Yadda murabus din Zinedine Zidane ya girgiza Real Madrid

Bayanan bidiyo, Zidane ya lashe kofin Zakarun Turai uku da kofin La liga a Real Madrid
An wallafa

Ya tafi kamar yadda ya zo, kuma kamar yadda ya shafe shekaru biyu da rabi a cikin mutunci.

Zinedine Zidane ya yanke shawarar ya bar Real Madrid kwanaki biyar bayan ya jagoranci 'yan wasansa ga nasarar lashe kofi Zakarun Turai karo uku a jere.

Matakin murabus din kocin ya jefa Real Madrid cikin wani yanayi na rashin tabbas ga nasarorin da ta samu a zamaninsa.

Shugaban Real Madrid Florentino Perez ya kadu matuka da matakin murabus din Zidane, inda yanzu zai shiga neman wanda ya fi dacewa ya gaji Bafaranshen.

Shin ko wane dalili ne ya sa Zidane yin murabus, sannan ya Real Madrid ta dauki murabus dinsa?

Ko murabus din Zidane ta zo ba-zata?

Tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Zinedine Zidane ne koci na farko da ya lashe kofin Zakarun Turai sau uku a jere

Lalle labarin murabus din ya girgiza Perez, wanda ya zauna kusa da Zidane a lokacin da yake sanar da matakinsa. Fuskarsa ta nuna yadda labarin ya zo ma shi.

Shugaban na Real Madrid ya sanar da cewa Zidane ya shaida ma sa zai yi murabus a kwana guda kafin ya sanar wa duniya zai bar Real Madrid.

Sannan ya ce wanda Zidane kawai ya shaida wa matakinsa na yin murabu shi ne Keftin din kungiyar, Sergio Ramos.

Zidane ya fito ya bayyana dalilin da ya tilasta ma shi yin murabus, inda ya amsa cewa ba shi da tabbacin kungiyar za ta ci gaba da samun nasara a karkashinsa.

Ya nanata cewa "kungiyar na bukatar sabon salo" tare da bayyana irin kalubale da matsin lamba da ke tattare da aikin.

Sai dai bai fadi asalin dalilin da ya tursasa ma shi daukar matakin ba. Ko da yake, da aka tambaye shi ya fadi babban kalubalen da ya fuskanta, sai Zidane ya bayyana cewa yadda Leganes ta fitar da Real Madrid a gasar Copa del Ray a watan Janairu.

An tambayi Zidane, ko don ya lashe kofin Zakarun Turai sau uku a jere ne, dalilin da ya yanke shawarar cewa yanzu lokaci ya yi da ya kamata ya tafi, sai ya amsa cikin dariya yana cewa watakila haka ne.

Ya makomar Real Madrid za ta kasance?

Akwai koci da dama da ake tunanin za su iya maye gurbin Zidane, kuma Kocin Tottenham Mauricio Pochettino na daya daga cikin wadanda ke sahun gaba.

Ana tunanin Pochettino ne Perez zai ba aikin horar da Real Madrid saboda yadda ya jima yana sha'awarsa tun yana aikin horar da Espanyol, kungiyar da ke da alakar kawance da Real Madrid.

Kuma Perez ya yaba da rawar da Tottenham ta taka a gasar Zakarun Turai a kakar da ta gabata.

Sai dai Pochettino bai dade da ya amince da sabuwar yarjejeniyar shekaru biyar da Tottenham ba, kuma ana ganin zai yi wahala kocin ya yi gaggawar ficewa bayan ya amince zai ci gaba da aikinsa a Ingila.

Ko da yake wasu rahotanni sun ce a cikin kwantaragin da ya sanya wa hannu akwai inda aka bayyana zai iya ajiye aikinsa idan har Real Madrid ta neme shi.

Sauran wadanda ake ganin za su iya maye gurbin Zidane sun hada da kocin Chelsea Antonio Conte, da kocin Jamus Joachim Low da tsohon kocin Napoli Maurizio Sarri, yayin da wasu ke ganin Perez zai iya sake dauko Jose Mourinho Kocin Manchester United.

Ya makomar Bale da Ronaldo?

Makomar Cristiano Ronaldo na daya daga cikin tambayoyin da aka yi wa Zidane a lokacin da yake sanar da matakinsa na barin Real Madrid.

An tambayi Zidane ko rashin tabbas ga makomar Ronaldo a Real Madrid na daga cikin dalilan da suka sa ya yi murabus. Nan take ya girgiza kai ya amsa cewa a'a.

Sai dai kuma ana ganin daga cikin manyan batutuwan da duk wanda Perez zai dauka a matsayin sabon kocin Real Madrid, zai fuskanta shi ne makomar Ronaldo da Gareth Bale a kungiyar.

Sannan da batun dauko Naymar, yayin da rahotanni suka ce dan wasan na Brazil ya nuna yana sha'awar barin Paris St-Germain zuwa Real Madrid.

Kazalika sabon kocin zai fuskanci kalubale zabin sabbin 'yan wasa a madadin wasu tsoffin 'yan wasan Real Madrid.

Keylor Navas zai ci gaba da zama golan Madrid na farko ne ko kuwa idan an dauko Thibaut Courtois ko David de Gea za su karbe wurinsa?

Shin lokaci ya yi da Benzema zai kama gabansa? Luca Modric da ke hararar shekara 33, zai ci gaba? Tsakanin Eden Hazard da Robert Lewandowski da Mohamed Salah wa ya fi dacewa da Real Madrid.

Yanzu ina Zidane ya dosa?

Real Madrid players arrive at Cibeles square after winning the La liga title on May 21, 2017

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zidane ya jagoranci Real Madrid ga nasarar lashe kofin La liga na farko tun 2012

Duk da cewa ya lashe kofin zakarun Turai sau uku a jere a cikin shekaru biyu da rabi, har yanzu wasu na ganin Zidane ba kwararren koci ba ne.

Wasu na ganin Zidane ya zo ne a sa'a, maimakon yin amfani da kwarewa.

Zidane ya gaji zubin manyan 'yan wasa, kuma daga cikin 'yan wasan da suka buga wasannin karshe a 2017 da 2018, babu dan wasa guda cikinsu da Zidane ya yi dalilinsa na zuwa Madrid. Amma babbar rawar da ake ganin ya taka shi ne yadda ya tafiyar da zubin manyan 'yan wasan.

Ya girmama 'yan wasan tare da ba kowa hakkinsa a muhallin da ya dace.

Amma ana ganin cewa manyan kungiyoyi da dama za su yi la'akari da shi a lokacin da suke bukatar gwarzon koci. Amma a yanzu Zidane ya yi ikirarin cewa zai huta, ba shi da ra'ayi, yana mai cewa ba zai horar da 'yan wasa ba a kaka mai zuwa.

Wasu na ganin aikin horar da Faransa ne Zidane ke harare idan har Didier Deschamps ya kasa taka rawar gani duk da zubin 'yan wasan da ke gabansa a gasar cin kofin duniya.