Ƴan wasan da suka buga Gasar Kofin Duniya da za su iya sauya kungiya a wannan bazarar

Asalin hoton, Getty Images/BBC Sport
Yayin da ake kusan kammala Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, hankula na karkata zuwa kakar wasanni ta kasashen Turai da za a fara cikin watan Agusta kaka ta 2026-27.
A irin wannan lokacin ne kasuwar saye da sayar da ƴan ƙwallo ake ta hada-hada, inda ƙungiyoyi ke yin cefanen da za su kara karfin tunkarar kalubalen da za su fuskanta.
Tuni wasu manyan sunayen ƴan wasa daga Gasar Kofin Duniya suka amince da yarjejeniyoyin komawa sabbin kungiyoyi, ciki har da Marc Cucurella da Elliot Anderson da kuma Youri Tielemans.
Sai dai har yanzu akwai cinikayyar ƴan wasa da dama da ke sa ran za a kammala ɗauka nan gaba, ana kuma zawarcin wasu daga cikin ƴan wasan da suka nuna bajinta a babbar gasar tamaula ta duniya ta bana.
Ga jerin ƴan wasa tara da suka buga Gasar Kofin Duniya da za su iya sauya ƙungiya a wannan bazarar, da kuma inda ake son a saye su.
Bradley Barcola

Asalin hoton, Getty Images
Daya daga cikin ƴan wasan gaba masu hatsari a Faransa, sai ka haɗa da Barcola wanda ya haskaka a Gasar Kofin Duniya, harma ya yi fice a tawagar duk da kasancewa tana da hazikan ƴan ƙwallo irin su Kylian Mbappe da Michael Olise da kuma Ousmane Dembele.
Barcola ya buga dukkan wasa bakwai na Faransa, an fara huɗu da shi a cikin fili, kuma ya ci ƙwallo biyu, ɗaya a wasan farko da Senegal, daya kuma da Sweden a zagayen ƴan tawaga 32.
Ɗan wasan mai shekara 23 ya kuma yi nasarar a kakar wasan da ta wuce a matakin kungiya, inda ya lashe Champions League karo na biyu a jere tare da Paris St Germain, yayin da ya buga wasa 49 a dukkan fafatawa.
Sai dai ba kasafai ake fara wasa da shi ba a PSG ba, har sai idan an samu matsala daga Khvicha Kvaratskhelia sai ya maye gurbinsa a ƙungiyar da Luis Enrique ke jan ragama.
Ana danganta ɗan wasan da manyan ƙungiyoyin Premier League, inda Liverpool da Arsenal duka ke nuna sha'awar ɗaukarsa.
Ayyoub Bouaddi

Asalin hoton, Getty Images
Bouaddi mai shekara 18 ya ja hankali a wannan bazarar, yayin da yake jagorantar wasan tsakiya a tawagar Morocco da ta kai wasan kusa da na kusa da karshe.
Bouaddi na sarrafa wasa ta hanyar da ta saɓawa karancin shekarunsa, domin sai wanda ya manyanta ya kamata da ƙwarewarsa, kuma ya burge a wasan da suka yi da Brazil, wanda ya haskaka fiye da Casemiro da Bruno Guimaraes.
Ana sa ran ƙungiyarsa ta Lille za ta dakile tayin sayensa daga ƙungiyoyi da yawa a wannan bazarar, domin yana daga cikin fitattun ƴan ƙwallon da ta dogara da su.
Chelsea, wadda ta sayar da ɗan wasanta na tsakiya Andrey Santos zuwa Manchester United, ita aka cewa za ta sayi matashin, haka kuma Manchester City da Arsenal da Real Madrid da Barcelona da kuma Paris St-Germain za suyi rige-rigen sayen ɗan wasan..
Yan Diomande

Asalin hoton, Getty Images
Yana da shekara 19 kacal, Diomande ya haskaka sosai a Gasar Cin Kofin Duniya ta bana, amma na dan lokaci, saboda an fitar da Ivory Coast a zagayen ƴan wasa 32 bayan shan kashi a hannun Norway.
Diomande na daga cikin fitattun ƴan wasa a matakin rukuni da ya taimaka wa Ivory Coast kaiwa matakin zagaye na biyu a karon farko a tarihi.
An zabe shi gwarzon ɗan wasa a nasarar da Ivory Coast ta samu a kan Ecuador a wasan farko cikin rukuni, sannan ya sake burgewa a karawa da Jamus duk da shan kashi da suka yi.
Liverpool ta daɗe tana sha'awar sayen ɗan wasan RB Leipzig, wanda zai iya taka leda a bangaren hagu da dama, kuma yana iya amfani da kafafunsa biyu sosai.
Sai dai bayan da Liverpool da ta kasa cimma bukatar Leipzig ta kusan fam miliyan 100, an ce PSG da Manchester United duka suna sha'awa ɗaukarsa, sai dai wasu na cewar ya fi son komawa Faransa da taka leda
Djed Spence

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan mai tsaron bayan tawagar Ingila, Spence ya yi kokari sosai a Gasar Kofin Duniya wanda ya buga guraben tsaron baya, saboda matsalar da kasar ta samu na raunuka da jan kati daga masu tsaron bayanta.
Koda yake an soki Spence kan yadda ya taka leda a wasan DR Congo a zagayen tawaga 32, amma dakatarwar da aka yi wa Jarell Quansah ta sa ya koma cikin ƴan wasan farko 11 na Ingila.
Ya yi fice a wasannin da ya fuskanci Norway da kuma Argentina, kuma kokarinsa na kai hari, aiki tukuru da kyakkyawan hali sun sa ake danganta shi da barin Tottenham, wadda ke cikin sauye-sauye da yawa a karkashin sabon koci Roberto de Zerbi.
Liverpool da Everton da Inter Milan suna daga cikin ƙungiyoyin da ake dangantawa da tsohon ɗan wasan Middlesbrough.
John Stones

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan mai tsaron baya daga tsakiya, Stones ya kafa ɗan karamin tarihi
cewar shi ne ya na farko a Ingila da ya wakilci kasar a Gasar Cin Kofin duniya ba tare da yana da yarjejeniya da wata ƙungiyar.
Lokacin da za a fara buga gasar kofin duniya, yarjejeniyarsa ta kare da Manchester City, wanda ke neman wata ƙungiyar da zai koma a wannan bazarar.
Manyan ƙungiyoyin Italiya wato Juventus da zakarun Serie A, Inter suna sha'awar sayen Stones, yayin da Leeds United ke fatan Stone ɗin zai buga mata wasannin kakar bana.
Antonee Robinson

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan mai tsaron baya daga hagu na Fulham, Robinson ya kasance fitattun ƴan wasan tawagar Amurka da take ɗaya daga cikin da suka karɓi bakuncin Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, inda suka kai zagayen ƴan 16.
Robinson ya buga wasa hudu daga cikin biyar da Amurka ta yi, inda kawai aka huta da shi a wasan rukuni a karawa da Turkiyya, sannan ya buga cikakken minti 90 a uku daga sauran
Wannan ya biyo bayan kokarin da ya yi a kakar da ta wuce a Fulham a gasar Premier League, ana kuma alakanta shi da komawa Manchester United.
Julian Alvarez

Asalin hoton, Getty Images
Ɗaya daga cikin ƴan wasan gaba da suka taimaka wa Argentina ta doke Ingila a wasan kusa da karshe, Alvarez yana da hazaka sosai a Atletico Madrid tun bayan komawarsa daga Manchester City a 2024.
Atletico ba ta son sayar da ɗan wasan mai shekara 26, wanda ya ci ƙwallo 25 a wasa 66 a gasar lig ta Sifaniya, kuma tuni ta yi watsi da tayin da Barcelona ta yi.
Amma hakan ba zai hana manyan ƙungiyoyin Turai kokarin sayen gogaggen ɗan wasan ba, kuma ana alakanta zakarun Premier League, Arsenal da cewa suna kokarin ɗaukarsa.
Kuma Alvarez ɗan wasan tawagar Argentina yana son barin Atletico Madrid.
Mikel Oyarzabal

Asalin hoton, Getty Images
Kafin Gasar Cin Kofin Duniya, wasu na kallon ɗan wasan gaban mai shekara 29 a matsayin bai kai gogewar sauran ƴan wasan gaban tawagar Sifaniya ba, amma sai gashi yanzu shine kan gaba a cin ƙwallaye, saboda ƙwazon da ya saka.
Oyarzabal ya ci ƙwallo biyar zuwa yanzu a gasar cin kofin duniya, kuma mai yiwuwa ya kara wasu a wasan karshe da Argentina ranar Lahadi.
Rahotanni sun ce yana da ƙunshin yarjejeniyar kusan fam miliyan 65 a Real Sociedad, yayin da ake cewa Arsenal da Barcelona da Juventus suna sha'awarsa sayen ɗan ƙwallon..
Zion Suzuki

Asalin hoton, Getty Images
Japan ta yi takaici da yadda ta kammala buga Gasar Kofin Duniyarta a zagayen ƴan wasa 32, duk da cewa ta kasance ɗaya daga cikin tawagar da suka burge a farkon gasar.
Mai tsaron raga, Suzuki ya taka rawar gani sosai.
Duk da sun yi rashin nasara a karin lokaci a hannun Brazil, hana wata ƙwallo shiga raga da ya sa yatsun hannunsa daga bugun da Vinicius Junior ya yi, za a daɗe ana tunawa da shi a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun hana ƙwallo ya shiga raga.
Newcastle ta sanya ido kan mai tsaron ragar Parma, ko da yake ana cewa James Trafford na Ingila shi ne wanda take da buri, yayin da Leeds ita ma ake danganta da mai tsaron ragar.










