Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masu horaswa 6 da suka rasa aikinsu bayan gasar Kofin Duniya
Gasar kofin duniya ta zo da sauye-sauye da dama ciki har da yawan ƙarin ƙasashe daga 32 zuwa 48.
Wannan ya bai wa ƙasashe da yawa ƙwarin gwiwar za su iya taka rawar azo a gani a gasar saboda faɗaɗa ta da aka yi.
Kasashe irinsu South Korea da suka fara gasar da ƙafar dama bayan cinye Czech Republic 2-1 sun sanya rai sosai a gasar, sai dai a ƙarshe ko iya samun fitowa daga rukuni ba su yi ba.
Wasu kuma irinsu Portugal sun kai ga fitowa sai dai tafiyar tasu ba ta yi nisan da aka yi tsammani ba.
Bayan cire wasu ƙasashe daga gasar, irinsu Senegal, an samu ɓaraka tsakanin 'yan wasa da mai horaswa wanda ya fito da wani ɓoyayyen rikici da ba a san da shi ba.
Wasu ƙasashe kuwa irinsu Tunisia tun a wasan farko na gasar suka sallami mai horaswa saboda gaza yin abin da aka yi tsammani.
Bari mu yi nazari kan wasu daga cikin masu horaswa da suka rabu da ayyukansu bayan fitarsu daga gasar kofin duniya.
Ronald Koeman - Netherlands
Ronald Koeman ya yi ritaya ne bayan an cire ƙasar Netherlands da yake jagoranta daga gasar kofin duniya.
Labarin ajiye aikinsa ya zo ne lokacin da ake ta fama da zage-zagen nuna wariya ga 'yan wasan da suka zubar da fenariti irinsu Kluivert a kafafen sada zumunta.
Morocco ne suka cire ƙasar ta Koeman a matakin 'yan 32 a bugun fenariti, bayan sun tashi kunnen doki 1-1.
Justin Kluivert da Quinten Timber da kuma Crysencio Summerville dukansu sun zubar da fenaretin wanda hakan ya janyo musu zagin wariyar launin fata.
Kocin ya bayar da uzurin cewa matarsa ba ta da lafiya shi ya sa yake son ya ajiye aikin ya zauna tare da ita domin lura da lafiyarta
Pape Thiaw - Senegal
Senegal ta kori kocinta Pape Thiaw daga bakin aiki bayan cire su da aka yi a matakin 'yan 32 a gasar Kofin Duniya.
Teranga Lions tana tare da Thiaw tun Disambar 2024, amma a gasar da aka cire su sun fara da rashin nasara ne a hannun Faransa sannan suka ƙara a hannun Norway a duka wasanninsu na farko guda biyu.
Sun doke Iraƙi ne 5-0 suka samu damar fitowa mataki na gaba, su ne masu maki uku kacal kuma suka iya kai wa matakin 'yan 32.
A matakin Belgium ta doke Senegal da ci 3-2, a wasan da Senegal ta ci 2-0 har zuwa minti na 85 da fara wasan, suka farke kafin kuma a tashi suka cinye Senegal.
Korar tasa ta biyo kukan da Pape Gueye cewa zai daina bugawa ƙasar wasa matukar kocin da tawagarsa na ci gaba da horar da tawagar.
Julian Nagelsmann - Germany
Kocin Jamun Julian Nagelsmann shi ma guguwar kofin duniya ta tafi da shi, bayan wata cirewa da ƙasar Paraguay ta yi mata mai matukar girgizawa a matakin 'yan 32.
Duk da cewa bai nuna yana son tafiya ba, a wata tattaunawa da aka yi da shi ya ce "ban yi kalar mutanen da za su gudu ba" amma daga baya sai yaji Hukumar Kwallon Ƙafa ta Jamus ta fara magana da wanda ake so ya maye gurbinsa.
Wannan abu ya kaɗa Julian Nagelsmann bai yi niyyar barin aiki ba a wannan lokaci sai dai ba shi da wani zaɓi da ya rage masa.
Tsohon kocin Liverpool Jurgen Klopp ne aka amince da zai maye gurbin kocin da ya bar aiki.
Kuma tuni ya amsa wa hukumar Kwallon Ƙafar cewa zai yi aiki, kamar yadda ta sanar.
Wannan ce gasa ta biyu da Julian Nagelsmann ya jagoranta bayan Euro 2024 da yaje wasan kusa da dab da na ƙarshe.
Tun 2014 da ta ci kofin duniya rabon da Jamus ta ci wasan sili ɗaya kwale, ba ta iya wuce matakin rukuni ba a 2018 da 2022.
Roberto Martinez - Portugal
Hukumar Kwallon Ƙafa ta Portugal ce ta ba da sanarwar ajiye aikin kocin tawagar ƙasar bayan Spain ta cinye su a wasan matakin 'yan 16.
Tun a Janairun 2023 Martinez ya ba da sanarwar zai ajiye muƙaminsa.
Portugal ta kammala wasan rukuni a matsayi na biyu, ta yi canjaras biyu da Colombia da kuma DR Congo ta fatattaka Uzbekistan da ci 5-0, ta cinye Croatia a matakin 'yan 32.
A matakin 'yan 16 kuwa Spain ce ta doke Portugal a mintinan ƙarshe na wasan 1-0 ta hannun dan wasanta na gaba Merino.
Martinez mai shekara 52, shi ne ya jagoranci Portugal zuwa UEFA Nations Lig a 2025, sai dai a 2024 an cire tawagarsa ne a matakin wasan kusa da dab da na ƙarshe a hannun Faransa a bugun fenariti.
Kocin ya sha suka saboda ana zarginsa da baiwa Ronaldo wanda ya girma dama sama da matasan 'yan wasansa da za su iya kai tawagar ga nasara.
Hong Myung-Bo - South Korea
Ƙasa da kwana guda da cire Korea ta Kudu daga kofin duniya kocin ƙasar Hong Myung-Bo ya sanar da ajiye aikinsa.
Ritayar tasa ta biyo bayan wata kakkausar suka da Shugaban ƙasar ya yi masa, har ya kira shi da "wanda bai kware ba" ya kuma nemi a yi bincike mai zurfi kan rawar da suka taka a gasar.
Ƙasar ta fara da nasara ne a wasan farko tsakaninta da Czech amma wasanni biyu saura na rukuni duka aka doke ta.
Ƙiris ya hana ta kaiwa zagayen 'yan 32, domin sai da ta jira ko da Mexico za ta yi canjaras ko a doke ta, amma Mexico ta ci wasanta.
Kocin Hong Myung-Bo ya fito ya nemi afwa a fili, yana cewa ya ɗauki nauyin laifin gazawar a matsayinsa na koci.
Sabri Lamouchi - Tunisia
Tunisia ce ta fara korar kocinta Sabri Lamouchi a Kofin Duniya bayan kashin da ta sha a wasan farko na gasar
Sweden ce ta fara zazzaga mata 5-1 a rukunin F a wasan da suka yi a filin wasa na Monterrey a Guadalupe, da ke Mexico.
Bayan nan rahotanni sun kunno kai cewa an kori Lamouchi ba tare da ɓata lokaci ba, amma wata majiya ta shaida wa BBC cewa kocin shi ne ma ya jagoranci atisayen tawagar a washe garin ranar korar.
Amma daga baya Hukumar Kwallon Ƙafar Tunisia ta sanar da cewa an rabu ne cikin mutunci da girmama juna.
Daga nan ne suka naɗa tsohon kocin Morocco da Saudiyya Herve Renard a matsayin sabon kocin ƙungiyar zuwa ƙarshen gasar.
Lamouchi shi ne na farko da aka kora a gasar, kuma bayansa wasu da dama sun bar aiki.