Arsenal ta sa Jesus a kasuwa, City ta dage kan Anderson

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal ta yi wa danwasanta na gaba Gabriel Jesus, dan Brazil mai shekara 29, farashin fam miliyan 20, ga duk kungiyar da ke son sayenshi a bazaran nan. (Athleti)

Manchester City na bayar da fifiko kan cinikin dan wasan tsakiya na Nottingham Forest da Ingila Elliot Anderson, mai shekara 23, yayin da take shirin fuskantar rayuwa bayan Pep Guardiola. (Mail)

Amma kuma City din ba ta da sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Chelsea Enzo Fernandez, na Argentina mai shekara 25, wanda ke son barin kungiyar ta Stamford Bridge. (Sky Sports)

RB Leipzig ta nuna cewa danwasanta na gaba na gefe Yan Diomande, na Ivory Coast mai shekara 19, wanda Liverpool, ke so ba inda za shi a bazaran nan, bayan da kungiyar ta amus ta samu gurbin zuwa gasar Zakarun Turai ta kaka mai zuwa. (Mirror)

Bayer Leverkusen na fatan shawo kan kociyan Bournemouth mai barin gado Andoni Iraola ya karbi aikin sabon mai horad da kungiyar. (Kicker)

Arsenal ta yi kyakkyawan shirin na cinikin danwasan tsakiya na Aston Villa Morgan Rogers na Ingila mai shekara 23. (Football Transfers)

Liverpool na son mai tsaron ragarta Alisson Becker dan Brazil mai shekara 33, ya ci gaba da zama a kungiyar karin kaka daya, wanda hakan ya sa rashin tabbas na shirin golan na tafiya Juventus a bazaran nan. (Gianluca Di Marzio)

Jami'ai daga Liverpool da Inter Milan sun gana a kan cinikin dan wasan tsakiya na Liverpool din Curtis Jones na Ingila mai shekara 25, kan tafiyarsa Italiya. (Gianluca Di Marzio)

A shirye Manchester City take ta saki dan wasanta na gaba na gefe Savinho, dan Brazil mai shekara 22, wanda kuma Tottenham ke sha'awarsa. (Football Insider)

Oscar Mingueza, mai shekara 27, yana son samun kungiya a Firimiya a bazaran nan, kuma, Aston Villa da Newcastle na daga kungiyoyin da suke bin diddigin dan bayan na Celta Vigo dan Sifaniya, wanda zai kasance ba shi da kwantiragin wata kungiya a kansa (Sky Sports)