Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Pakistan ta yanke shawarar buɗe wa Iran hanyar kasuwanci?
Pakistan ta sanar da cewa za ta buɗe hanyar kasuwanci ga Iran, wanda zai bai wa ƙasar damar amfani da tasoshin ruwan Pakistan ɗin na Gwadar da Karachi wajen dakon kayayyaki.
A cewar "Umarnin fitar da kayayyaki ta Pakistan na 2026" wanda ma'aikatar harkokin kasuwanci ta fitar, ya ce an buɗe wasu hanyoyi guda shida domin jigilar kayakin Iran. Ta waɗannan hanyoyi, Iran za ta iya fitar da kayayyakinta zuwa ƙasashe ta tasoshin ruwan Pakistan ko kuma shigar da kayaki ƙasarta da ta saya daga wasu ƙasashe.
Sanarwar ɗaukar wannan mataki da gwamnatin Pakistan ta yi, ya zo a daidai lokacin da Iran ke fuskantar wahalhalu wajen shigar da kayaki cikin ƙasar daga wasu ƙasashe ko kuma sayar da kayanta saboda toshe hanyoyin ruwanta da Amurka ta yi.
Ƙasashe dai na amfani da tashoshin jiragen ruwan wasu ƙasashe don yin kasuwanci. Afghanistan ta yi amfani da tashoshin ruwan Pakistan na gomman shekaru wajen yin kasuwanci. Sai dai, Iran tana da tashoshin ruwa masu aiki waɗanda take amfani da su wajen fitar da mai da sauran kayaki zuwa ƙasashe daban-daban a faɗin duniya.
Yayin da Pakistan ke kasancewa mai shiga tsakanin Amurka da Iran wajen ganin an kawo karshen yaƙi, masu sharhi na cewa matakin Islamabada wata hanyace mai muhimmanci wajen gina alaƙa mai kyau da kuma yarda tsakaninsu da Iran.
Me wannan mataki ke nufi?
Ma'aikatar harkokin kasuwanci da masana'antu ta Pakistan ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa: "Bisa wannan umarni, za a ci gaba da laluɓo hanyoyin ƙarfafa hanyar kasuwanci tsakanin Pakistan da Iran kuma zai taimaka wajen inganta harkar kasuwanci a yankin."
A cewar ministan kasuwancin ƙasar Jam Kamal, ya ce matakin "zai ƙarfafa muhimmancin Pakistan da kuma ɗora ƙasar kan turbar zama cibiyar hada-hadar kasuwanci ta yankin."
Ma'aikatar ta kuma ce: "Hanyoyi da dama, ciki har da na Gwadar da Karachi da kuma Taftan, an tsara su a matsayin hanyoyin jigilar kayaki, kuma don haka, aikin zai kasance gudana cikin gaskiya da kuma bisa tsari na dokoki."
Pakistan da Iran suna iyaka da juna na tsawon kilomita 909, kuma akwai hanyoyi dama a wannan kan iyaka.
Duk da yaƙin da ake yi, harkokin kasuwanci tsakanin Iran da Pakistan bai samu tsaiko ba.
Masu sharhi sun ce buɗe wannan hanyar kasuwanci ga Iran zai bai wa Pakistan damar kai wa ga ƙasashen tsakiyar Asiya a nan gaba.
Ma'aikatar harkokin kasuwanci ta Pakistan ɗin ta ce a 2008, an amince da yarjejeniyar kasuwanci tsakanin Islamabada da Tehran, kafin nan, gwamnatin Pakistan ta bayar da umarnin cewa a riƙa barin kayan Iran na fita ta iyakokin ƙasar.
Bisa wannan kuduri, Iran za ta iya amfani da Pakistan a matsayin hanyar shiga da kuma fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.
Pakistan ta sanar da buɗe hanyoyin kasuwanci guda shida ga Iran.
Mene ne muhimmancin wannan mataki?
Wani masanin tattalin arziki Abed Salehri ya ce: "Zai iya yiwuwa Pakistan ta buɗe wa Iran hanyar kasuwanci ne kaɗai bayan fada wa Amurka matakin nata."
Dakta Zubair Khan, tsohon minista a ma'aikatar kasuwanci ta Pakistan, ya ce: "Sharuɗan da ke lura da harkokin kasuwanci da Afghanistan irinsu ne za a yi amfani ga Iran ma bayan buɗe hanyar kasuwancin."
Ya ƙara da cewa: "Bayan yaƙi, lamarin ya kasance Iran ta zama kamar ƙasar da ba ta da ruwa."
A cewarsa, "wannan mataki ba wai zai kawowa Pakistan kuɗaɗen shiga bane kaɗai, zai kuma inganta alaƙa tsakanin mutanen Iran da Pakistan."
Ɗanjarida Mushtaq Ghahman ya ce: "Pakistan ta yanke shawarar buɗe hanyar kasuwancin ne bayan buƙatar haka daga wajen gwamnatin Iran."
Ya faɗa wa BBC cewa: "Bayan bazuwar rikici a rufe mashigar Hormuz, jagororin Iran sun buƙaci Pakistan ta buɗe musu hanyar kasuwanci, kuma bayan tattaunawa, tsakanin manyan jami'ai, Pakistan ta amince da matakin."
A cewarsa, Pakistan ta samarwa Afghanistan irin waɗannan hanyoyi a can baya, kuma a yanzu wannan mataki zai ƙarfafa damar Pakistan na nausawa Tsakiyar Asiya a nan gaba.
Masanin tattalin arziki Abed Salehri ya ce wannan matakin zai kara haɓaka kasuwanci tsakanin Iran da Pakistan da kuma samar da yanayin amincewa da juna.
Shin Pakisytan za ta iya buɗe wa Iran hanyar kasuwanci duk da takunkumin Amurka?
Iran ce ƙasar da ta fi samar da mai da kuma iskar gas a duniya. Sai dai, Pakistan na sayan mafi yawan mai da kuma gas daga Saudiyya da wasu ƙasashen Gulf.
Duba da takunkumin ƙasashe da kuma taƙaita hulɗar bankuna, Pakistan ba ta sayan mai wajen Iran, amma suna hulɗar kasuwanci na kayan masarufi, ciki har da abinci - kiuma an ci gaba da yin haka har a lokacin da ake yaƙi.
Tambayar ita ce, shin Pakistan za ta iya samar wa Tehran wannan dama duk da takunkumin da aka kakaba mata?
"Pakistan na son samar da hanyar kasuwanci ga ƙasar da aka toshe ruwanta a yanzu, bisa tsari na dokokin Majalisar Ɗinkin Duniya," a cewar Zubair Khan, tsohon minista a Pakistan.
Ya yi imanin cewa Pakistan ba za ta fuskanci takunkumi daga wajen Amurka ba kan wannan mataki saboda ƙara hulɗar kasuwanci kai-tsaye ba, kawai ta samar da hanyar da za a yi amfani da ita.
Abed Salhari shi ma ya ce: "Pakistan ta sanarwa Amurka da kuma dukkan ɓangarori da ya kamata kafin ɗaukar matakin, kuma babu yiwuwar cewa an ɗauki matakin ba tare da sanin Washington ba.
Zuwa yanzu, Amurka ba ta yi martani a hukumance kan buɗe hanyoyin kasuwancin ga Iran ba.
Mushtaq Gahman ya ce: "Saboda yaƙin da ake yi, akwai ƙarancin magunguna da sauran kayan masarufi a Iran, kuma Iran za ta iya shigo da irin kayakin da ba a saka musu takunkumi ba kaɗai ta Pakistan.
Mafarkin zama cibiyar kasuwanci ta yanki
Masana tattalin arziki sun ce wannan mataki yana da muhimmanci wajen mayar da Pakistan zama kasuwanci wanda zai haɓaka kasuwanci na yanki.
A farkon watan Afrilu, gwamnatin Pakistan ta tura jirgin ruwan dakon kaya na farko ta Iran zuwa Tashkent, babban birnin Uzbekistan, abin da ya buɗe hanyar kasuwanci tsakanin Iran da Pakistan.
Pakistan ta sanar a lokacin cewa motocin dakon kaya za su shiga Iran daga Karachi ta iyakokin Gabd da Rimdan, sannan a kai kayan zuwa Uzbekistan. Sanarwar ta ce matakin zai taimakawa kasuwancin duniya, karfafa alaƙar yanki da kuma daidaita tattalin arzikin ƙasashen yankin.
Abed Salehri ya ce: "A 2018, Islamabad da Tehran sun amince cewa Pakistan za ta samu damar kasuwanci da Turkiyya ta hanyar Iran, inda ita kuma Iran za ta aika kayayyaki zuwa China ta iyakar Pakistan."
Ya ƙara da cewa: "Idan Iran na hulɗar kasuwanci da ƙasashe ta tashoshin ruwan Pakistan, ita ma Pakistan za ta iya kasuwanci da ƙasashen Tsakiyar Asiya ta hanyar Iran."
A cewarsa, hakan zai fi sauki ga Pakistan maimakon amfani da hanyar Aghanistan.
Pakistan ta kasance tana amfani da hanyoyin Afghanistan wajen samun damar kai wa Tsakiyar Asiya ta ƙasa a baya, sai dai rashin tsaro da kuma zaman tankiya da Taliban sun jawo rufe iyakoki da kuma tsaiko a harkokin kasuwanci.