Wannan shafi na kawo muku bayanai kai-tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
Rufewa
Bayani kan maĈala
Marubuci, Mustapha Musa Kaita
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo Ĉarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma Instagram domin karanta wasu labaran da muka wallafa ko kuma tafka muhawara a kansu.
Saudiyya ta fitar da wasu sharuÉa kan dawowa da zirga-zirgar jirage
Asalin hoton, Getty Images
Ĉasar Saudiyya ta bayyana sharuÉa ga Ĉasashe 25 da akwai yiwuwar ta amince jiragensu su ci gaba da zirga-zirga zuwa Saudiyyar.
Mujallar Life in Saudi ta ruwaito cewa cikin sharuÉan har da tabbatar da duka fasinjojin da ke cikin jirgin da aka Éauko ba su Éauke da cutar korona.
Kuma dole duka fasinjojin su killace kansu na mako guda idan suka shiga Saudiyyar.
Haka zalika, dole kowane fasinja ya amince da cewa zai biya tarar riyal dubu 500 idan ya karya dokokin da aka saka da kuma zama gidan yari na shekaru biyu.
Cikin Ĉasashe 25 da aka aika wa sharuÉan har da Najeriya.
Yadda tsadar rayuwa ta fara Ĉure haĈurin wasu 'yan Najeriya
Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron rahoton Ibrahim Isa kan tsadar rayuwa a Najeriya
A
Najeriya, `yan kasar da dama sun fusata sakamakon tsadar rayuwa, suna kokawa da
yadda farashin man fetur da wutar lantarki ke karuwa.
Tuni dai farashin kayan
masarufi, irin su shinkafa da masara ya yi tashin-gwauron zabo.
Ita ma Ĉungiyar Ĉwadagon Ĉasar ta nuna rashin jin daÉinta game da wannan lamari, har ta fara
tunanin daukar mataki.
Yayin
da wasu ma`aikata ke kukan ana zaftare masu dan albashin nasu, wasu kuma aikin
ne Éungurungum suka rasa, sakamakon annobar korona.
Ana haka sai ga hukumar wutar lantarki ta yi Ĉarin kuÉin wuta da kusan
ninkin farashinta, kuma ko numfasawa `yan kasar ba su yi ba sai farashin litar
man fetur ya tashi daga naira 148 zuwa dari 151.
Kodayake kungiyar daillalan mai cewa ta yi idan ba
ta sayar da lita a naira 162 ba za ta kwan-ciki.
MINTI ĈAYA DA BBC - LABARAN YAMMA 02/09/2020
Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron labaran
Amurka ta saka takunkumi ga babbar mai shigar da Ĉara ta kotun ICC
Asalin hoton, AFP
Amurka ta saka takunkumi ga babbar mai shigar da Ĉara a kotun aikata manyan laifuka ta duniya wato Fatou Bensouda.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bayyana ICC a matsayin wata kotu da aka kafa bisa wata manufa daban.
Ya kuma ce ICC na yi wa Amurkawa bita-da-Ĉulli ta hanyar ci gaba da bincikar 'yan Ĉasar kan zargin aikata laifukan yaki a Afghanistan.
A yanzu gwamnatin Amurkar ta kwace duk wata kadara ta Ms Bensouda da kuma babban jami'in da ke aiki da ita Phakiso Mochochoko.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta bayyana matakin gwamnatin a matsayin wani yunkuri na kauce wa hukunci.
Sudan na tattaunawa da 'yan tawaye kan aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma
Asalin hoton, AFP
Gwamnatin rikon Ĉwarya a Sudan Ta Kudu da 'yan tawayen da aka yi yarjejeniyar zaman lafiya da su a kwanakin baya sun fara tattaunawa ta yadda za a fara aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma.
Ana sa ran cewa yarjejeniyar da aka cimma da Ĉungiyoyin 'yan tawaye biyar na Ĉasar Ĉarkashin inuwar Sudanese Revolutionary Front (SRF) za ta kawo Ĉarshen yaĈin da aka shafe shekaru 17 ana gwabzawa a yankin gabashin Darfur da kuma yaĈin da aka kwashe shekaru tara ana yi a kudancin Kordofan.
WaÉanda suka rattaÉa hannu a yarjejeniyar sun haÉu ne a Juba babban birnin Ĉasar inda suka amince kan burin nasu.
Jam'iyyun adawa a Nijar sun Ĉulla Ĉawance
Jam'iyyun adawa a Jamhuriyyar Nijar sun Ĉulla kawance inda suka rataÉa hannu tare da saka wa Ĉawancen suna CAP 2021, da niyyar fuskantar gwamnati a Jamhuriya ta bawaki a Ĉasar.
Wannan Ĉawance dai ya zo ne bayan kiran da madugun
adawa a Ĉasar Hama Amadou ya yi na cewa lokaci ya yi da za su fito su yi gwagwarmaya
don kawo Ĉarshen wariyar siyasa da ya ce ake yi cikin kasar.
Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 15 a Sokoto
Asalin hoton, Getty Images
An tabbatar da mutuwar mutum 15 sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta faru a wasu Ĉananan hukumomi shida a jihar Sokoto.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito hukumar bayar da agajin gaggawa ta Ĉasar wato NEMA inda ta ce sama da mutum 27,000 wannan bala'i ya shafa.
Ĉananan hukumomin da bala'in ya shafa sun haÉa da Goronyo da Rabah da Arewacin Sokoto da Wamakko da Silame da Binji.
Rahoton da jaridar ta samu daga hukumar ya nuna cewa mutum 5,254 sun rasa muhallansu inda wasu mutum 12 kuma suka samu raunuka sakamakon rugujewar gine-gine.
Buhari ya jajanta wa al'ummar Kebbi
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwa kan ambaliyar ruwan da ta yi ajalin rayuka ta kuma shafe gonaki.
Shugaban ya ce ya damu sosai kan matsalar ta ambaliya saboda ta mai da hannun agogo baya a yunkurin gwamati na bunkasa noman shinkafa a cikin gida da nufin hana shigar da abinci kasar daga kasashen waje.
Buhari ya ce asarar rayuka shida da aka yi - da kuma har yanzu ba a gama tantance yawan wadanda suka mutu ba, da dubban kadada da ruwa ya mamaye da kuma asarar da manoman shinkafa suka yi ta akalla fiye da Naira biliyan guda, wasu alamu ne dake nuna gagarumin koma baya wajen bunkasa noman abinci.
A wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan kafofin watsa labarai Malam Garba Shehu ya sanya wa hannu, shugaban ya ce labarin da ya fito daga Kebbi ba mai dadi ba ne, kuma ya zo a lokacin da tasirinsa zai fi kowanne muni.
Buhari ya jajanta wa iyalan da suka suka rasa danginsu da kuma manoman da suka yi asara, sannan ya ce gwamnatin tarayya za ta yi aiki da gwamnatin jihar Kebbi wajen taimaka wa mutanen da lamarin ya shafa.
Ethiopia za ta yi gagarumin rabon burodi kyauta
Asalin hoton, Sheger Bread
Hukumomi a kasar Habasha sun yi shirin raba dubban kunshin burodi kyauta a Addis Ababa babban birnin kasar, a wani bangare na murnar shiga sabuwar shekarar kasar ta 2013.
Za a raba burodin ne a ranar Litinin 7 ga Satumba, a ranar farko ta bikin da za a kwashe kwanaki biyar ana gwangwajewa a watan karshe na shekarar ta Habasha ko kuma Ethiopia.
A watan Yulin da ya wuce ne gwamnati ta kaddamar da wani katafaren gidan burodi a wajen babban birnin kasar.
Hukumomi sun ce za a iya gasa matsakaicin burodi miliyan biyu a kowace rana a gidan.
Wani jami'in gwamnati ya yada bidiyon yadda ake aiki a gidan burodin na Sheger lokacin kaddamar da shi.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi âamince sannan ka ci gabaâ.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Kungiyar IPMAN ta mayar da farashin man fetur 162
Asalin hoton, Others
Kungiyar masu gidajen mai masu zaman kansu ta kasa IPMAN, ta umarci 'ya'yanta su kara kudin farashin mai zuwa Naira 162 kan kowace lita.
Ipman ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamakon karin kudin mai da gwamantin Najeriya ta yi zuwa N151.56k.
Wata sanarwa da reshen kungiyar na shiyyar kudu masu yamma ya fitar ta ce ba su da wani zabi illa su kara kudin man domin gudun kada su yi asara.
Shugaban kungiyar ta Ipman reshen Kano mai kula da wasu jihohin arewacin Najeriya Alhaji Bashr Dan Malam ya ce dole ne su yi karin, domin cike fansshe karin da za su samu daga wajen da suke sayo man fetur din sakamakon matakin gwamnati na mayar da fetur din N151.56k.
Wannan ne karo na uku da gwamnati take sauya farashin mai a 'yan watannin baya-bayan nan, sai dai sabanin wasu lokutan da ake rage farashin, karin na man na wannan karon shi ne mafi yawa a baya-bayan nan.
Isra'ila ta yi tur da danne wuyan Bafalasdine da wani sojanta ya yi
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Khairi Hanoon ya ce an kama shi ne a yayin wata zanga-zangar lumana, amma sojojin Isra'ila sun ce ta tarzoma ce
Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana yin duba kan lamarin da ya faru wanda aka dauki bidiyon wani soja ya danne wuyan wani Bafalasdine da gwiwar kafarsa, yayin da mutumin ke kwance a kasa hannayensa cikin ankwa a yayin wata zanga-zanga a Yammacin Kogin Jordan da Yahudawa suka mamaye.
Bidiyon ya nuna yadda sojan ya danne Khairi Hanoon, wani fitaccen mai fafutuka mai shekara 60 da 'yan kai a kasa.
Daga nan sai sojan ya sanya giwarsa ya danne wuya da kan mutumin na kusan dakika 50.
Lamarin ya jawo yin tur da Allah-wadai daga Falasdinawa, amma rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarun sun yi hakan ne don shawo kan lamarin da ke neman rincabewa.
Ta ce bidiyon bai nuna abin da ya faru gaba daya ba, don bai nuna yadda masu zanga-zangar suke tunkara da jifan sojojin ba, dalilin da har ya kai su ga kama mutane.
Ba mu fitar da sunayen Éaliban da aka bai wa tallafin karatun Ĉasar waje ba - Ma'aikatar Ilimin Najeriya
Jerin sunayen da ke yawo a intanet na Éaliban Najeriya da aka bai wa tallafin karatun Ĉasar waje ba na gaskiya ba ne, a cewar Ma'aikatar Ilimi ta Najeriya.
An fara yaÉa jerin sunayen da ke yawo ne daga wata wasiĈa da aka ce wani Éan Najeriya mazaunin Ĉasar waje ne ya rubuta wa Ministan Ilimi Adamu Adamu domin yin Ĉorafi game da yadda ake bayar da tallafin karatun.
Me Ĉorafin ya yi zargin cewa abin kunya ne ga arewacin Najeriya a cikin wasiĈar da aka yi wa take da JUSTICE TO ONE IS JUSTICE TO ALL wato YIN ADALCI GA MUTUM ĈAYA ADALCI NE GA AL'UMMA BAKI ĈAYA.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wasiĈar na cewa a jerin sunayen, mutum 21 ne kawai suka fito daga jihohin arewa 19, yayin da jihohin kudu suka samu mutum 70.
Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukan zumunta, Ma'aikatar Ilimi ta Najeriya ta ce har yanzu ba ta saki sunayen waÉanda aka bai wa tallafin karatun Ĉasar wajen ba na 2020 ĈarĈashin shirin 2020 Bilateral Education Agreement.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi âamince sannan ka ci gabaâ.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Labarai da dumi-dumi, Guba aka saka wa jagoran 'yan adawar Rasha
Ĉasar Jamus ta ce an saka wa jagoran 'yan adawar Rasha, Alexei Navalny gubar Novichok.
Gwaji ya nuna akwai "hujja Ĉarara" cewa an saka masa guba ta rukunin Novichok.
An kai Mista Navalny birnin Berlin na Jamus don duba lafiyarsa bayan ya yanke jiki ya faÉi a cikin wani jirgi a watan da ya gabata.
Tun daga wannan lokaci yake a sume.
Cristiano Ronaldo ya cashe da waĈar Jerusalema
Ĉan Ĉwallo Cristiano Ronaldo ya zama tauraro na baya-bayan nan da ya tallata waĈar Master KG ta Jerusalema.
MawaĈin Éan Ĉasar Afirka ta Kudu ya gode wa Ronaldo a shafinsa na Twitter.
Ronaldo ya wallafa wani bidiyo ne mai tsawon minti huÉu a Instagram ana cashewa da waĈar kuma ya rubuta: "Rayuwa ta fi daÉi da masoyaâ¤ï¸ Ku ji daÉi tare da masoyanku cikin nishaÉi."
WaĈar ta Jerusalema wadda ta addinin Kirista ce, ta karaÉe Nahiyar Afrika da wajenta.
Wani da korona ta kashe 'yan uwansa bakwai za a yi gwajin rigakafin cutar a kansa
Jacob Serrano na da dalili mai Ĉwari sama da kowa domin taimakawa wurin samar da rigakafin annobar cutar korona saboda ta kashe 'yan uwan matashin har guda bakwai.
Jacob mai shekara 23 na cikin wani rukunin 'yan sa-kai da za a yi gwajin rigakafin cutar a kansu.
Yana cikin mutum 31 'yan Amurka da aka yi wa ragakafin a Florida a Ĉarshen makon da ya gabata yayin gwajin maganin a mataki na Ĉarshe.
"Na san cewa akwai hatsari saboda kamar gwaji ne," in ji shi a cikin wata hira da kafar CBS News. "Amma na gwammace na bayar da gudummawata ko ma mene ne zai faru."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi âamince sannan ka ci gabaâ.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Ĉungiyar Kiristocin Najeriya ta nemi Buhari ya soke dokar CAMA
Asalin hoton, Nigeria Presidency
Ĉungiyar Kiristoci ta Najeriya CAN ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya soke dokar CAMA wadda ya saka wa hannu ranar 7 ga watan Agusta.
Dokar mai suna Companies and Allied Matters Act (CAMA) 2020, ta tanadi cewa shugaban hukumar kula da kuma bai wa kamfanoni lasisi ta Corporate Affairs Commission (CAC) zai karÉe ragamar duk wata Ĉungiyar addini idan har aka tabbatar akwai rashin gaskiya a shugabancin Ĉungiyar.
Kazalika dokar ta bai wa CAC ikon dakatar da kwamitin amintattun Ĉungiyar addini sannan ta naÉa shugabannin riĈo idan ta aminta cewa ba a gudanar da ayyukan Ĉungiyar yadda suka dace ko kuma akwai almundahana.
Jaridar TheCable ta ruwaito shugaban Ĉungiyar yana bayyana matsayinsu a cikin wata wasiĈa da ya aike wa mai bai wa Buhari shawara kan Majalisar Dattawa ranar Talata.
Ĉungiyar ta haĈiĈance cewa ba a tuntuÉi waÉanda ya abin ya shafa ba kafin amincewa da dokar.
"Muna kallon wannan doka a matsayin wani kundi mai cike da batutuwan da za su kawo tarnaĈi ga tsaro da jin daÉin Najeriya," CAN ta bayyana a wasiĈar.
Kashi biyu cikin uku na 'yan Najeriya na amfani da intanet
Asalin hoton, Getty Images
Farfesa Umar Danbatta, shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya Nigerian Communications Commission (NCC), ya ce masu amfani da layin wayar salula a Najeriya sun Ĉaru zuwa milyan 199.3.
An samu Ĉaruwar ne daga miliyan 184 a watan Disamban 2019 zuwa Mayun 2020.
Dambatta ya bayyana haka ne yayin miĈa lamunin kuÉi da NCC ta bai wa wasu cibiyoyin sadarwa biyu da za su gudanar da bincike kan annobar korona ranar Talata, wanda ya gudana ta intanet.
Ya Ĉara da cewa masu amfani da intanet ma sun Ĉaru a tsawon wannan lokacin daga miliyan 126 zuwa 147.1, yayin da masu sayen layin intanet a dunĈule wato broadband suka Ĉaru daga miliyan 72 zuwa 80.2.
Kasancewar Najeriya na da al'umma kusan miliyan 200, hakan na nuna cewa kashi biyu cikin uku na 'yan Ĉasar na amfani da intanet.
"Irin waÉannan [bincike] za su taimaka wurin samar da yiwuwar gudanar da taruka ta intanet da za su riĈa samar da tazara [tsakanin mutane]," in ji shi.
'Yan adawar Venezuela sun yarda su shiga zaÉen Ĉasar
Turkiyya da ke sasanta rikicin siyasar Venezuela ta ce biyu daga cikin fitattun jagororin 'yan adawar Ĉasar sun amince su shiga zaÉen da za a yi na watan Disamba.
Ministan harkokin wajen Turkiyya, Mevlut Kavusoglu ya ce Henrike Kapriles da Stalin Gonzalez sun nemi a bai wa masu sanya ido na Ĉasashen waje damar duba yadda zaÉen zai gudana.
'Yan adawa dai sun ki shiga zaÉen, kana sun zargi shugaba Nicolas Moduro da ĈoĈarin yin maguÉi.
Kwanan nan ne shugaban ya yafe wa Éaruruwan 'yan hamayya da suka shafe watanni a garĈame, domin ba su damar tsayawa takara idan suna da ra'ayin yin hakan.
PSG na son Bellerin, Chelsea ta sanya farashi kan Kante, Juve na zawarcin Suarez
Asalin hoton, Getty Images
Paris St-Germainta yi tayin biyan £25m da kuma Ĉarin £5m kuÉin talla kan Éan wasan Arsenal Hector Bellerin, a yayin da Bayern Munich da Juventus su ma suke zawarcin Éan wasan na Sufaniya mai shekara 25.(Guardian)
Everton ta amince ta Éauko Éan wasan Colombia James Rodriguez, 29, daga Real Madrid a kwangilar shekara uku.(Telegraph)
Chelsea za ta sayar da N'Golo Kante kan £80m a yayin da Inter Milan take zawarcin Éan wasan na Faransa mai shekara 29.(Express)
Sai dai tsohon Éan wasan Leicester Kante yana son ci gaba da zama a Chelsea.(Goal)