Jirgin ruwa ɗauke da fasinja 116 ya nutse a Guyana
Asalin hoton, Transport and Harbours Department
Hukumomi a ƙasar Guyana sun ce wani jirgin ruwa da ke ɗauke da fasinja 116 ya nutse a gabar Tekun Atlantika, inda kawo yanzu mutum takwas ne kawai aka ceto.
Ministan ayyukan jama'a na ƙasar, Juan Edghill, ya ce jirgin na kan hanyarsa ne daga babban birnin ƙasar, Georgetown, zuwa Port Kaituma da ke arewacin ƙasar lokacin da hatsarin ya faru a daren Asabar.
Ministan ya ce ana ci gaba da aikin nema da ceto domin gano dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin.
Ya zuwa yanzu, ba a san musabbabin hatsarin ba.
Iran ta ce adadin waɗanda suka mutu a hare-haren Amurka ya haura 50
Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar lafiyar Iran ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon hare-haren sama da Amurka ta kai ya haura mutum 50, yayin da sama da mutum 500 suka jikkata.
Shugaban cibiyar hulda da jama'a ta ma'aikatar, Hossein Kermanpour, ya rubuta a shafin X cewa zuwa karfe 7:00 na safiyar 18 ga Yuli, hare-haren sun yi sanadin jikkatar mutum 517 da kuma mutuwar fiye da mutum 50.
A cewarsa, daga cikin waɗanda suka jikkata akwai mata 35 da yara 19 da ba su kai shekara 18 ba.
Haka kuma cikin waɗanda suka mutu akwai mata biyar da yara biyu da ba su kai shekara 18 ba.
Ya ƙara da cewa an sallami mutum 468 daga asibiti bayan sun samu kulawa, yayin da mutum 33 ke ci gaba da karbar magani a asibitoci.
An saki wasu masu rajin kare namun daji da aka tsare a Iran
Kafafen yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa an saki Hooman Jokar, tsohon daraktan masu rajin kare namun daji da kuma masaniyar namun daji kuma mai fafutukar kare muhalli Sepideh Kashani, tare da 'yar uwarta Sima Kashani.
Lauyan su, Hojat Kermani, ya ce an saki mutanen uku daga tsarewa.
A cewar shafin labaran Emtaed, jami’an ma’aikatar leƙen asirin Iran sun kama su a gidajensu da ke Tehran a ranar 1 ga Yuli.
Lauyan ya kuma ce a lokacin kamen, jami’an tsaron sun ƙwace dukkan na’urorin su na lantarki, sannan suka tsare Sima Kashani, 'yar uwar Sepideh Kashani.
RFI: Rasha ce ta shirya sasancin Mali da Aljeriya
Asalin hoton, Getty Images
Wani sharhi da gidan rediyon Radio France Internationale (RFI) ya wallafa a shafinsa na intanet a ranar 18 ga Yuli ya yi iƙirarin cewa sulhun da aka samu tsakanin Mali da Aljeriya ya samu ne sakamakon shiga tsakani Rasha ta yi, wanda rahoton ya ce ya biyo bayan gajiya da ta yi da rashin jin daɗin raunin ƙawayenta na yankin Sahel, musamman ma ƙasar Mali.
A cewar marubucin sharhin, Barry, bayan janyewar dakarun Africa Corps daga Kidal cikin watan Afrilu, lamarin ya zama abin kunya saboda saboda sun fice ne tare da rakiyar mayaƙan ƴanawaren Tuareg, da kuma wani sabon jerin hare-hare da aka kai a farkon watan Yuli wanda ya yi wa dakarun illa a sansanoninsu da ke yankuna masu nisa.
Moscow ta matsa wa shugaban gwamnatin mulkin sojin Mali, Janar Assimi Goïta, ya fahimci cewa ƙarfin ikon Mali kan yankunan arewacin ƙasar ya dogara ne da haɗin gwiwa da Aljeriya.
Sharhin ya ƙara da cewa a duka waɗannan abubuwa biyu, sa hannun Aljeriya ne ya taimaka wajen tabbatar da cewa dakarun Rasha sun samu hanyar tsira.
Rahoton ya ce: "Sau biyu cikin ƙasa da watanni shida, Aljeriya ce ta kuɓutar da Mali daga matsalar Azawad... Ba don taimakon Aljeriya ba, ba zai yiwu ta riƙe arewacin ƙasar ba. Tun daga shekarar 1963 hakan abin yake."
Iran ta ce wasu jiragen ruwa biyu sun yi hatsari a mashigar Hormuz
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar Sojin Ruwa ta IRGC a Iran ta ce jiragen ruwa biyu da ta zarga da ƙeta umarnin zirga-zirga a Mashigin Hormuz sun yi hatsari yayin da suke ƙoƙarin bi ta wata hanya da rundunar ta bayyana a matsayin marar tsaro.
A cikin wata sanarwa, rundunar ta ce jiragen ruwa huɗu ne suka kashe na'urorin tantance inda suke da kuma yin watsi da gargaɗin cibiyar kula da Mashigar Hormuz ta IRGC.
Ta zarge su da yunƙurin ficewa daga mashigar ta wata hanya da ba a amince da ita ba.
Rundunar ta IRGC ta sake jaddada cewa ita ce da cikakken iko kan Mashigar Hormuz, tana mai cewa hanyar da ta amince da ita kaɗai ce ke da tsaro ga zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.
Mayaƙan ISWAP sun kashe ɗalibai yayin musayar wuta da sojoji a Borno
Asalin hoton, Getty Images
Wasu ɗalibai sun mutu bayan harbin bindigogi da ake zargin mayaƙan ISWAP suka yi ya same su yayin musayar wuta da jami’an tsaro, lokacin da sojoji ke ƙoƙarin daƙile harin da suka kai makarantar da ake amfani da ita a matsayin masaukin ɗalibai a Monguno da ke Jihar Borno.
A cikin wata sanarwa, rundunar Operation HADIN KAI ta ce maharan sun kai farmaki Kwalejin mata ta gwamnati (FGGC) da misalin ƙarfe 1:30 na safiyar ranar 19 ga Yuli da nufin yin garkuwa da ɗalibai.
Sai dai jami'an tsaro da ke wurin, tare da goyon bayan rundunar MOPOL da dakarun gaggawa, sun yi gaggawar mayar da martani tare da hana maharan cimma burinsu in ji sanarwar.
Rundunar ta ce an ceto ɗalibai 46 baki ɗaya tare da kwashe su zuwa Barikin Kinnasara da ke Monguno domin duba lafiyarsu, kuma babu wanda aka yi garkuwa da shi.
Ta kuma jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu tana mai cewa ana ci gaba da farautar maharan da kuma binciken mutanen da ake zargin sun taimaka musu wajen kai harin..
Baharain da Kuwait sun ce sun daƙile hare-haren Iran ta sama
Asalin hoton, Getty Images
Baharain da Kuwait sun ce sun daƙile wasu hare-haren sama da Iran ta kai musu.
An kuma ji ƙarar gargaɗi a birnin Manama, babban birnin Baharain, inda hukumomi suka buƙaci mazauna yankin su nemi mafaka.
Tun da fari, Iran ta ce ta kai hari kan sansanonin sojin Amurka guda biyu da ke Kuwait a matsayin martani kan kwana takwas a jere na hare-haren da Amurka ke kai mata.
A nata ɓangaren, rundunar sojin Amurka ta ce hare-haren nata sun kai wa mambobin rundunar juyin-juya-hali ta Iran, waɗanda take zargi da hannu a harin da aka kai a Jordan, wanda ya yi sanadin mutuwar sojojin Amurka biyu.
Sojojin Najeriya su ce sun daƙile harin ISWAP
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta daƙile wani hari da mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka kai kan wani sansanin soji a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar, inda aka kashe wasu daga cikin maharan, yayin da soja guda ɗaya ya rasu a artabun.
Kafar yaɗa labarai ta Daily Post mai zaman kanta ta ruwaito a ranar 18 ga Yuli cewa kakakin rundunar Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce maharan sun samu damar mamaye wani ɓangare na sansanin da ke ƙauyen Logomani a ƙaramar hukumar Ngala na ɗan wani lokaci, kafin sojojin su sake tsara kansu tare da ƙaddamar da farmakin martani.
Kyaftin Goni ya ce: "Abin takaici, soja ɗaya ya sadaukar da rayuwarsa a yayin artabun, yayin da aka lalata motocin yaƙi guda biyu da kuma wasu kayan aikin yaƙi."
Bai bayyana ranar da harin ya faru ba, haka kuma rahoton Daily Post bai fayyace hakan ba, inda ya ƙara da cewa an shawo kan lamarin bayan an tura ƙarin sojoji domin ƙarfafa tsaron yankin.
A ranar 12 ga Yuli, rundunar sojin ta sanar da cewa ta daƙile wani hari da ISWAP ta kai kan wani sansanin soji a ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno. Hukumomi sun kuma ce sun kama wani da ake zargin ɗan ƙasar Morocco.
A wani samame daban kuma, rundunar sojin ta ce ta ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su tare da ƙwace kuɗi kimanin dala 870 na Amurka da kuma kayan abinci a wani samame da ta kai a ƙaramar hukumar Askira/Uba ta jihar.
Iraq na shirin gina bututun mai domin kauce wa mashigar Hormuz
Gwamnatin Iraq na nazarin wani shiri na gina bututun mai daga Basra zuwa Kirkuk, sannan zuwa tashar jiragen ruwa ta Ceyhan a Turkiyya da kuma Banias a Siriya.
Ministan Man Fetur ɗin ƙasar, Bassem Muhammad Khedir, ya ce shirin na da nufin faɗaɗa hanyoyin fitar da man ƙasar maimakon dogaro da Mashigar Hormuz kaɗai.
Ya bayyana cewa ma'aikatar man fetur ta ƙasar na nazarin yadda za a aiwatar da aikin, wanda kuma zai haɗa da tsawaita bututun zuwa Banias, wani birnin gabar teku a arewa maso yammacin Siriya mai matatar mai da tashar fitar da kayayyaki ta Bahar Rum.
Mahara sun kashe aƙalla sojojin Mali 50 a kwanton-ɓauna
Asalin hoton, MICHELE CATTANI/AFP via Getty Images
Hukumomi a arewacin Mali sun ce mayaƙan Tuareg masu neman ɓallewa da kuma mayaƙan ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi sun kashe aƙalla sojojin Mali 50 a wani kwanton-ɓauna da suka yi wa ayarin motocin soji a ranar Asabar da ta gabata.
Sun kuma ce maharan sun yi garkuwa da sama da mutum 20 a yayin harin.
Wannan bayani na jami'an yankin ya yi daidai da ikirarin da Azawad Liberation Front (FLA) ta yi cewa mayaƙanta sun yi wa sojojin Mali da kuma dakarun Rasha da ke mara musu baya mummunar illa.
A cewar FLA, ayarin motocin sojin na kan hanyarsa ne daga garin Anefis, mai muhimmanci ta fuskar dabarun soja, zuwa birnin Gao, lokacin da aka kai musu harin.
Trump da shugaban FIFA za su gabatar da kofin duniya ga zakaran gasar
Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran shugaban Amurka Donald Trump zai halarci wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya tsakanin Spain da Argentina a ranar Lahadi, inda zai miƙa kofin ga tawagar da ta lashe gasar tare da shugaban FIFA Gianni Infantino.
Ziyarar Trump na zuwa ne bayan ce-ce-ku-ce da ya janyo, sakamakon wani rahoto da ya ce ya kira shugaban FIFA kai tsaye domin neman a ɗage dakatarwar ɗan wasan Amurka Folarin Balogun kafin wasan zagaye na 16.
Duk da suka da aka yi kan zargin tsoma bakin siyasa a harkokin FIFA, Trump ya bayyana gasar Kofin Duniya ta 2026 a matsayin ɗaya daga cikin wasannin da suka fi samun nasara a tarihi, yana mai cewa ta ƙara shahara ƙwallon ƙafa a Amurka.
An samu girgizar ƙasa mai ƙarfi a Khuzestan dake Iran
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar agajin gaggawa ta Red Crescent a Iran ta ce wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 5.0 a ma'aunin Richter ta auku a yankin Saland da ke lardin Khuzestan da safiyar Lahadi.
Babban daraktan hukumar a lardin ya bayyana cewa girgizar ƙasar ta afku ne da misalin ƙarfe 5:55 na safiya, yayin da cibiyarta ke zurfin kilomita 12 ƙarƙashin ƙasa.
A cewarsa, an tura tawagogin ceto guda biyu zuwa ƙauyukan da ke kusa da inda girgizar ƙasar ta fara domin duba ko an samu wata ɓarna ko asarar rayuka.
Haka kuma, an sanya dukkan cibiyoyin Red Crescent da ke lardin Khuzestan cikin shirin ko-ta-kwana domin mayar da martani cikin gaggawa idan buƙatar hakan ta taso.
Zuwa yanzu dai, babu wani rahoto da ke nuna an samu asarar rayuka ko wata babbar ɓarna sakamakon girgizar ƙasar.
Iran ta ce ta kai hari kan sansanonin sojin Amurka biyu a Kuwait
Asalin hoton, Getty Images
Sojojin Iran sun ce sun kai hari da jirage marasa matuƙa zuwa sansanonin sojin Amurka guda biyu da ke Kuwait.
A cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar, sun ce hare-haren sun auka wa ma'ajiyar makamai da ke sansanin Al-Adiri, da kuma na'urorin rada da na sa ido ta sama da ke sansanin Ali Al-Salem.
Iran ta ce ta kai waɗannan hare-hare ne a matsayin martani ga hare-haren da take zargin Amurka da kai wa ƙasar, waɗanda ta ce sun shafi muhimman ababen more rayuwa da kuma yankunan fararen hula.
Sai dai zuwa yanzu, gwamnatin Kuwait da sojojin ƙasar, da kuma jami'an Amurka, ba su fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da aukuwar hare-haren ba, kuma ba a samu wani tabbaci mai zaman kansa da ke tabbatar da ikirarin Iran ɗin ba.
Za mu ɗorawa Amurka nauyin da ya fi na yaƙe-yaƙen baya tsanani - Iran
Asalin hoton, Tasnim news agency
Iran ta yi barazanar cewa za ta ɗora wa Amurka nauyin da ya fi na yaƙe-yaƙen da suka gabata tsanani idan ta ci gaba da kai mata hare-hare.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Ali Abdullahi, kwamandan Hedkwatar Tsakiya ta Khatam al-Anbiya, ya fitar, inda ya ce rundunonin sojin ƙasar a shirye suke su mayar da martani cikin ƙarfi ga duk wata barazana daga Amurka.
Abdullahi ya ce duk wani hari da Amurka za ta kai zai fuskanci martani mai tsauri daga Iran, yana mai jaddada cewa ƙasarsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen kare kanta.
Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin rundunonin tsaro, gwamnati da al'ummar Iran, tare da yin ishara da wata wasiƙa da aka danganta wa Mojtaba Khamenei, wadda ya ce ta nuna muhimmancin jajircewa da haɗin kai wajen tunkarar barazanar ƙasashen waje.
Assalamu alaikum
Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye wanda ke kawo muku labaran duk abubuwan da ke faruwa a Najeriya da saurarn sassan duniya a wannan rana ta Lahadi.
Aisha Bbabangida ce ka fatan saka kasance da ku a daidai wannan lokaci.