Fifa ta fara bincike kan kan faɗan da aka yi bayan wasan karshe
Hukumar kwallon ƙafa ta duniya Fifa za ta fara bincike kan mummunar halayyar ta 'yan wasan Argentina suka nuna bayan kammala wasan ƙarshe na Kofin Duniya.
Fifa ta nemi kwamitin ladabtarwarta ya samar da wani kwamiti da zai bincike kan lamarin domin tabbatar da abin da ya faru a filin wasa na MetLife.
Duk ɗan wasa ko koci da aka samu da hannu cikin lamarin za a dakatar da shi, kuma za a ci tarar hukumar kwallon ƙafa ta Argentina.
Bayan rashin nasarar da ta yi a hanun Spain 1-0 a ranar Lahadi, wasu 'yan wasa da kuma mutanen tawagar kocin Argentina sun kama rikici da yan wasan Spain lokacin da suke murnar cin wasansu.
Nahuel Molina da Leandro Parades da Thiago Almada da mataimakin kocin Roberto Ayalla duka an gansu cikin rikicin.