Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool za ta sake yunkurin dauko Sarr a watan Janairu
Liverpool na duba yiwuwar sake yunkurin daukar dan wasan gaba na Crystal Palace, Ismaila Sarr a watan Janairu bayan ta gaza cimma yarjejeniyar sayen dan wasan mai shekara 28 dan kasar Senegal kafin karshen rufe kasuwar cinikayyar yan kwallo a bazara nan. (Football Insider)
Dan wasan gaba na Tottenham dan asalin Brazil Richarlison na fatan kammala komawa gasar Saudi Pro League bayan da batun komawarsa kungiyar Trabzonspor ta Turkiyya aka kasa kammala cinikin kafin rufe kasuwar cinikin 'yan wasa a Kasar a ranar Juma'a. (Standard)
Arsenal na dab da cimma yarjejeniya a kan tsawaita sabuwar kwantiragi da kocinta Mikel Arteta, wanda yarjejeniyarsa ta yanzu za ta kare a karshen wannan kakar wasa yayin da a gefe guda ta ke ci gaba da tattaunawa don tsawaita yarjejeniyar wasu fitattun 'yan wasanta, ciki har da dan wasan tsakiya na Ingila Declan Rice mai shekaru 27, da dan wasan Norway Martin Odegaard mai shekaru 27, da kuma mai tsaron baya na Netherlands Jurrien Timber mai shekaru 25. (Teamtalk)
Arsenal ta yi sha'awar daukar dan wasan gefe na Jamus Kevin Schade a lokacin kasuwar cinikin 'yan wasa ta bazara yayin da kungiyar Brentford ba ta yi niyyar sayar da dan wasan mai shekaru 24 ba.. (Teamtalk)
Manchester United za ta ci gaba da bibiyar dan wasan baya na Newcastle United , Lewis Hall mai shekaru 21, da nufin duba yiwuwar daukar sa a lokacin kasuwar cinikin 'yan wasa ta bazara mai zuwa. . (Football Insider)
Dan wasan tsakiya na Belgium, Amadou Onana, ya sanya hannu a kan sabuwar yarjejeniyar da zata kai karshen kakar 2031 da kungiyar Aston Villa.(Sacha Tavolieri)
Har yanzu AC Milan na sha'awar daular mai tsaron bayan Sporting Lisbon, Goncalo Inacio, sannan kuma za ta yi yunkurin daukar dan wasan Portugal a kasuwar cinikin 'yan wasa a watan Janairu. (Tuttomercatoweb - in Italian)
Har yanzu Manchester United na tattaunawa akan yiwuwar daukar dan wasan tsakiya na Ingila Louis Page daga Leicester City, bayan da kungiyar ta gaza cimma matsaya akan sayen dan wasan mai shekaru 18 a kasuwar cinikin 'yan wasa a bazarar nan. (Manchester Evening News via Evening Standard)
Aston Villa da Sunderland na daga cikin kungiyoyin da suka nuna sha'awarsu ta daukar mai tsaron bayan Faransa Matthieu Udol, sai dai kuma Lens ta hana mai shekaru 30 barin kungiyar. (Foot Mercato, via Get French Football News)