Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ƴandaba suka hana Peter Obi shiga garinsu a jihar Benue
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya fito ya bayyana cewa an hana shi shiga wasu al'ummomin da ya yi niyyar ziyarta a jihar Benue.
Obi ya ce wasu matasa tare da jami'an tsaro sun tare shi da tawagarsa, suna gaya musu cewa ba a son ganinsu a jihar.
Obi ya isa Makurdi, babban birnin jihar Benue, domin ya kai ziyara wasu al'ummomin da suka fuskanci hare-hare da tashe-tashen hankula, amma bai samu shiga ba.
Ya kuma ƙara da cewa mutanen da suka tare shi sun kai hari kan ayarin motocinsa a ranar Talata yayin da yake ƙoƙarin isa wasu yankunan jihar.
Martanin Peter Obi
Obi ya ce manufar tafiyarsa zuwa Benue ita ce domin ya ziyarci wuraren da 'yan bindiga suka kai hare-hare a kwanakin baya.
"Abin takaici ne ƙwarai. Mun isa Benue da safiyar yau. A hanyarmu ta zuwa ƙauyen Yelwata domin jajanta wa mutanen da hare-haren suka shafa, na ji ya dace in ziyarce su, kamar yadda muka fara yi tun lokacin yaƙin neman zaɓenmu, domin nuna girmamawa da goyon baya gare su."
"Sai dai da muka isa Makurdi da safiyar yau, wasu 'yan daba suka tare ni suna ihun 'Peter Obi ka koma baya'. A lokacin ne na fara tambayar kaina ko har yanzu ina Najeriya ne," in ji Obi.
A cewarsa, bai kamata jami'an tsaro su yi biris da wannan barazana ba, sai sun tabbatar da an hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin.
"A matsayina na ɗan takarar shugaban ƙasa, ina son ziyartar al'ummomi daban-daban da ganawa da jama'a, shi ya sa nake nan a yau. Ba ma son tayar da rikici ko saka rayuwar mutane cikin haɗari, saboda haka muka yi komai cikin lumana. Ina kira ga jami'an tsaro su binciki wannan batu tare da tabbatar da gwamnonin jihohi sun kiyaye doka da oda."
"Abin baƙin ciki ne matuƙa ganin irin wannan nuna ƙiyayya. Ban zo Benue saboda siyasa ba, na zo ne domin yin alhini tare da jama'armu, sauraren iyalan da suka rasa 'yan uwansu, da kuma yi musu ta'aziyya a wannan lokaci na jimami."
Martanin Rabi'u Kwankwaso
Shi ma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa kuma abokin takarar Obi, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana harin da aka kai wa Obi a Benue a matsayin "rana mai duhu ga dimokuraɗiyyarmu."
Kwankwaso, cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata da rana, ya ce duk wani ɗan Najeriya yana da 'yancin zirga-zirga a ko'ina cikin ƙasar.
"Dole ne mahukunta su tuna cewa Kundin Tsarin Mulki ya bai wa kowane ɗan ƙasa 'yancin motsi da zirga-zirga. Wannan haƙƙin ya fi dacewa ga Mista Obi, wanda tsohon gwamna ne kuma jagoran babbar 'yan adawa," in ji Kwankwaso.
Ya ƙara da cewa ya kamata gwamnatin jihar Benue ta gano waɗanda suka shirya harin, ta gurfanar da su gaban kuliya, sannan ta tabbatar da cewa ɗan takarar NDC da tawagarsa suna iya zirga-zirga cikin walwala a jihar.
A wani ɓangaren kuma, Ƙungiyar Obidient Movement ta fitar da sanarwa tana Allah-wadai da harin da kuma hana Obi motsi cikin 'yanci a jihar Benue.
Ƙungiyar ta ce waɗanda ake zargi da zama 'yan daba sun tare hanyar Gboko Road kusa da filin jirgin saman Makurdi, lamarin da ya haddasa cunkoson ababen hawa domin hana Obi ci gaba da ziyarce-ziyarcensa a faɗin jihar.
Obi bai sanar da mu ziyararsa ba - gwamnatin Benue
A gefe guda kuma, Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Benue, Solomon Iorpev, ya shaida wa kafafen yaɗa labarai na cikin gida cewa ziyarar da Peter Obi ya kai jihar ya kamata ta bi ƙa'idojin da suka dace.
Kwamishinan, wanda ke mayar da martani kan cece-kucen da suka biyo bayan hana Obi motsi a cikin jihar, ya ce gwamnati ba ta san waɗanda suka tare shi ba. Sai dai ya jaddada cewa ya kamata Obi ya sanar da gwamnatin jihar kafin zuwansa.
Ya ce, la'akari da matsayin Peter Obi, bai kamata ya riƙa zirga-zirga a jihar ba tare da bin ƙa'idojin tsaro da suka dace ba.
A cewarsa, Obi mutum ne mai muhimmanci, kasancewarsa tsohon gwamna kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, don haka nauyin samar masa da tsaro yana kan gwamnatin jihar.
"Mutum mai muhimmanci kamar tsohon gwamna yana shigowa jihar; ya kamata ya rubuta wa gwamnatin jihar wasiƙa."
"Mu ne ya kamata mu tabbatar da tsaronsa da kariyarsa. Amma idan ba a rubuto mana wasiƙar sanarwa ba, ba za mu iya tabbatar da tsaronsa ba," in ji kwamishinan.
Kwamishinan ya kuma ce zuwan Peter Obi jihar Benue ya zo ne a daidai lokacin da matasa daga ƙananan hukumomi 23 na jihar ke gudanar da wani taro. Saboda haka, gwamnatin ba ta san waɗanda ke da hannu a harin da ake zargi ba.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Benue ta yi fatali da zargin da ɗan takarar NDC, Peter Obi, ya yi cewa wasu 'yan daba masu alaƙa da gwamnatin jihar sun tare shi tare da kai masa hari yayin ziyararsa.
A cikin wata sanarwa da Tersoo Kula, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna, ya fitar a madadin gwamnatin jihar, ya ce lamarin na iya kasancewa wata rigima ta cikin gida a jam'iyyar NDC.
Ya ce Gwamnan Jihar Benue ba shi da masaniya kan zarge-zargen da Obi ke yi.
"Waɗannan zarge-zarge ba su da tushe, kuma wata yunƙuri ce ta jefa Gwamna Hyacinth Alia da al'ummar Benue cikin abin da ka iya zama rikicin siyasar cikin gida na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC)."
"Duba da tarihin yin zarge-zargen da ba su tabbatar ba kan jihar, muna da dalilan yin shakku ko ma ya ziyarci Makurdi, babban birnin jihar, a yau."
Gwamnatin jihar ta kuma ce Peter Obi ba barazana ba ce ga gwamnan jihar, kuma ko da ya ziyarci jihar, hukumomin tsaro suna da ikon kula da duk wani lamari da ya shafi tsaro.