hanci da rashawa, gina sabon ɗakin taro a Fadar White House, da kuma hanyoyin da Hukumar Kula da Shige da Fice da Kwastam (ICE) ke amfani da su wajen kama da korar baƙi daga ƙasar, na daga cikin batutuwan da za a iya bincikawa.

Haka kuma akwai muhawara a cikin Jam'iyyar Democratic kan yiwuwar tsige Trump daga mulki. Matakin zai haɗa da gabatar da tuhume-tuhume a majalisa waɗanda za su zama tushen tsarin siyasa na tsige shugaban ƙasa daga kan mulki, wanda ba shari'ar laifi ba ne.

Idan Jam'iyyar Republican ta ci gaba da rike ikon Congress, Trump zai iya ci gaba da aiwatar da shirye-shiryensa a sauran wa'adin shugabancinsa.

Me hakan ke nufi ga zaɓen 2028?

Sunan shugaban ƙasa ba zai kasance a takardar kaɗa ƙuri'a ba a zaɓen tsakiyar wa'adi. Sai dai Trump ya ƙarfafa 'yan Republican su ɗauki zaɓen kamar sunansa ma yana cikin takardar zaɓe, ta hanyar kaɗa ƙuri'a ga 'yan takarar jam'iyyarsa a matsayin hanyar nuna goyon baya ga matakan da ya ɗauka zuwa yanzu.

Ko da kuwa sakamakon zaɓen ya kasance yaya, masu sharhi za su iya amfani da shi wajen tantance ra'ayin masu kaɗa ƙuri'a game da alkiblar da Amurka ke bi ƙarƙashin jagorancin Trump.

Trump ba zai iya sake tsayawa takarar shugabancin ƙasa karo na uku ba. Bayan zaɓen tsakiyar wa'adi, ana iya fara tattaunawa da hasashe kan wanda zai gaje shi a matsayin ɗan takarar Jam'iyyar Republican a zaɓen shugaban ƙasa na 2028, da kuma wanda zai nemi shugabancin ƙasa a ƙarƙashin inuwar Jam'iyyar Democratic.