Aƙalla Falasɗinawa 9 sun mutu a hare-haren da Isra'ila ta kai Gaza
Aƙalla Falasɗinawa tara ne suka mutu sakamakon hare-haren sama guda biyu daban-daban da Isra'ila ta kai a Gaza.
Jami'an lafiya na Gaza sun sanar da cewa mutum uku sun mutu a wani hari da aka kai a unguwar Zeitoun da ke cikin birnin Gaza.
Kafofin yaɗa labarai na Falasɗinawa sun kuma ruwaito cewa wasu mutum shida sun mutu a wani hari daban da aka kai kan wani ginin gidaje da ke yammacin birnin.
Har zuwa yanzu, Isra'ila ba ta fitar da wata sanarwa kan waɗannan hare-hare ba.
Hare-haren Isra'ila a Gaza na ci gaba duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ya kamata ta fara aiki tun watan Oktoban bara.
A cewar Ma'aikatar Lafiya ta Gaza, wadda ke karkashin kulawar Hamas, dakarun Isra'ila sun kashe fiye da mutum dubu ɗaya a Gaza tun bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wutar.