Dalilan da ya sa muke so hukumomin Najeriya su taimaka mana — Ƴan gudun hijirar Sudan

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan kasar Sudan waɗanda rikici ya raba da ƙasar suka samu mafaka a Najeriya, sun roƙi hukumomi su taimaka musu da abubuwan da za su kyautata rayuwarsu.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta fitar da wani sabon rahoto da yake bayanin irin mummunan halin da ƙasar Sudan ta faɗa sakamakon yaƙi da ƙungiyar RSF, inda ɗaruruwan mutanen suka fantsama ƙasashe daban-daban don neman mafaka.
Ƴakin na Sudan da ake gwabzawa tsakanin sojojin ƙasar da dakarun RSF ya jefa dumbin iyalai cikin halin kunci inda da dama suka gudu don tsira da rayukansu zuwa kasashen Najeriya da Nijar da Libiya da sauransu.
Da dama daga cikin ƴan gudun hijirar na cikin mawuyacin hali saboda rashin sana'a da kuma rashin karatun ƴaƴansu.
Wata mata da ta ke gudun hijira a Kano, ta shaida wa BBC cewa, ta shafe kusan shekara uku a jihar, amma babban abin da ya fi tayar da mata hankali shi ne rashin karatun ƴayanta.
Ta ce," Burina yarana su yi karatu saboda sus amu sauyi a rayuwarsu, ni na yi karatu har jami'a amma ƴaƴana yanzu suna zaune ko matakin farko na karatun ma ba su fara ba."
"Muna zaune a Kano babu sana'a babu wani abu da muke, dole mu shiga damuwa, don gak ani ina fata a gama ƴakin nan mu koma kasarmu, domin kuɗin haya ma kaɗai ya ishi mutum a Najeriya." In ji ta.
Ita kuwa wata matar da ita ma ta ke gudun hijirar a Kano, ta shaida wa BBC cewa mijinta ya rasu sanadiyar yaƘin, inda ya barta da ƴaƴa takwas.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ta ce," Lokacin da muka baro Sudan kashe-kashe ake yi sosai kuma sai da muka sha wahala kafin mu isa Kano."
Nemawa waɗannan mutane mafuta na daga cikin manufar da ta sa ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnasty international ta fitar da wani rahoto akan yadda yaƙin na Sudan ya jefa ɗumbin ƴan ƙasar cikin ruɗani da tashin hankali tare da kiran hukumomin Najeriya su shiga lamarin.
Malam Isa Sanusi, daraktan ƙungiyar Amnesty a Najeriya,ya shaida wa BBC cewa, su abin da suke so shi ne a tsagaita wuta nan take.
Ya ce,"Tun 2023 ake wannan faɗa a Sudan, don haka ya kamata ƙasashen duniya su tashi tsaye da sahalewar Majalisar Ɗinkin Duniya a tura dakarun wanzar da zaman lafiya domin mu muna ganin yin hakan ne kawai zai kawo zaman lafiya a Sudan.
Isa Sanus,i ya ƙara da cewa akwai fargabar ƙasar Sudan mai mutum fiye da milyan hamsin za ta wargaje, muddin ƙasashen Afirka ƙarƙashin jagoranci Najeriya ba su ɗaukin matakin gaggawa ba, da zai daƙile yiwuwar ƴan bindiga su ɗauki makamai su bazama cikin ƙasashen yankin.
Rikicin a tsakanin sojojin gwamnatin Sudan da na ƙungiyar RSF ya zama ɗaya daga cikin yaƙe-yaƙe mafi ƙazancewa a faɗin Afirka, kuma babu alamar tsagaitawa duk da shiga tsakanin Amurka a wajen tattaunawar zaman lafiya.
Hare-haren jirage marasa matuƙa da ake kai wa kusan kullum sun faɗa wurare kamar kasuwanni da asibitoci da jerin gwanon motocin kai kayan agaji da kuma unguwannin al'umma a yankin Kordofan, lamarin da ya janyo ƙorafi daga jami'an agajin jin-ƙai na Majalisar Dinkin Duniya.










