Mutum 5,000 sun tsere daga gidanjensu a Philippines bayan aman wuta da wani dutse ya yi

Asalin hoton, Marco Restivo / Barcroft Media
Dubban mutane a Philippines sun tsere daga gidajensu sakamakon aman wuta da wani dutse ya yi a kasar.
Dutsen Mayon da ke yankin Bicol ya yi aman ne ranar Asabar din da ta gabata, inda ya fitar da toka da ta turnuƙe sararin samaniya.
Sama da mutane dubu biyar da ke zaune a kasan dutsen yanzu haka suna matsugunan gaggawa na wucin gadi, yayin da hukumomi ke kokarin bude hanyoyin da toka ta mamaye.
Kasar Philippines na daya daga cikin kasashen da suka fi fuskantar bala'i a duniya, inda ake yawan samun duwatsu masu aman wuta da girgizar kasa da ambaliya da kuma zabtarewar kasa.





