PSG ta shiga jerin manya bayan lashe Champions League na biyu a jere

Paris St-Germain manager Luis Enrique smiling with the Champions League trophy

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Luis Enrique ya zama koci na biyar da ya lashe Champions League uku a tarihi
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Paris Saint-Germain ta tabbatar da matsayinta ta ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Turai, bayan da ta yi nasarar lashe Champions League na biyu a jere-sakamakon nasara 4-3 a bugun fenariti a kan Arsenal, bayan tashi 1-1 a wasan ƙarshe da aka buga a Budapest.

Wannan nasara ta zo ne bayan da ta lallasa Inter Milan da ci 5-0 a Munich a shekarar da ta gabata.

Da wannan, PSG ta zama ƙungiya ta farko da ta kare kambunta tun bayan Real Madrid wadda ta yi hakan sau uku a jere tsakanin 2016 zuwa 2018, kuma ita ce ƙungiya ta biyu kacal da ta yi hakan a zamanin Champions League (daga 1993 zuwa yanzu).

A tarihin gasar da ta kai shekara 71, PSG ta zama ƙungiya ta 10 kacal da ta lashe kofin a jere.

Dukkan ƴan wasan ciki fili su 10 da suka fara wasan karshe da Arsenal, su ne dai suka fuskanci Inter Milan, sai dai kawai canji shi ne mai tsaron raga Matvey Safonov wanda ya maye gurbin Gianluigi Donnarumma, wanda ya koma Manchester City a bazarar da ta gabata.

A cikin shekaru biyu da suka wuce, ƙungiyar Luis Enrique ta mamaye kusan dukkan gasar da ta shiga. Tun farkon kakar da ta gabata, sun lashe kofuna 8 daga cikin 10 da ake takara a kansu, inda suka rasa kawai Gasar Club World Cup ta bazara da kuma Kofin Faransa na wannan kakar.

Idan suka ci gaba da wannan salon nasara, PSG za ta iya zama ƙungiya ta biyar a tarihi da ta lashe Champions League sau uku a jere. Amma har yanzu tana da hanya mai tsawo idan aka kwatanta da bajintar Real Madrid na lashe kofin Turai sau biyar a jere tsakanin 1956 zuwa 1960.

Yanzu PSG na kafaɗa da manyan ƙungiyoyin Turai

Dan jaridar ESPN, Laurens, ya ce nasarar PSG ta biyu a gasar UEFA Champions League ta sanya ta a wani sabon matsayi na musamman a tarihin ƙwallon ƙafa a Turai.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ta kuma zama ƙungiyar da ta fi kowa zura ƙwallaye a gasar bana da guda 45, tare da samun mafi girman kaso na mallakar ƙwallo da kashi 60.5%.

Laurens ya shaida wa BBC Radio 5 Live cewa:

"Yanzu PSG tana cikin manyan ƙungiyoyin da suka kafa tarihi. Pep Guardiola bai taɓa kare kofin Champions League a jere ba tare da Lionel Messi a Barcelona ko kuma tare da Manchester City ba.

Lashe kofi guda ɗaya babban abu ne, amma ka ɗauka sau biyu a jere wani mataki ne daban gaba ɗaya."

PSG ta buga wasan ƙarshe a Champions League karo na uku a tarihinta. Na farko ya kasance a kakar 2019-20 lokacin da suka sha kashi 1-0 a hannun Bayern Munich a Portugal.

Sai dai da wannan nasarar ta biyu, PSG ta zama daga Faransa mafi nasara a tarihin gasar, inda ta zarce Marseille, wadda ke da kofin Champions League guda ɗaya kacal.

Yanzu Paris Saint-Germain ta kafa bajintar kanta a matsayin mafi girma daga Faransa a tarihin gasar zakarun Turai, tare da nuna cewa nasarar shekarar da ta gabata ba ta kasance ta sa'a ba, illa sakamakon gagarumin aiki da tsarin da Luis Enrique ya gina.

The Paris St-Germain fans unveiling a tifo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Magoya bayan Paris Saint-Germain sun nuna wata babbar tuta ta musamman (tifo) kafin fara wasan, wadda ke nuna cewa ba su da niyyar miƙa kofin Champions League da suke riƙe da shi cikin sauƙi.

Tun farko Luis Enrique bai yi niyyar karɓar aikin PSG ba

Kocin PSG, Luis Enrique, ya shiga jerin manyan masu horarwa kamar Bob Paisley, Pep Guardiola, Carlo Ancelotti da Zinedine Zidane, inda ya zama na biyar da ya lashe kofin UEFA Champions League sau uku a tarihi.

Ɗan ƙasar Sipaniya, wanda aka naɗa kocin PSG a watan Yuli 2023, ya kuma taɓa lashe Champions League a matsayin ɗan wasa tare da Barcelona a kakar 2014–15.

A cewar ɗan jarida Guillem Balagué, Luis Enrique da farko bai nuna sha'awar karɓar aikin PSG ba, inda ya ce ƙungiyar "ta cika da taurari" kuma ba ya sha'awar hakan. Amma daga baya aka yi masa bayani cewa ba kawai batun lashe Champions League ba ne, sai dai gina sabuwar al'ada da salon wasa mai kai hari da nishaɗi.

A ƙarƙashin jagorancinsa, PSG sun rasa Kylian Mbappé zuwa Real Madrid a 2024, amma hakan ya taimaka wajen daidaita salon wasan ƙungiyar. A kakar farko ba tare da Mbappé ba, PSG sun zura ƙwallaye 44 fiye da kakarsa ta ƙarshe a ƙungiyar.

Balagué ya bayyana cewa yanzu "dukkan 'yan wasa suna taka leda a matsayin ƙungiya ɗaya," inda PSG suka zama ɗaya da ke da ƙarancin katunan gargadi a manyan lig-lig na Turai, alamar nutsuwa da haɗin kai da kuma ladabi.

Luis Enrique ya kuma yi imanin cewa ya fi ƙyau a samu ƴan wasa biyar suna zura ƙwallaye 10-10 fiye da guda ɗaya mai zura 50 a kaka ɗaya. A wannan kakar, PSG suna da sama da ƴan wasa 20 daban-daban da suka zura ƙwallaye.

Har ila yau, ya gina ƙyaƙƙyawar alaƙa da magoya bayan PSG, musamman bayan nasarar Champions League, inda aka yi masa tarbar girmamawa da tutoci da kuma yabo saboda tarihin kansa da kuma ƴarsa Xana, wadda ta rasu tana da shekara tara.

A yanzu, Luis Enrique yana jin daɗin goyon bayan magoya baya yayin da PSG ke ci gaba da zama ƙungiya mai haɗin kai da salo mai jan hankali.

Luis Enrique banner

Asalin hoton, Getty Images