Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 22/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku bayani kan muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 22 ga watan Yuli, 2026.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Abdullahi Bello

  1. Kotu ta ɗaure mutumin da ya yi yunƙurin sace motar ƴansanda

    Kotu a Ghana ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 26 hukuncin ɗauri bayan kama shi da laifin yunƙurin satar motar ƴansanda.

    Matashin mai suna Ebenezer Frimpong ya shiga motar sulke ta ƴansanda ya har ya fara tafiya bayan direban motar ya fita domin sayen magani a wani kemis, a watan Afrilun wannan shekarar.

    Bireban motar, Joshua Denkyi ya ce matashin ya samu damar sace motar ne bayan ya tsaya sayen magani a lokacin da yake kan hanya.

    An kama matashin ne bayan an bi shi da gudu yayin da yake ƙoƙarin tserewa da motar, inda daga baya ƴansanda suka tsare shi.

    Alƙalin kotun ya buƙaci a yi wa matashin gwajin ƙwaƙwalwa domin tabbatar da cewa yana cikin hankalinsa.

    Ebenezer ya amsa laifinsa, lamarin da ya sa alƙalin ya yanke masa hukuncin ɗaurin wata ɗaya a gidan yari.

    Alƙalin ya ce ya yanke masa hukuncin wata ɗaya kacal ne saboda matashin ya amsa laifinsa kai tsaye ba tare da ɓata lokacin kotu ba.

  2. Nijar da Mali da Burkina Faso na son karɓar baƙuncin Afcon

    Ƙasashen Jamhuriyar Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun miƙa takardar haɗaka ta neman karɓar baƙuncin gasar ƙwallon ƙafa ta Afirka, Afcon a shekarar 2032.

    Jami'an ƙasashen sun gabatar da takardar buƙatar ne ga shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF), Patrice Motsepe.

    Shugabannin hukumomin kula da ƙwallon ƙafa na ƙasashen sun gana da Motsepe a birnin New York na Amurka a ranar Asabar, tare da Kanar Djibrilla Hima Hamidou, wakili a hukumar ƙwalllon ƙafa ta duniya FIFA, kuma ɗaya daga cikin manyan hukumar ƙwallon ƙafa ta Jamhuriyar Nijar.

    A ranar Talata ne hukumar ƙwallon ƙafa ta Mali (FEMAFOOT) ta sanar da ganawar da aka yi, inda ta ce za a yi amfani da gasar wajen bunƙasa "haɗin kai tsakanin ƙasashen yankin da kuma haɓɓaka ƙwallon ƙafa a Afirka."

    Miƙa takardar neman karɓar baƙuncin ta biyo bayan nuna sha'awar hakan da ƙasashen AES suka yi.

    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Mali ta ce za ta yi aiki tare da sauran ƙasashen biyu wajen yin "ingantaccen shirin karɓar gasar" wanda zai kawo sabon ci gaba a harkar ƙwallon ƙafa a nahiyar.

    Har yanzu hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka ba ta riga ta zaɓi ƙasar da za ta karɓi baƙuncin gasar ta 2032 ba, gasar da ake yi duk bayan shekara biyu, tana tattara zaƙaƙuran masu taka leda na nahiyar.

    A shekarun baya-bayan nan ne ƙasashen Mali da Nijar da Burkina Faso suka kafa ƙungiyar ƙasashen yankin Sahel ta AES bayan ficewa daga ƙungiyar haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (Ecowas), bayan jerin juyin mulki a ƙasashen.

    AES ta ce manufarta ita ce bunƙasa haɗn kai tsakanin ƙasashen uku, musamman a ɓangaren tsaro da kasuwanci da kuma tattalin arziƙi.

  3. 'Amurka da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar nukiliya'

    Kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito cewa gwamnatin Donald Trump ta cimma wata yarjejeniya da Saudiyya game da sarrafa makamashin nukiliya, kuma za a sanar da abin da yarjejeniyar ta ƙunsa nan ba da daɗewa ba.

    Yarjejeniyar za ta iya bai wa Saudiyya damar inganta makamashin yureniyom (Uranium) ta yadda za ta iya amfani da shi a rumbunan sarrafa makamashin nukiliya.

    Yarjejeniya kan makamashin nukiliya tsakanin ƙasashen duniya abu ne da ke haifar da muhawara a tsawon shekaru.

    Wasu daga cikin ƴan majalisar dokokin Amurka sun nuna damuwa kan cewa Saudiyya za ta iya yin amfani da damar wajen ƙera makaman ƙare-dangi.

    Wannan yarjejeniya za ta iya sake yauƙaƙa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu, wadda da alama ta fara rawa sanadiyyar yaƙin Iran - kuma hakan zai iya bai wa kamfanonin Amurka wata ƙarin dama.

  4. Muna da niyyar ci gaba da tattaunawa da Iran - Amurka

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce har yanzu Washington na da niyyar ci gaba da tattaunawa da Iran ta hanyar diflomasiyya, duk da cewa Amurkar ta kwashe dare na 11 a jere tana kai hare-hare a ƙasar.

    Da yake jawabi a taron ministocin harkokin wajen ƙasashen Kudu maso Gabashin nahiyar Asiya, Mr Rubio, ya zargi Iran da rashin nuna muhimmanci ga tattaunawar.

    Ya kuma sake jaddada cewa barin Iran ta mallaki ikon mashigar Hormuz, zai zama wani abin koyi mai haɗari ga ƙasashen duniya.

    A sabbin hare-haren da aka kai, rundunar sojin Amurka ta ce ta kai hare hare kan gine-gine da tashoshin gaɓar ruwa da kuma wuraren samar da kayan aiki na Iran.

    A nasa bangaren, kamfanin dillancin labaran Iran ya ce an kunna na'urar tsaron sararin samaniya a birnin Tehran, yayin da aka ji ƙarar fashe-fashe a birnin Tabriz da kuma Bushehr, inda tashar nukiliya guda ɗaya tilo ta Iran take.

  5. Shugaban Faransa ya goyi bayan dokar hana yara shiga shafukan sada zumunta

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya yaba wa ƙuri’ar da majalisar dokokin ƙasar ta kaɗa, wadda ta amince da hana yara ƴan ƙasa da shekara 15 amfani da kafafen sada zumunta.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa tare da wasu bidiyo da ke nuna matsalolin da matasa ke fuskanta, ciki har da cutar rashin cin abinci da sauran illolin amfani da kafafen sada zumunta, Macron ya ce Faransa ta ɗauki matakin ne a kan tafarki ma daidadi ci.

    Ya bayyana cewa ƙasar na jagorantar sauran ƙasashen Turai wajen kare matasa daga illolin da ke tattare da amfani da waɗannan kafafe.

    A ƙarƙashin dokar da Macron ya mara wa baya, kamfanonin da ke mallakar kafafen sada zumunta dole ne su samar da hanyoyin tabbatar da shekarun masu amfani da su.

    Haka kuma, dole ne makarantun sakandare su haramta amfani da wayoyin hannu a cikin makaranta.

    Daga watan Satumba, duk wanda zai buɗe sabon shafi a kafafen sada zumunta sai an tabbatar da shekarunsa, kuma duk wanda bai kai shekara 15 ba, ba za a ba shi damar buɗe shafi ba.

  6. Barka da warhaka!

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye a wannan rana ta Laraba - Tabawa ranar samu- inda muke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp domin samun labarai da ɗumi-ɗuminsu kuma ku yi shiyarin.

    Haka nan za ku iya tofa albarkacin bakinku a shafukan mu na facebook, instagram, X da kuma YouTube.