Chadi ta kori ƴan gudun hijirar Najeriya - AFP

Asalin hoton, Getty Images
An kori ɗaruruwan ƴan Najeriya da ke zama a Chadi domin neman mafaka daga hare haren masu iƙirarin jihadi zuwa Najeriya a makon da ya gabata, kamar yadda wasu daga cikinsu suka shaida wa kamfanin dillanci labarai na AFP.
Hakan na zuwa ne a yayin da masu sharhi ke gargaɗin cewa an samu ƙaruwar hare hare a arewa maso gabashin Najeriya a shekarar da ta gabata.
Wasu ƴan Najeriya biyu da aka kama a Chadin sun shaidawa AFP cewa ƴan ƙasarsu ɗari shida aka tsare bayan an kama su, kuma aka yi watsi da su a birnin Kousseri, wanda ke kusa da iyakar babban birnin ƙasar N'Djamena.
Ƴan sandan Chadi sun tabbatar cewa an kori mutanen, amma basu bayar da adadi ba.
Sun ce sun ƙaddamar da wani shiri da suka saba yi kan ƴan gudun hijira da suka shigo ta ɓarauniyar hanya, ba tare da la'akari da ƙasar su ba.
'' A ranar Juma'a jami'an tsaro suka dira a gidanjenmu, suka ce duk ƴan gudun hijira daga Najeriya ƴan Boko Haram ne, kuma su fice daga ƙasar su. Kuma suka ɗauki bayanan hannunmu'' kamar yadda Kyari Musa ya shaidawa AFP.
A cewar sa sun kuma yi gargaɗin cewa duk wada ya dawo kuma aka kama shi zai je gidan yari na shekara 20.
Ƴan Najeriyan sun kuma ce a ranar Asabar ne jami'an Kwastam na Chadi suka kai su garin Gamboru da ke kan iyakar ƙasar da Najeriya.
Najeriya dai ta shafe kusan shekara 17 tana fama da mayaƙa masu iƙirarin jihadi, waɗanda suka yi ta bazuwa zuwa ƙasashen Nijar da Kamaru da Chadi.







