Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 20 ga watan Yulin 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Kotu a Ghana ta daure jagoran adawa shekaru 20

    Wata kotu a Ghana ta yanke wa ɗaya daga cikin fitattun ƴan adawar ƙasar hukuncin daurin shekara 20 a gidan yari bayan samunsa da laifin haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.

    Kotun ta samu Bernard Antwi Boasiako, shugaban jam'iyyar New Patriotic Party (NPP) da laifuka shida, ciki har da ba da umarnin gudanar da haƙar zinari ba tare da bin ƙa'ida ba.

    An ce wannan ne mafi tsaurin hukunci da aka taɓa yanke wa wani babban ɗansiyasa a Ghana kan laifukan da suka shafi haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba.

    Wannan lamarin a cewar hukumomin ƙasar ya daɗe yana haifar da matsalolin gurɓata muhalli da lalata albarkatun ƙasar.

  2. Sabon Firaministan Birtaniya ya yi waya da Trump kan rikicin Gabas ta Tsakiya

    Sabon Firaministan Birtaniya, Andy Burnham, ya tattauna ta waya da shugaban Amurka Donald Trump, a cikin jerin kiraye-kirayen farko da ya yi bayan hawa mulki.

    A cewar ofishin Firaministan, shugabannin biyu sun tattauna kan shirye-shiryen gasar cin kofin duniya da kuma rikicin da ke ci gaba da ƙamari a Gabas ta Tsakiya.

    Burnham ya kuma shaida wa Trump cewa yana fatan yi masa rangadi a birnin Manchester da ke arewacin Birtaniya, inda ya taɓa riƙe muƙamin magajin gari.

    Haka kuma sabon firaministan ya yi magana ta waya da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, inda ya sake jaddada cikakken goyon bayan Birtaniya ga Ukraine.

  3. Sabon Firaministan Birtaniya Andy Burnham ya fara garambawul a gwamnatinsa, Ya sallami jami'ai 11 masu kusanci da tsohon Firaminista Starmer

    Sabon Firaministan Birtaniya, Andy Burnham, ya fara yin garambawul a gwamnatinsa, wani mataki da ake ganin zai taimaka masa wajen aiwatar da sauye-sauyen da ya yi alƙawarin kawowa.

    Burnham ya naɗa tsohon shugaban jam'iyyar Labour, Ed Miliband, a matsayin sakataren harkokin wajen ƙasar, yayin da ya naɗa John Healey a matsayin ministan kuɗi.

    Sabon ministan kuɗin dai shi ne tsohon sakataren tsaron Birtaniya, wanda ya sauka daga muƙaminsa a watan Yuni bayan ya zargi gwamnati da kasa samar da isassun kuɗaɗen da ake buƙata domin ɓangaren tsaron ƙasar.

    Mutane goma 11 ne da ke da kusanci da tsohon firaiministan Kier Starmer sabon firaiminstan ya kora daga gwamnatin ciki har da mataimakin tsohon Firaiministan.

    Ga jerin waɗanda Firaminista Andy Burnham ya sallama daga majalisar ministoci:

    • Rachel Reeves – Ministar kuɗi
    • David Lammy – Mataimakin tsohon Firaminista
    • Steve Reid – Ministan gidaje
    • Peter Kyle – Ministan kasuwanci
    • Lord Richard Hermer – Babban lauyan gwamnati (Atoni Janar)
    • Liz Kendall – Ministar kimiyya, ƙirƙire-ƙirƙire da fasaha
    • Jo Stevens – Sakatariyar kula da harkokin Wales
    • Hilary Benn – Sakataren kula da harkokin Arewacin Ireland
    • Darren Jones – Babban sakataren ofishin firaminista
    • Jenny Chapman – Ministar bunƙasa ƙasa
    • Nick Thomas-Symonds – Ministan hulɗa da Tarayyar Turai

    Bayan sallamar ta, Rachel Reeves ta wallafa a shafinta na X cewa yin aiki a matsayin ministar kuɗin ƙasar shi ne mafi girman abin alfahari da ta taɓa samu a rayuwarta.

  4. Kotu ta yanke wa jagororin ƙungiyar Ansaru hukuncin ɗaurin rai da rai a Najeriya

    Kotu a Najeriya ta yanke wa wasu manyan jagororin ƙungiyar Ansaru mai alaƙa da Al-Qaeda hukuncin ɗaurin rai da rai, bayan sun amsa laifukan da suka shafi ta'addanci da ake tuhumarsu da su.

    Mutanen da gwamnatin ƙasar ke zargin ta kama su ne tun a watan Agustan 2025 kuma sun shafe watanni suna musanta zarge-zargen.

    Mutanen biyu da ake zargi Mahmud Usman, wanda hukumomi suka ce shi ne jagoran ƙungiyar Ansaru, da kuma Abubakar Abba, wanda ake zargi dan shi ne mataimakinsa sun amsa dukkan tuhume-tuhumen 32 da ake musu.

    A zaman kotun na ranar Litinin, lauyansu Bala Dakum ya shaida wa kotun cewa bayan tattaunawa da waɗanda yake karewa, sun amince da tuhume-tuhumen bayan sake karanto su a gaban kotu,

    Hukumar SSS ta gurfanar da su a gaban kotu tun a watan Satumbar 2025 kan tuhume-tuhumen da suka haɗa da ɗaukar nauyin ta'addanci, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba, ƙera bama-bamai na gida da kuma wasu laifuka masu alaƙa da ta'addanci.

    Hukumar ta kuma zarge su da jagorantar ƙwayoyin ta'addanci a ɓoye, da shirya hare-hare, da kuma alaƙa da ƙungiyoyin ta'addanci masu alaƙa da Al-Qaeda da ke aiki a yankunan Sahel da Maghreb.

    Mahmud Usman ya amsa cewa shi ne jagoran Ansaru, yayin da su biyun suka amsa kasancewa mambobin ƙungiyar tare da shiga garkuwa da mutane, haƙar ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba da sauran ayyukan ta'addanci.

    Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya sanar da kama mutanen biyu ne tun a watan Agustan 2025 a wani samame na haɗin gwiwar hukumomin tsaro bayan tattara bayanan sirri tsakanin watan Mayu da Yulin shekarar.

  5. Ƴanbindiga sun kashe babban limamin Juma'a a Iran

    Rundunar ‘yan sandan lardin Sistan da ke Baluchestan a ƙasar Iran, ta ce wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe Maulvi Mohammad Anwar Rigi, limamin Juma’a na Ahlus Sunna a Mirjaveh, da safiyar ranar Litini.

    Rundunar ‘yan sandan ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa maharan sun tsere daga wurin tare da bindigoginsu nan take bayan harbe-harben.

    Sanarwar ta ce cibiyar bayar da agajin gaggawa ta ‘yan sanda ta mayar da martani cikin gaggawa bayan samun rahoton harbe-harben a kusa da Babban Masallacin Mirjaveh.

    To sai dai bayanan sun ce Maulvi Mohammad Anwar Rigi ya rasu ne sakamakon munanan raunukan da ya samu.

    ‘Yan sandan Iran sun ce an fara gudanar da bincike domin gano da kama waɗanda suka kai harin.

    A gefe guda kuma, Cibiyar Tattara Bayanai kan Hakkokin Dan Adam ta Baluchistan, tana ambaton majiyoyinta, ta ce Maulvi Mohammad Anwar Rigi na kan hanyarsa ta zuwa masallaci domin gudanar da sallar asuba ne lokacin da mutanen masu ɗauke da makamai da ke cikin wata mota suka buɗe masa wuta.

  6. Bayanan sirrinmu sun nuna Amurka na jibge kayan yaƙi - Qalibaf

    Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, ya zargi Amurka da cewa tana ikirarin neman zaman lafiya yayin da take ƙara ƙarfafa kasancewar sojojinta a yankin.

    Mista Qalibaf, wanda shi ne babban mai shiga tsakani na Iran a tattaunawar da ake yi da Amurka, ya rubuta a shafinsa na X cewa:

    “Amurkawa na ci gaba da kawo sabbin kayan aikin soja zuwa yankin yayin da suke ikirarin suna neman dakatar da yaƙi. Sun dogara ne kan tunanin cewa bayanan sirrinmu ba za su kai nasu ba. Mun kai matakin cikakkiyar fahimtar waɗannan dabarun na Amurka kuma mun shirya yadda ya kamata.”

    Kalaman Mista Qalibaf sun zo ne bayan wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito cewa Amurka na aika ƙarin jiragen yaƙi zuwa yankin domin shirin wani “cikakken yaƙi” da Iran.

  7. Iran ta ce ta kai hari kan Sojojin Amurka a Kuwait da Bahrain

    Dakarun juyin juya halin Iran (IRGC) sun sanar da cewa sun kai hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka da ke Bahrain da Kuwait da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa.

    A wata sanarwa da dakarun suka fitar, sun ce rundunar ruwan IRGC ne ta yi wa sojojin Amurka "mummunan rauni" a harin da ta kai a mataki guda uku..

    Sanarwar ta ce a mataki na farko da na biyu dakarun sun kai hari ne kan cibiyoyin gyarawa da kula da jirage marasa matuƙa na Amurka da ke filin jirgin sama na Al Sakhir da kuma tashoshin shirya jiragen ruwa na TF59 a tashar Salman da ke Bahrain.

    A mataki na uku kuwa, sun kai hari kan cibiyoyin da ake horaswa da tallafa wa rundunar ruwan Amurka ta musamman a sansanin Arifjan da ke Kuwait.

    IRGC ta kuma jaddada cewa hare-haren kan sojojin Amurka a yankin za su ci gaba.

  8. Hamas ta zaɓi sabon shugaba

    Ƙungiyar Hamas ta sanar da zaɓen Khalil al-Hayyah a matsayin shugaban ofishinta na siyasa, inda ya maye gurbin Yahya Sinwar, wanda aka kashe a wani hari da sojojin Isra’ila suka kai a Zirin Gaza a watan Oktoban 2024.

    Matsayin Al-Hayyah ya ƙara karfi a cikin ƙungiyar bayan kashe wasu manyan shugabannin Hamas, ciki har da Ismail Haniyeh a Tehran, Yahya Sinwar a Gaza, da kuma kwamandan rundunar sojin kungiyar Muhammad Deif, duk a cikin shekarar da ta gabata.

    An haifi Khalil al-Hayyah a shekarar 1960 a Zirin Gaza, kuma yana cikin mambobin da suka kafa Hamas tun daga kafuwarta a shekarar 1987.

    Zaɓen nasa na zuwa ne a wani lokaci da ƙungiyar Hamas ke fuskantar manyan ƙalubale sakamakon yaƙin da ake ci gaba da yi a Gaza da kuma asarar wasu daga cikin fitattun shugabanninta.

  9. Houthi ta Yemen ta ƙaƙaba wa Saudiyya takunkumin zirga-zirgar jiragen ruwa

    Ƙungiyar Houthi ta Yemen ta sanar da ƙaƙaba takunkumin zirga-zirgar jiragen ruwa kan Saudiyya kuma zai fara aiki nan take.

    Houthi sun ce rikicin ya ƙara tsananta ne bayan da Saudiyya ta yi yunƙurin hana wani jirgin saman Iran sauka a filin jirgin saman kasa da kasa na Sanaa.

    A gefe guda kuma, Iran da Amurka sun nuna alamun aniyar komawa kan teburin tattaunawa duk da ci gaba da musayar hare-hare a tsakaninsu.

    Iran ta ce ta samu shawarwari daga masu shiga tsakani domin rage tashin hankali, yayin da ministan harkokin cikin gidan ƙasar ke shirin kai ziyara Pakistan a yau.

  10. An miƙa wa Iran tayin tsagaita wuta na kwana 10 - Baghaei

    Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya tabbatar da cewa Iran ta karɓi tayin tsagaita wuta na kwana 10 da wasu masu shiga tsakani suka miƙa mata, amma ya ce ba zai bayyana cikakkun bayanan tayin a wannan lokaci ba.

    Da yake magana a wani taron manema labarai, Baghaei ya ce an miƙa wa Iran tayin ne yayin da harkokin diflomasiyyar ƙasar na ci gaba da gudana a kwanakin nan.

    Game da yiwuwar sake komawa tattaunawa idan shugaban Amurka Donald Trump ya nemi hakan nan gaba, Baghaei ya ce bai dace a ɗora batun a matsayin zaɓi tsakanin tattaunawa ko yaƙi ba.

    Ya ƙara da cewa diflomasiyya da kare ƙasa ba sa cin karo da juna, domin dukkansu suna da manufar kare muradun ƙasar Iran.

  11. Mun kama mayaƙin ƙasar waje a Borno - Sojojin Najeriya

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation HADIN KAI sun kama wani mutum ɗan ƙasar Sudan da ake zargi da kasancewa "mayaƙin ta'addanci " na ƙasashen waje.

    A cikin wata sanar da rundunar ta fitar, ta ce an kama mayaƙin ƙasar wajen ne a wani samame da dakarun suka kai a yankin Lassa da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba a jihar Borno ranar 19 ga Yulin 2026.

    "An kama Musa Fashir mai shekaru 32 da misalin ƙarfe 11:48 na safe bayan bayanan sirrin da muka samu wanda hakan ya sa muka kai samame." in ji rundunar.

    Sanarwar ta ce wanda ake zargin yana da alaƙa da wasu ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya, lamarin da ke nuna yiwuwar samun goyon baya daga wasu ‘yan ƙasashen waje ga ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

    Haka kuma rundunar ta ce sojojinta sun kama wata Mary Florence mai shekaru 36, wadda ta ce ‘yar ƙasar Ghana ce kuma ta shiga Najeriya ba bisa ƙa’ida ba.

    Rundunar ta ce tana binciken yadda ta isa yankin da kuma sahihancin bayanan da ta bayar game da asalinta da ayyukanta.

    Rundunar ta bayyana cewa mutanen biyu suna tsare a hannun sojoji domin ci gaba da tantance su da gudanar da bincike kan yiwuwar alaƙarsu da ƙungiyoyin ta’addanci ko wasu hanyoyin aikata laifukan ƙetare.

  12. Iran ta ce mutum ɗaya ya mutu a harin Amurka kan wani sansanin soji a Tabriz

    Hukumar kula da agajin gaggawa ta lardin Gabashin Azerbaijan a Iran ta sanar da cewa mutum ɗaya ya mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani hari da Amurka ta kai a arewa maso yammacin ƙasar.

    A cewar hukumar, harin ya faru da misalin ƙarfe 2:35 na safiyar Litinin a wani wurin soji da ke kudu maso yammacin birnin Tabriz.

    Sanarwar ta ce mutum ɗaya ya rasa ransa, yayin da wasu da dama suka samu raunuka sakamakon harin.

    Tun da farko, shugaban Amurka Donald Trump ya ce wannan shi ne hari na tara da Amurka ta kai kan Iran, yana mai cewa an kai hare-haren ne a matsayin ramuwar gayya kan kisan sojojin Amurka da aka yi a Jordan.

  13. Andy Burnham ya zama sabon firamintsan Birtaniya

    Andy Burnham ya zama sabon Firaministan Birtaniya bayan ganawa da Sarki Charles na Uku a Fadar Buckingham, inda sarkin ya ba shi umarnin kafa sabuwar gwamnati.

    Nadin nasa ya zo ne jim kaɗan bayan Keir Starmer ya gana da Sarkin tare da miƙa takardar murabus ɗinsa daga muƙamin Firaminista.

    Bayan karɓar umarnin kafa gwamnati, Burnham zai koma ofishin Firaminista da ke Downing Street, inda zai fara zaɓen ministocinsa da kuma tsara sabuwar gwamnatin da za ta jagoranci ƙasar.

  14. Kalli yadda magoya bayan Spain suka yi murnar lashe kofin duniya

  15. Kier starmer ya miƙa takardar murabus daga firaminista ga Sarki Charles

    Firaministan Birtaniya mai barin gado, Keir Starmer, ya miƙa takardar murabus ɗinsa ga Sarki Charles na Uku a wata ganawa da suka yi a Fadar Buckingham a safiyar yau.

    A wata sanarwa da fadar ta fitar, ta ce Sarki Charles ya karɓi murabus ɗin Starmer a matsayinsa na Firaminista da kuma Babban Jami’in Baitulmali na Farko.

    Fadar Buckingham ta bayyana cewa Starmer ya gana da Sarkin ne a yau inda ya mika murabus ɗinsa, wanda Mai Martaba Sarkin ya amince da shi.

    Sanarwar ta kuma ce matar Starmer ta halarci ganawar tare da shi kuma ita ma ta samu ganawa da Sarkin.

    Hotunan da aka fitar daga fadar sun nuna Keir Starmer da Sarki Charles suna musabaha.

    Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da Starmer ya ajiye muƙaminsa na Firaministan Birtaniya, lamarin da ke kawo ƙarshen wa’adinsa a jagorancin gwamnati.

  16. An kashe limamin Juma’a na Sunni a Mirjaveh na Iran

    'Yan sandan lardin Sistan da Baluchistan na Iran sun sanar da cewa wasu 'yanbindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe Malam Maulvi Mohammad Anwar Rigi, limamin Juma'a na Sunni a garin Mirjaveh.

    A wata sanarwa da rundunar 'yansandan ta fitar, ta ce maharan sun harbe malamin ne da safiyar Litinin sannan suka tsere daga wurin da makamansu.

    Sanarwar ta ce cibiyar bayar da agajin gaggawa ta 'yan sanda ta yi gaggawar isa wurin da harin ya faru, kusa da Babban Masallacin Mirjaveh.

    Sai dai duk da ƙoƙarin ceton rayuwarsa, Maulvi Mohammad Anwar Rigi ya rasu sakamakon munanan raunukan da ya samu daga harbin.

  17. Na kammala aikina - Keir Starmer

    Firaministan Birtaniya mai barin gado, Keir Starmer, ya ce ya kammala aikinsa yayin da yake gabatar da jawabinsa na ƙarshe a gaban ofishin firaminista da ke Downing Street kafin ya nufi Fadar Buckingham domin miƙa murabus ɗinsa ga Sarki Charles na Uku.

    Ya ce ya bar ƙasar cikin yanayi mafi ƙarfi da adalci fiye da lokacin da ya karɓi mulki shekaru biyu da suka gabata.

    Starmer ya ce jagorancin Birtaniya ya kasance babban abin alfahari a rayuwarsa.

    Ya tuna yadda ya jagoranci jam'iyyar Labour daga mummunar shan kaye da ta yi a zaɓen 2019 zuwa samun gagarumar nasara a babban zaɓen 2024, wanda ya kai shi ga zama Firaminista.

    Bayan miƙa murabus ɗinsa, sabon shugaban Jam’iyyar Labour, Andy Burnham, zai gana da Sarki Charles kafin a naɗa shi sabon Firaministan Birtaniya a hukumance.

    A jawabin nasa na ƙarshe, Starmer ya yi wa Burnham fatan alheri, yana mai cewa yana da cikakken yaƙinin cewa sabon shugaban zai ci gaba da gina kan nasarorin da gwamnatin Labour ta samu.

  18. Jirgin ruwa ya kama da wuta bayan hari a mashigar Hormuz

    Wata cibiyar sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa ta Birtaniya, UK Maritime Trade Operations (UKMTO), ta ce wani jirgin ruwa ya kama da wuta a mashigin Hormuz bayan wani makami mai linzami ya auka masa

    An kai harin ne kimanin kilomita 15 arewa maso yammacin garin Kumzar da ke ƙasar Oman.

    A cewar cibiyar, ma’aikatan jirgin sun yi nasarar barin jirgin cikin aminci, inda aka yi amfani da wani ƙaramin wajen kuɓutar da su.

    Sai dai har yanzu ba a samu damar kashe wutar gaba ɗaya ba, kuma jirgin na ci gaba da shawagi a ruwa ba tare da wani iko da ke sarrafa shi ba.

    Cibiyar ta kuma gargaɗi sauran jiragen ruwa da ke wucewa ta yankin da su kasance cikin shiri tare da kai rahoton duk wani abin da ya bayyana a matsayin mai tayar da hankali ko abin zargi.

  19. Ɗalibai uku ne suka mutu yayin musayar wuta tsakanin sojojin da mayaƙan Iswap a Borno

    Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Borno, Usman Tar, ya ce ɗalibai uku ne suka mutu a musayar wutar da aka yi jiya Lahadi tsakanin sojin Najeriya da mayaƙan ISWAP bayan harin da suka kai a Monguno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

    A tattaunawarsa da BBC, kwamishinan ya ce mayaƙan sun kai hari ne da nufin yin garkuwa da ɗaliban da ke zaune a makarantar sakandaren ƴan mata ta FGGC da ke Monguno.

    Ya ce yayin da sojoji ke musayar wuta da maharan domin dakile harin, harsasai sun samu wasu ɗalibai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar uku daga cikinsu, yayin da wasu kuma suka jikkata.

    Tun da farko, Rundunar Operation HADIN KAI ta ce maharan sun kai farmaki makarantar da misalin ƙarfe 1:30 na safiyar ranar 19 ga Yuli, amma jami'an tsaro da ke wurin tare da goyon bayan rundunar MOPOL da dakarun gaggawa sun yi nasarar hana su cimma burinsu.

    Rundunar ta ce an ceto ɗalibai 46 baki ɗaya tare da kwashe su zuwa Barikin Kinnasara da ke Monguno domin duba lafiyarsu, kuma babu wani ɗalibi da aka yi garkuwa da shi.

    Ta kuma ce tana ci gaba da farautar maharan tare da binciken mutanen da ake zargin sun taimaka musu wajen kai harin, yayin da ta jajanta wa iyalan ɗaliban da suka rasu.

  20. Bahrain ta buƙaci mazauna su koma wurare masu tsaro saboda hare-haren Iran

    Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Bahrain ta buƙaci al’ummar ƙasar su gaggauta komawa wurare masu tsaro tare da kwantar da hankalinsu bayan da aka kunna ƙararrawar gaggawa a sassa daban-daban na ƙasar, a daidai lokacin da ake fargabar hare-haren da Iran ke kai wa wuraren da ke da alaƙa da Amurka a yankin Gulf.

    Kafofin yaɗa labaran cikin gida a Iran sun ruwaito cewa an ji wasu fashe-fashe a Bahrain.

    Lamarin na zuwa ne yayin da rikici tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da ƙamari, inda Iran ta sha bayyana cewa tana kai hare-hare kan wuraren da sojojin Amurka ke amfani da su a ƙasashen yankin, ciki har da Kuwait da Bahrain.

    Tun da farko, Rundunar Juyin Juya halin Iran (IRGC) ta ce ta kai hari kan wasu wuraren sojin Amurka a Kuwait.

    A gefe guda kuma, rundunar sojojin Amurka (CENTCOM) ta sanar da kammala zagaye na tara na hare-haren da take kai wa wasu wurare a Iran a jere, yayin da kafar yaɗa labaran gwamnatin Iran ta ce hare-haren sun shafi yankuna da dama da suka haɗa da Bandar Imam Khomeini, Mahshahr, Sirik, Jask, Chabahar, Konarak da wasu sassan lardunan Bushehr da Hormozgan..