Bayern Munich na son ta tsawaita kwantaragin Kane,Chelsea na nazari kan Alonso da Silva

Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan Ingila Liam Delap,mai shekara 23, ya na son ya ci gaba da taka leda a Chelsea ya yin da kungiyar ke shirin yanke shawara kan 'yan wasanta masu kai hari (Telegraph - subscription required), external

Barcelona ta fara tuntubar Atletico Madrid domin sanin matsayin kungiyar game da yiwuwar siyan dan wasan Argentina Julian Alvarez, mai shekara 16, a bazara. (ESPN), external

Akwai rashin tabbass game da makomar Scott Parker a matsayin kocin Burnley sakamakon faduwar da kungiyar ta yi a gasar firimiya kuma tsohon kocin Rangers da Aston Villa Steven Gerrard, mai shekara 45, na iya kasancewa cikin wadanda za a dauka don maye gurbin kocin mai shekaru 45.(Talksport), external

Ita ma Bristol na zawarcin Gerrard, wanda ya bar kungiyar Al-Ettifaq ta Saudi Arabiya bisa amincewar juna bayan ya shafe watanni 18 yana horar da 'yan wasan kungiyar tun shekarar 2025. (Independent), external

Borussia Dortmund na gab da kulla yarjejeniyar sake siyan dan wasan Ingila Jadon Sancho a wannan bazarar amma Aston Villa na fatan za su amince da siyan dan wasan mai shekara 26 idan kwantaraginsa ya zo karshe a watan Yuli.(Teamtalk), external

Liverpool za ta iya rasa dan wasan Ivory Coast Yan Diomande saboda mai yiwuwa dan wasan mai shekaru 19 ya ci gaba da zama a RB Leipzig har na akalla shekara guda.(Christian Falk via CFBayerninsider), external

Chelsea ta saka sunan tsohon kocin Real Madrid Xabi Alonso, mai shekara 44, da kocin Fulham Marco Silva, mai shekaru 48, a cikin jerin sunayen wadanda za ta dauka aiki a matsayin sabon kocinta (Sun), external

Bayern Munich za ta fara tattaunawa da dan wasan gaban Ingila Harry Kane a karshen kakar wasa ta bana, yayin da zakarun Jamus ke neman tsawaita zaman dan wasan mai shekaru 32 har zuwa 2027.(Mirror), external

AC Milan da Bayern Munich na son dan wasan Sabiya, Dusan Vlahovic idan dan wasan mai shekara 26 be sabunta kwantaraginsa da Juventus a wannan bazara ba .(Sky Sports), external