Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa ADC ke son a gaggauta yanke hukunci kan shugabancinta
Nan gaba a yau Alhamis ne ake sa ran kotun ƙolin kasar za ta yanke hukunci kan shari'ar rikicin shugabancin jam'iyyar hamayya ta ADC.
Hukuncin dai zai fayyace makomar jam'iyyar musamman hamayyar shugabanci tsakanin bangaren Sanata David Mark da kuma bangaren Nafiu Bala Gombe.
Tun da fari dai jam'iyyar hamayya ta ADC ta fara neman a gaggauta yanke hukunci kan saɓanin da take ciki kan sahihancin shugabancinta, lamarin da za a iya cewa ya tsayar da harkokin jam'iyyar cak.
Dukkan jam'iyyu suna da zuwa ƙarshen watan Mayu ne domin kammalawa tare da gabatar da ƴantakararsu da za su shiga takarar babban zaɓen 2027 kamar tsare-tsaren zaɓen 2027 suka nuna.
Ana dai ganin jam'iyyar ADC ce babbar wadda za ta yi hamayya da jam'iyya mai mulki ta APC, musamman ganin irin manyan ƴansiyasar da ke cikin jam'iyyar da kuma tarihin su.
Wani abu da ya ƙara ɗaukar hankali shi ne yadda ADC da PDP da wasu jam'iyyun hamayya suka haɗu, suka tattauna tare da ayyana ƙudurinsu na tsayar da ɗantakara ɗaya da zai fafata da Bola Tinubu a zaɓen na 2027.
Sai dai ADC na ta fama da rikicin gida, inda yanzu haka ake Kotun Ƙoli, inda ake sauraron hukuncin da za ta yanke.
Kotun ta ƙarshe a Najeriya ta kammala sauraron bayanan kowane ɓangare, sannan ta ce za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci, lamarin da ya jefa ƴan hamayya cikin ɗari-ɗari.
Sai dai a daidai lokacin da ake sauraron shari'ar ta Kotun Ƙoli, sai kwatsam wata kotun tarayya a Abuja ta dakatar da INEC daga amincewa da tsagin su David Mark a matsayin shugabannin jam'iyyar.
Buƙatar kammala shari'ar
Tuni dai babbar jam'iyyar hamayyar ta rubuta wasiƙa zuwa ga babbar mai shari'ar ƙasar, inda ta buƙaci ta saka baki domin tabbatar da an ƙarasa shari'ar jam'iyyar domin ta samu damar shiga zaɓen.
A wasiƙar da lauyan jam'iyyar ya rubuta a madadin tsagin shugabancin David Mark-led zuwa ga babbar mai shari'ar Kudirat Kekere-Ekun, ya buƙaci kotun ƙolin ƙasar ta gaggauta yanke hukuncin kan shugabancinta.
A wasiƙar, ADCn tsagin Mark ta ce bai kamata a ja ƙafa wajen yanke hukuncin ba, domin a cewarsu, hakan zai iya kawo tsaiko ga harkokin jam'iyyar, musamman ma shiga zaɓen 2027.
Lauyan ya kuma tunatar da babbar mai shari'ar cewa shirye-shiryen INEC suna tafiya, kuma hukumar zaɓen da lokaci take amfani.
"Lallai samun damar shiga zaɓukan 2027 ya dogara ne kacokam kan wannan hukuncin kan shugabancin jam'iyyar ADC."
Wasiƙar ta ƙara da cewa matuƙar ba a yanke hukuncin cikin gaggawa ba, lallai za a iya kai wa ga matakin da dole ADC ta haƙura da tsayar da ƴantakara a babban zaɓen 2027.
"Wannan kuma zai tauye haƙƙin miliyoyin ƴan Najeriya waɗanda suke da ra'ayin jam'iyyar ADC da kuma hana wasu ɗabbaƙa haƙƙin su na tsaya takara a jam'iyyar da suke so," in ji lauyan a wasiƙar.
Abin da muke so - ADC
Faisal Kabir mai magana ne da yawun ADC tsagin shugabancin David Mark ya ce sun je wajen babbar mai shari'ar ne domin suna buƙatar a kammala shari'ar a cikin lokaci.
''Ka san ita wannan shari'ar da ke gaban Kotun Ƙoli, shari'a ce da ke amfani da lokaci, tunda ka san sabbin dokokin zaɓe da aka sanya wa hannu na 2026 sun tabbatar da cewa zuwa ranar 10 ga watan Mayu, dole kowace jam'iyya ta miƙa sunayen ƴan jam'iyyarta ga INEC, idan ba haka ba, jam'iyya ba za ta tsayar da ɗantakara ba," in ji shi.
Faisar ya ce wannan ya sa suke ganin ya kamata kotun ta duba lamarin tare da tabbatar an yanke hukunci kan saɓanin na shugabancinsu, domin a cewarsa lokaci na neman ƙurewa.
Ya ƙara da cewa shari'a da yake tunanin tana da sauƙi, "domin neman amsa ne kan ko kotu na da hurumi a kan abubuwan da suka shafi jam'iyya duba da sashe 83 na kundin zaɓe ya ce kotu ba ta da hurumi. Wannan ya sa muke so Kotun Ƙoli ta fayyace mana."
A game da tanadin da suke da shi idan wannan bai samu ba, Faisal ya ce sun lura ana yunƙurin hana su tsayar da ɗantakara, inda ya ƙara da cewa sun shirya tsaf koma za su yi duk mai yiwuwa domin shiga zaɓen.
"Lallai za mu tsayar da ƴantakara a babban zaɓe, kuma za mu ƙalubalanci Bola Tinubu a zaɓen, sannan za mu yi nasara," in ji Faisal.
A game da sabon hukuncin da wata kotun daban ta fitar, inda ta buƙaci a daina sauraron tsagin Mark na ADC, Faisal ya ce dama suma sun dai zaɓi sababbi ne, amma ba su ce su fara aiki ba.
"Kotun cewa wa'adin shugabannin yanzu bai ƙare ba, kuma dama haka muka ce tun a baya. Mun dai yi zaɓen sababbin shugabanni, amma wa'adin na yanzu sai ranar 12 ga Mayu zai ƙare, kafin sababbi su fara aiki," in ji Faisal.