Jerin ƴan takarar shugaban Najeriya 18 da za su fafata a 2027

Asalin hoton, Omoyele Sowore, BBC, Peter Obi, Bola Tinubu and Seyi Makinde/Facebook, Sandy Onor/X
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta wallafa jerin sunayen ƙarshe na ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu da za su fafata a babban zaɓen watan Janairun 2027.
Jerin sunayen, wanda Sakatariyar Hukumar, Rose Oriaran-Anthony, ta sanya wa hannu, kuma aka fitar da shi ranar Asabar a Abuja, ya ƙunshi ƴan takarar da jam'iyyun siyasa 18 suka tsayar domin neman kujerar shugaban ƙasa a 2027.
Hukumar ta INEC ta bayyana sunayen'yantakarar 18 da mataimakansu ga dai wasu daga cikinsu:
APC

Asalin hoton, Social Media
Shugaban kasa mai ci a Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, shi ne dan takarar shugaban kasa a jam'iyya mai mulkin Najeriya APC, kuma Kashim Shettima, shi ne zai sake yi masa mataimaki a zaben 2027.
ADC

Asalin hoton, ADC /X
Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa a Najeriya a lokacin mulkin Obasanjo, shi ne zai yi wa jam'iyyar ADC takarar shugaban kasa, inda Chibuike Rotimi Amaechi kuma zai masa mataimaki.
NDC

Asalin hoton, Peter Obi na Kwankwaso
Peter Gregory Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour a zaben 2023, shi ne zai yi wa jam'iyyar NDC, takarar shugaban kasa a zaben 2027 da ke tafe, yayin da Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso kuma zai masa mataimaki.
Sauran 'yan takarar shugaban kasa da mataimakansu a zaben na 2027, sun hada da;
Jam'iyyar LP, in da Sunday Chibuzo Okereke, zai yi mata takarar shugaban kasa Hajja Bintu Konto, kuma mataimakiya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
PDP, Sandy Ojang Onor, dan takarar shugaban kasa, Umaru Babangida, mataimaki.
AA, Rufai Adekunle Omo-Aje, dan takarar shugaban kasa da Shehu Hussaini, mataimaki.
ADP, Aliyu Abbas-Bin, dan takarar shugaban kasa da Chinazam Ike, mataimaki.
APP, Kabiru Yusuf, dan takarar shugaban kasa da Peace Egobia Ofordile, mataimaki.
AAC, Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa da Haruna Garba Magashi, mataimaki.
APM, Oluseyi Abiodun Makinde, takarar shugaban kasa da Musa Lawal Daura, mataimaki.
BP, Sunday Adenuga, takarar shugaban kasa, Usman Turaki Mustapha, mataimaki.
DLA, Moses Olusoji Adebisi, takarar shugaban kasa da Nafisat Usaku Abubakar, mataimakiya.
NDP, Ada Elizabeth Fredrick Okwori, takarar shugabar kasa da Uchenna Anthony Chukwuemeka, mataimaki.
NRM, Nkem Esther Okereke, takarar shugabar kasa da Nasir Muhammed Sulaiman, mataimaki.
PRP, Donald Duke, dan takarar shugaban kasa, Kabiru Rabiu, mataimaki.
SDP, Adewole Ebenezer Adebayo, takarar shugaban kasa da Usman Muhammed Bugaje, mataimaki.
YPP, Peter Ada Agada, takarar shugaban kasa da Patience Ndidi Key, mataimakiya.
ZLP, Daniel Daberechukwu Nwanyanwu, takarar shugaban kasa da Hassan Khalid, mataimaki.










