Dalilai huɗu da suka haddasa ƙaranci da tsadar citta a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Hankalin masu amfani da citta a Najeriya na ci gaba da tashi sakamakon ƙarancinta da tsadarta a kasuwannin ƙasar.
Citta dai wata nau'in saiwa ce da masana suka bayyana cewa ta samo asali ne daga yankin Kudancin Asia, kuma tana daga cikin kayan kamshi da ake amfani da su wajen dafe-dafen abinci ko kuma abin sha.
Ana kuma iya amfani da citta a ɗanyar ta, ko busasshiya ko a yi garinta har ma da ruwanta, kuma tana da sauƙin samu a kasuwanni a faɗin duniya.
Kusan za a iya cewa an fi noma citta a jihohin arewacin Najeriya musamman jihohi huɗu da ke noman cittar.
BBC ta tattuna da manoma da masu sana'ar citta dangane da dalilan da suka saka saiwar ta yi ƙaranci da tsada, inda kuma suka lissafa dalilai guda huɗu.
Rashin tsaro
Wasu daga cikin manoman sun ce tsada da ƙarancin cittar sun daɗe ba wai yanzu aka fara fuskantar su ba sakamakon matsalar tsaro da ke addabar yankin arewacin Najeriya, inda mafi akasarin jihohin da ake noma ta a can suke.
"Tsakani da Allah tsadar citta a Najeriya ba wai tun yau ba tun shekara guda da ta gabata daman kuɗin sun yi yawa. Gaskiya yawan tashin hankali ga inda muke noman ta ne ya yawaita a Najeriya," in ji wani manomin citta.
Jihohin Kaduna da Nassarawa da Neja da Plateau waɗanda su ne wuraren da aka fi noma cittar na fuskantar hare-haren ƴan bindiga.
"Matsalar tsaro na nan gaskiya. Duk ɗan kasuwar da ke son sayen citta sai dai ya bayar da kuɗi a bai wa direbobi su kai masa tunda hanyoyin ba su da kyau," in ji wani mai sana'ar sayar da citta.
Tsadar sufuri

Asalin hoton, Getty Images
Tun dai bayan da Najeriya ta zare hannunta daga tallafin man fetur da take bayarwa ƴan ƙasar a 2023, abubuwa suka yi tashin gwauron zabbi kuma ciki har da citta.
Sakamakon tsadar farashin man fetur ya sa kuɗin sufuri ya ƙaru inda kuma ya shafi duk wani abu da aka ɗauke shi a abin hawa domin kaiwa zuwa wani wuri.
Manoman cittar da masu saye da sayar da ita sun ce wannan ma na ɗaya daga dalilan da suka saka cittar ta ƙara yin tsada da ƙaranci a Najeriya.
Fitar da citta ƙasashen waje

Asalin hoton, Getty Images
Wani babban dalilin da ya sa cittar ta yi ƙaranci da tsada a Najeriya shi ne yadda ake tururuwar fitar da ita zuwa ƙasashen waje.
"A yanzu ganin ta ma samun sa'a ne domin buhu ɗaya na citta kusan naira 800,000 ne abin da bai wuce 120,000 ba. Kuma ga shi su Ƴan China sayen ta suke yi sosai...mu ake bai wa kuɗin mu saya mu aika musu. Su kuma sarrafa su dawo mana mu saya," in ji wani mai saye da sayar da citta.
Ɓoye citta domin ta yi tsada

Asalin hoton, Getty Images
Manoman da masu sayar da cittar sun kuma ce duk da tsadar da cittar ke yi a yanzu haka amma har yanzu akwai masu kuɗin da ke sayen cittar domin kawai su ɓoye ta har zuwa lokacin da ta ƙara hauhawa domin samun riba.
Wannan halayya dai ta sayen kayan noma a ɓoye domin idan lokacin tsadar abin ya yi a sayar ba sabon abu ba ne a Najeriya.
A shekarar 2025 sai da hukumar wayar da kan jama'a ta NOA ta yi gargaɗin cewa ɓoye kayan abinci na ɗaya daga cikin dalilan da ke ƙara janyo hauhawar farashi.










