Real Madrid za ta bada fam miliyan 130 kan Olise,RB Leipzig za ta rike Diomande

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Real Madrid za ta yi wa Bayern Munich tayin fam miliyan 130 kan dan wasan Faransa Michael Olise, mai shekara 24, idan aka zabi Florentino Perez a matsayin shugaban kungiyar.(Telegraph - subscription required), external

Tsohon kocin Liverpool Arne Slot, da kungiyar ta kora a makon daya gabata, ya yi watsi da damar rike ragamar horar da 'yan wasan kungiyar Fulham bayan da Marco Silva ya sanar da cewa zai bar kungiyar ta landan. (Talksport), external

Yunkurin da Barcelona ke yi na sayan dan wasan Argentina Julian Alvarez ya gamu da cikas kuma Atletico Madrid na shirin saka sunansa a cikin jerin 'yan wasan da za su yi wasa a kaka mai zuwa, ya yin da Arsenal ita ma ta na sha'awar daukarsa, sai dai ba ya son ya koma Landan (Cadena Ser - in Spanish), external

Watakila dan wasan Chelsea da Ingila Liam Delap, mai shekara 23, ya koma Fulham idan tsohon kocinsa a Ipswich Town, Kieran McKenna, ya maye gurbin Marco Silva a Craven Cottage. (Talksport), external

Tsohon kocin Crystal Palace Oliver Glasner ya fi kocin tawagar Amurka Mauricio Pochettino damar zama sabon kocin AC Milan. (Gazzetta dello Sport - in Italian), external

Dan wasan AC Milan Rafael Leao, mai shekara 26, ya ce yana bukatar sabon wuri, inda dan wasan kasar Portugal ya yi ammanar cewa koma wa gasar wasan Premier League ko La Liga zai dace da shi . (Sport TV, via Football Italia), external

Kawo yanzu RB Leipzig tana da kwarin gwiwar cewa dan wasan gaban Ivory Coast Yan Diomande, mai shekara 19, zai ci gaba da zama a kungiyar a bazarar nan duk da kokarin da Liverpool ke yi domin daukarsa.(Teamtalk), external

Newcastle United na shirin sanya hannu kan cinikinta na farko a wannan bazara bayan sun amince da yarjejeniyar fam miliyan 24 kan mai tsaron ragar Faransa Reims Ewen Jaouen mai shekaru 20.(Northern Echo), external

Kocin Tottenham Roberto de Zerbi na son dan wasan Croatia Luka Vuskovic mai shekara 19 ya bar kungiyar a wannan bazara . (Football Insider), external

Barcelona za ta sayi Marc Cucurella, mai shekara 27, daga Chelsea idan ta yanke shawarar sayarda dan wasan Sfaniya Alejandro Balde, mai shekara 22, a wannan bazara (Marca - in Spanish), external