Wace ƙungiya ce ta fi yawan ƴanwasa da za su buga kofin duniya a 2026?

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City tana da ƴan wasa 19 da za su wakilci kasashensu a gasar cin kofin duniya 2026 da za a buga a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Daga cikin waɗannan ƴan ƙwallon, huɗu suna daga cikin tawagar Ingila da suka haɗa da mai tsaron raga, James Trafford da mai tsaron baya, Marc Guehi da Nico O'Reilly da kuma John Stones da koci, Thomas Tuchel ke fatan za su taka rawar gani.
Kamar yadda John Stones zai bar Etihad bayan kammala kakar bana, haka shima ƙyaftin ɗin City, Bernardo Silva wanda ya lashe kofuna a ƙungiyar yana kuma ɗaya daga cikin ƴan wasan uku da za su yi wa tawagar Portugal gasar cin kofin duniya tare da Ruben Dias da kuma Matheus Nunes.
Haka kuma Netherlands da Croatia kowacce tana da ƴan ƙwallon City biyu a cikin tawagarta. Tijjani Reijnders da Nathan Aké suna cikin tawagar Netherlands, yayin da Mateo Kovačić da kuma Joško Gvardiol ke wakiltar Croatia.
Sauran ƴan wasan City da za su halarci gasar sun haɗa da Erling Haaland a Norway da Omar Marmoush a Masar da Rayan Cherki a Faransa da Jérémy Doku a Belgium da Rodri a Sifaniya da Rayan Aït-Nouri a Aljeriya da Antoine Semenyo a Ghana da kuma Abdukodir Khusanov da zai buga wa Uzbekistan gasar kofin duniya 2026.
Ba wai kawai City ce mafi yawan ƴan wasa daga kowace ƙungiya a Ingila ba, har ma ya sa Manchester City ta zama wadda ta fi yawan wakilai a gasar daga cikin dukkan ƙungiyoyin duniya.
Sai dai kuma daga cikin waɗan nan ƙididdige ba a haɗa da ƴan wasan da suka buga wasannin aro ba a kakar da aka karkare.
Akwai ƙungiya 17 da take da ƴan ƙwallo 10 ko fiye da haka da za su buga gasar kofin duniya, kuma biyar daga cikinsu daga Ingila suke masu buga Premier League.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Arsenal tana matsayi na uku tare da Paris Saint-Germain, inda kowacce take da ƴan wasa 17 da za su wakilce su a Amurka da Canada da kuma Mexico. PSG ce ta doke Arsenal a wasan ƙarshe ta kuma lashe Champions League.
Wadda ta lashe Bundesliga, Bayern Munich, tana matsayi na biyu da ƴan wasa 18 biye da Man City, yayin da wadda ta ɗauki kofin La Liga na bana, Barcelona take da ƴan wasa 15, waɗanda sune kaɗai aka samu daga manyan gasar Turai biyar, watp Premier League da La Liga da Bundesliga da Serie A da kuma Ligue 1.
A gasar Kofin Duniya ta ƙarshe da aka yi a Qatar a 2022, Barcelona ce ta fi kowace ƙungiya yawan wakilai da mai ƴan ƙwallo 17, yayin da Manchester City da Bayern Munich suka zo na biyu da 16 kowacce.
A gasar da aka yi a Rasha a 2018, Manchester City ce ta jagoranci yawan wakilai mai ƴan wasa 16, Real Madrid ta zo ta biyu da 15, sannan Barcelona ta uku da 14.
Adadin ƴan wasa 17 da suka buga gasar kofin duniya a Qatar daga Barcelona ya sa ta kafa sabon tarihi a lokacin, amma yanzu Manchester City ta karya wannan tarihi a bana da ƴan ƙwallo 19, kuma hakan ya biyo bayan da aka faɗaɗa gasar daga 32 zuwa 48 ne za su kece raini a bana.
Send us your questions













