An zaɓi sabon shugaban ƙasa a Lebanon

Asalin hoton, Reuters
'Yan Majalisar dokokin Lebanon sun zaɓi hafsan hafsoshin sojin kasar, Joseph A,oun a matsayin sabon shugaban kasa, wanda ya cike gibin muƙamin da aka shafe shekara biyu ba a sami wanda zai jagoranci ƙasar ba .
A kalamansa na farko zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya yi alƙawarin sake gina birnin Beirut da kudancin Lebanon bayan yaƙin da Hezbullaah ke yi da Israila .
Janarar Ao-un ya kuma ce zai maida hankali wajan tabatar da cewa gwamnatin ta ɗauki mataki kan waɗanda suka mallaki makamai.
Sai dai sabon shugabna ƙasar zai fuskanci ƙalubale waɗanda suka haɗa da yajejeniyar tsagaita buɗe wuta da ke tangal- tangal da kafa gwamnati da za ta iya aiwatar da sauye sauyen tattalin arziki.





















