Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda matashi ya yanki yatsansa don kai wa 'boka' kan miliyan 80 a Kano
Wani lamari mai ban mamaki da ya jawo ce-ce-ku-ce a Kano ya kai ga cafke mutane huɗu bayan zargin wani matashi da yanke yatsarsa don kai wa boka, bisa alƙawarin samun kuɗi har naira miliyan 80.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce bincikenta ya gano cewa matashin ya aikata hakan ne bayan an yi masa alƙawarin samun ɗimbin kuɗi, amma daga bisani ya ce bai samu kuɗin da aka yi masa alƙawari ba.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa BBC yadda lamarin ya faru, yana mai cewa bincike ya kai ga gano wasu da ake zargin suna da hannu a wannan al'amari.
A yayin binciken, matashin da ake zargi da kuma bokan sun yi bayani kan abin da suka ce ya faru, inda kowannensu ya bayyana nasa ɓangaren labarin dangane da zargin da ake yi.
Yadda Lamarin ya faru
CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce wani matashi mai suna Yusuf Mahmuda, mai shekara 27 ne ya shigar da ƙorafi, cewa wani mutum ya buƙaci ya nemo masa yatsar mutum mai rai, kuma zai biya naira miliyan 80.
''Mutumin ya ce bayan ya zagaya, ya faki mutane da dama bai samu ba, sai ya yanke shawarar yanke yatsarsa tun da dai yatsar mutum mai rai ake buƙata'', in ji CSP Kiyawa.
Sai dai mutumin ya ce bayan ya kai yatsar mutumin ya fara ka mi masa wala-wala, inda daga ƙarshe ya hana shi kuɗin.
Lamarin da ya sa matashin ya shigar da ƙorafi a ofishin ƴansanda.
'Abin da ya na kai ƙara'
Matashin wanda ya yanke yatsarsa ya ce ya shigar da ƙara ne saboda an kasa cika masa alƙawarin da aka yi masa tun farko.
''Ya bani cigiyar nemo ɗan yatsar mutum mai rai a kan naira miliyan 70 zuwa miliyan 80, shi ne ni kuma da ban samu na yanke nawa na kai masa'', in ji matashin.
Matashin mai shekara 27 ya ce ya yanki ƙaramar yatsarsa ta hannun hagu domin cika wannan cigiya da aka ba shi.
''Amma da na kai masa bai ba ni kuɗin ba. Na sani abin da na yi ba daidai ba ne'', in ji shi.
'Ni ma wani ya bani cigiya'
Mutumin da ya buƙaci Yusuf ya samo yatsar ya shaida wa ƴansanda cewa shi ma wani ne ya saka shi aikin amma da ya ga ba zai iya ba, sai ya nemi wani.
''Lallai ni na ba shi cigiya, saboda ni ma wani ne ya buƙaci na samo masa amma na ga ba zan iya ba'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa bayan na faɗa masa ya ce min nawa za a bayar, sai ya ce masa miliyan 80, nan kuwa ya ce zai iya.
''Shi ne da ya je bai samu ba ya yanko tasa yatsar, ni kuma na kai wa wanda ya buƙaci na kawo, amma kuma ba samu kuɗin ba'', in ji shi.
'Ba yatsa na buƙaci ya kawo min ba'
Shi kuwa aihinin wanda ya buƙaci yatsar domin samun kuɗin ya ce ɗaya daga cikin matasan ne same shi da nufin neman kuɗin auren yarsa.
''Amma kuma ƙashin mutum na buƙata a wajensa ba yatsa ba, za mu yi amfani da shi don samun kuɗin da ya buƙata'', in ji shi.
Ya bayyana wa ƴansanda cewa shi ba boka ba ne, kuma ya yi hakan ne kawai domin smaun kuɗi.
Kakakin ƴansandan ya ce tuni rundunar ƴansanda ta kama mutum huɗu bisa zargi hannu a faruwar wannan lamari.
''Tuni an kammala bincike kuma a yau 9 ga watan Satumban 2026 an gurfanar da mutanen gaban kotun shari'ar Musulunci da ke Jogana a ƙaramar hukumar Gezawa da ke jihar Kano'', in ji CSP Kiyawa.