Me Atiku ke nufi da ba zai sake yin takara ba bayan 2027?

Lokacin karatu: Minti 4

Ƴan Najeriya na ta shaci faɗi da kokwanta haƙikanin abin da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya faɗi dangane da burinsa na neman shugabancin Najeriya, inda ya ce ba zai sake takara ba bayan wadda zai yi a 2027.

Atiku Abubakar ya shaida hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talbijin na Arise ranar Laraba.

Ɗan jaridar ya tambayi Atiku cewa yanzu shekarunsa sun kai 80 da alama wannan ce takararsa ta ƙarshe kasancewa shekarun nasa sun ja, sai tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya ce "E wannan haka yake. Babu ja a ciki."

Wannan ya sa BBC ta tuntuɓi masana dangane da abin da kalaman nasa ke nufi a daidai lokacin da wasu ƴan siyasa suke sa ran Atikun zai goya musu baya su yi takara a 2027.

Ma'ana uku daga kalaman Atiku

Malam Kabiru Sufi, masanain kimiyyar siyasa kuma malami a kwalejin share fagen shiga jami'a, CAS da ke Kano ya ce tsohon shugaban Najeriya ya aike da gamagarin saƙo ne.

"Na ɗaya ya aike da saƙo ga abokan takararsa na siyasa cewa yana buƙatar su ba shi wannan dama duba da cewa wasunsu suna da sauran lokaci na damar da za su yi takara a nan gaba kuma zai iya goya musu baya....saboda idan suka goya masa baya a yanzu to shi ma nan gaba zai goya musu baya.

"Sannan ya miƙa saƙo ga ƴan ƙasa musamman na kudancin Najeriya a kan cewa bayan shekarun hudun mulkinsa zai iya haƙura tunda a wannan lokacin ya kai shekaru 84 kenan saboda haka akwai yiwuwar mulkin ya koma kudanci," in ji Kabiru Sufi.

"Sannan kuma akwai saƙon da yake aikawa gam-garin al'umma musamman cewa shi ɗan dimokraɗiyya ne kuma mutum ne da ya yadda cewa akwai lokaci saboda haka yana ganin lokacin da zai shekaru 84 lokaci ne da za a koma a zama masu bayar da shawara ga ƙasa ba wai mutum ne da zai hau mulki ya maƙale duk da shekaru sun cimma sa ba,"

Yawan takarar shugaban ƙasar da Atiku ya yi

Ya zuwa 2023, karo uku Atiku Abubakar ke tsayawa takarar shugaban ƙasa, ko da yake ya tsaya zaben fitar da gwani sau uku.

A shekarar 2007, jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) ta tsayar da shi takara inda ya sha kaye a hannun dan takarar PDP, Umaru Musa Yar'adua.

Kazalika a shekarar 2019 ya fafata da Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC amma bai yi nasara ba.

Sai kuma a 2023 da PDP ta sake tsayar da shi takara domin fafatawa a zaben da ya bai wa Bola Tinubu nasara.

Idan har Atiku Abubakar zai sake tsayawa takarar a 2027, zai zama karo na huɗu kenan da zai tsaya a babban zaɓe sannan kuma karo na bakwai a zaɓen cikin gida na jam'iyya.

Atiku Abubakar ya tsunduma harkokin sisaya a 1989, kuma yana cikin makusantan tsohon mataimakin shugaban kasa na mulkin soji, Janar Shehu Musa Yar'adua.

Ya shiga jam'iyyu daban-daban tun da ya shiga harkokin siyasa.

An zabi Atiku Abubakar a matsayin gwamnan Jihar Adamawa a 1998, ko da yake daga bisani Cif Obasanjo ya zabe shi domin kasancewa mataimakinsa.

Ko Obi da Kwankwaso za su kawo wa Atiku cikas wajen samun takara a ADC?

Masana da dama na ganin cewa mutanen guda biyu Peter Obi da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso na da ƙwarin gwiwa cewa suna da yawan mabiya saboda haka za su iya kai bantansu idan jam'iyya ta ba su dama.

Peter Obi

Ɗan takarar shugabancin Najeriya a 2023 a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya tabbatar da cewa zai yi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC, inda ya yi watsi da yiwuwar zama mataimakin Atiku Abubakar.

Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talbijin na Channels.

"Zan tsaya takarar shugaban ƙasar jamhuriyar Najeriya, kuma na yi imani ina da cancantar yin hakan." In ji Obi.

"..Babu wanda ya taɓa tattauna batun (kasancewa mataimakin Atiku Abubakar). Mutane suna tsammanin abubuwa da yawa. Babu mutumin da ya taɓa magana da ni akan wannan cewa ko zan zama kaza ko kaza".

Peter Obi ya sha nanata aniyarsa na yin wa'adi ɗaya na shekaru huɗu a matsayin shugaban Najeriya idan aka zaɓe shi a 2027.

A shafinsa na X, Peter Obi ya ce idan ya samu nasarar zama shugaban ƙasar, wa'adi ɗaya na shekara huɗu kawai zai yi kamar yadda ya yi alƙawari.

"Ko tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln wa'adi ɗaya ya yi na shekara huɗu, sannan John F. Kennedy bai ma ƙarasa wa'adi ɗaya ba, amma ana ci gaba da tunawa da su a matsayin shugabanni masu adalci."

Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kanon, Rabi'u Musa Kwankwaso na ɗaya daga cikin ƴan siyasa a arewacin Najeriya da suka daɗe suna tasiri, musamman saboda yadda ya shiga zuciyar matasa.

Ana dai ganin tun bayan Malam Aminu Kano ba a sake samun wani ɗan siyasa ba da ya fito da wani tsari na siyasa a arewa da ya saka wa suna, kuma yake da mabiya na ga-ni-kashe-ni, sai Kwankwason.

Kwankwaso ne jagoran aƙidar siyasa mai suna ɗarikar Kwankwasiyya da mabiyanta ke saka jar hula.

A baya, Kwankwaso ya yi takarar cikin gida da Atiku Abubakar.