Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Khalil al-Hayya, sabon shugaban ƙungiyar Hamas?
Ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas ta zaɓi, Khalil al-Hayya a matsayin sabon shugabanta, da zai maye gurbin Yahya Sinwar da sojojin Isra'ila suka kashe a watan Oktoban 2024 a Gaza.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce an zaɓi Al-Hayya bayan zagaye biyu na zaɓen shugaban ƙungiyar.
Tun da farko kan mambobin kwamitin zaɓen ya rabu kan wanda zai zama sabon shugaban ƙungiyar.
A zagayen farko na zaɓen ba a samu wanda ya yi nasara kai tsaye ba.
A cewar wani jami'in Falasɗinawa mai masaniya kan zaɓen, tsohon shugaban ofishin siyasa na Hamas, Khaled Mashaal, ya samu ƙuri'u fiye da Al-Hayya, amma bai kai adadin ƙuri'un da ake buƙata domin samun nasara kai tsaye ba.
Bisa ga dokokin Hamas, dole ne ɗan takara ya samu aƙalla ƙuri'u 36 daga kwamitin zaɓen mai mambobi 69.
An fahimci cewa zagaye na biyu na zaɓen ne ya tantance wanda ya yi nasara.
Wane ne Khalil al-Hayya?
An haifi Khalil al-Hayya ranar 5 ga watan Nuwamban 1960.
Ya samu digirinsa na farko a jami'ar Musulunci da ke Gaza, yayin da ya samu digirinsa na biyu a Jami'ar Jordan.
Sannan ya samu digirin digirgir a jami'ar Qur'ani da ilimin Addinin Musulunci.
Ya shiga Hamas ne bayan kammala digirinsa na farko a lokacin yana aiki a matsayin malamin makaranta.
Ya riƙe muƙamai a ƙungiyar har zuwa matsayin babban mataimakin sashen siyasar ƙungiyar, muƙamin da ya riƙe har zuwa Agustan 2024.
Al-Hayya, wanda a baya ya kasance jagoran ƙungiyar Hamas a ƙasashen waje, ana kallonsa cikin masu tsattsauran ra'ayi a Hamas, wanda ya fito fili a lokacin yaƙin Isra'ila da Hamas da ya fara kusan shekaru uku da suka gabata.
Ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin amintattun mutane na kusa ga tsohon shugaban Hamas, Yahya Sinwar, kuma an bayyana shi a matsayin "ɗaya daga cikin tsirarun mutanen da Sinwar yake ji da su."
Bayan kashe Yahya Sinwar a watan Oktoban 2024, an riƙa kallon Al Hayya a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda za su iya maye gurbinsa a shugabancin ƙungiyar.
Wace rawa ya taka a Hamas?
A matsayinsa na babban mai shiga tsakani a tattaunawar Hamas, al-Hayya ya samu karɓuwa a idon duniya ta hanyar jagorantar tawagogin ƙungiyar a tattaunawar tsagaita wuta, inda ya riƙa ganawa da masu shiga tsakani daga Masar da Qatar.
A baya-bayan nan ya kasance babban jami'in diplomasiyyar da tsare-tsare siyasar
A watan Nuwamban 2019, Al Hayya da Rouhi Mushtaha suka jagoranci wata tawaga daga Gaza, zuwa ƙasashe da dama, ciki har da Turkiyya da Lebanon.
Al Hayya ya kuma jagoranci tattaunawar sulhu da ƙungiyar Fatah.
A watan Janairun 2022, ya ziyarci Aljeriya bayan ya samu gayyata daga shugaban ƙasar Aljeriya.
Al Hayya ya wakilci Hamas a tattaunawar da aka yi da Isra'ila kan sakin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su da kuma tsagaita wuta.
Ya sha tsallake rijiya da baya
A watan Satumban 2025, Al-Hayya mai shekara 65 ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Isra'ila ta kai kan shugabannin Hamas da ke wani taro a Doha, babban birnin Qatar.
A lokacin harin an kashe mutum biyar ciki har da ɗansa, wanda mamba ne a rundunar tsaron Qatar.
A lokacin, Firaministan Isra'ila ya ce an kai musu harin ne saboda zarginsu da kitsa harin ranar 7 ga watan Oktoban 2023 a kudancin Isra'ila, wanda ya haifar da yaƙin Gaza.
Da fari an kashe wasu ƴaƴan Al-Hayya biyu a wani hari da aka kai da nufin halaka shi a Gaza, yayin da aka kashe ɗansa na huɗu a wani hari a Gaza cikin watan Mayun da ya gabata.
A 2007 ne wani harin Sira'ila kan gidansa ya kashe bakwai daga cikin ƴan'uwansa, ciki har da shaƙiƙansa biyu.
Haka ma a 2008 aka kashe ɗaya daga cikin ƴaƴansa a wani hari ta sama da aka kai masa.
Sannan a 2014 aka kashe wani ɗan nasa da surukarsa da kuma jikansa a wani hari ta sama kan gidansa a Gaza.