Yadda aka yi wa manoma sama da 20 kisan gilla a Zamfara - Amnesty

Asalin hoton, FB/Dauda Lawal
Sama da mutum 20 ne mahara suka kashe a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, yankin da ya daɗe yana fama da matsalar ƴan bindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa.
Lamarin wanda ya faru a ranar Laraba ya rutsa da manoma waɗanda suka raja'a wajen aikin gona.
Wani wanda ya ga abin da ya faru ya shaida wa BBC cewa: "Muna gona muna aiki aka ce ga su nan sun taho, kafin mu ankara sun riga sun rufe mu, sun rufe ko ina, idan ka gudu sai su buge ka da mashin su harbe ka sannan su take ka.
"Sun zo ne a babura sun kai 100, suka riƙa bin mutane suna kashewa, sannan suka tattara dabbobi suka tafi da su," in ji mazaunin ɗaya daga cikin ƙauyukan.
Ya ƙara da cewa maharan sun fito ne daga "wajen Jangebe", wani yanki na jihar ta Zamfara da ya yi ƙaurin suna kan matsalar tsaro.
"A halin yanzu muna cikin jeji ne, da idona na ga gawarwaki sun kai 20".
Ya ce ƴan bindigar sun kai harin ne a ƙauyuka Sauna, Tudun Namale, Tsangaya, Mashekari da kuma Unguwar Shanu.
A wani bayani da ta wallafa shafinta na facebook, ƙungiyar Amnesty International ta ce lamarin ya yi sanadin rayuka 24, yayin da mutane da dama suka tsira da munanan raunuka.
"Wannan na nuni da cewa dabarar da ake amfani da ita wajen yaƙi da matsalar tsaro a jihar Zamfara ba ta aiki", in ji Amnesty.
Ƙungiyar ta ce ƴan bindiga na kai hare-hare a ƙauyukan Zamfara a duk lokacin da suka ga dama, inda suke sanar da mazauna ƙauyuka a lokacin da za su kawo hari, sannan kuma sukan buƙaci a biya su maƙudan kuɗaɗe.
Zamfara ta shafe sama da shekara 10 tana fama da matsalar ƴan fashin daji masu kai hare-hare suna kashe mutane da kuma garkuwa da wasu domin neman kudin fansa.
Matsalar ta kuma shafi sauran jihohin yankin, kamar Katsina, Sokoto, Kebbi Kaduna da kuma Neja a arewa ta tsakiyar ƙasar.
An yi amannar cewa akwai ƙungiyoyin yan bindiga da dama da suke cin karensu babu babbaka a dazukan da suka haɗa jihohin yankin har zuwa kudu maso yammacin ƙasar.
A baya-bayan nan an samu lokutan da irin waɗannan mayaƙa ke kai hari a ƙauyuka suna kashe mutane tare da ƙona gidaje da kadarori.
Hukumomi a ƙasar sun sha nanata cewa suna daukar matakai kan lamarin, amma har yanzu abin ya ci tura.


